Part 2 page 2

267 14 1
                                    



DAMA TA BIYU
(The Second chance)

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:Northern_life_stories.

RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....

Littattafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu

*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis CTRIJF LOML* 😢😭



Part two
Page Two....
          Ta miqa masa wayar tana dariya tace da qarfi yanda Immileeyn zata ji "Duk saurin ki dai mun samu wasu kuma zamu sake daukan wasu."

Kunnen ta Mooha yaja ta fasa qara tana riqe hannunsa yace "Wai bana gaya miki cewar yayar ki bace yanzu ba qawar ki ba?"

Da sauri tace "Don Allah kayi haquri bazan sake ba."

Sakin mata kunnen yayi yana cewa "Idan kika sake zane ki zanyi da kyau kuwa."

Amnah tazo ta zauna a dinning table din tana cewa "Ai gara ka zane tan ta dade bata ga bulala ba tunda Jaan L ya tafi."

Jannah ta harare ta tace "Muguwa ai daman halin magoyin naki kikai."

Amnah ta kama baki tana girgiza kai tace "Jaan din nawa ne mugu?"

Jannah ta miqe don tasan sarai Mooha na iya zaneta da gaske idan tayi wasa tace "Ni bance ba munafuka kawai." Da gudu ta haye sama don Kar Mooha ya samu damar mata magana,tana ji yana qwala mata kira tayi kamar bata ji ba don tasan sauran idan ta koma.

Wanka ta tarar har Immileey ta fito,ta dan duke ta a kafada tana fad'in "Kika sa aka murde min kunne a kanki zan rama."

Dariya tasa manyan dimples dinta suka lotsa tace "maganin mara kunya kenan."

Murguda mata baki tayi tace "Naji nidai ai baki girme niba a shekaru."

Cikin dariya Immileey tace "Amma kinsan dai dole ace da mijin iya baba tunda na ajiye kamar ki yanzu ta isa ku jera zance."

Dariya Jannah tasa tace "A garin ga6a ga6a ba."

Duk suka saka dariya,Immileey tace "A garin masu hankali ma hakanne."

Uniform ta soma cirewa tana wulla su cikin laundry basket tana cewa "Kin dai ajiye Baby Eve ba dai kamata ba."

Daga haka ta shige toilet lokacin da Lami sabuwar er aikin da sukayi ta shigo da waya a hannun ta ta miqa mata tana cewa "Gashi inji Mummy tace a kawo kiki."

Tasan kwanan zancen don haka da murna ta karba ta kuma yi dialing number din Innar ta da itace a farko wajen kiran.

"Assalamu'alaykum." Kamilalliyar muryar Goggo Lari ta yi sallama.

Cikin murna tace "Innata."

Murmushi tayi kafin tace "Baki amsa sallama ne ke?"

Tana dariya tace "Waalaykisalam Innahta,ina wuni."

"Lafiya lau,ya gida ya makaranta."

"Duka lafiya Inna,ya kowa da kowa?"

"Lafiya lau."

"Innah Ma'u  fa na manta in tambaye ta lokacin bikin nata,kuma kinga muna makaranta bamu jima da komawa ba bana son nayi missing komai ko kinji lokacin bikin?"

DAMA TA BIYUWhere stories live. Discover now