🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
*And*
*Written*
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}
*WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg
*FREE PAGE*
*Page: 7*
*Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*
....Tunda suka ɗau hanya mai motar ke sharara gudu dan so yake so isa NIGAR kafun asuba daga nan ne SHAHEED zaiyi canjin mota, lokacin ticket ɗinsu na shiga ƙasar zai fara aiki, tunda suka ɗauki hanya NABIL da ILHAM bacci suke haka UMMA yau jikin nata da sauƙi tunda har ta samu sauƙi saɓanin saura rana ku da duk dare zata dinga suma, wasu lokutan ma har takanyi aman jini, SHAHEED ne kaɗai idanunsa biyu, wadda fargaba da tsoro suka taru suka masa yawa acikin zuciya, koya motar tayi slow sai ƴan cikinsa sun amsa, da ace wani zai samu nasara kallonsa koda sau ɗayane zaiga zunzurutun damur dake shimfiɗe a fuskarsa, ahaka har suka iso jibiya suka cigaba da ratsawa cikin garin, jejin driver motar ya yanka suka cigaba da tafiya suna wuce ƙauyin kan NIGER ga wani irin gudu da driver ke tsulawa kamar ba babba mota yake ja ba.
*NIGER*
Misalin ƙarfe 4:00am na asuba suka iso cikin ƘASAR NIGER, tsaida mota driver yayi SHAHEED dake zaune duk a firgice yake ƙirjinsa na mugun duka fat-fat, buɗe motar da driver yayi har sai daya haifawa SHAHEED zabura yana wurwurga idanu saboda tsanin tsoro ganin driver mota ne yasanya SHAHEED sauke nanauyiyar ajiyar zuciya driver motar ya ce, "mun iso inda za'ayi canjin mota" hamdallah SHAHEED yayi tare da sauke ajiyar zuciya ganin cewa ya bar NIGERIA bari na har abada kamar yarda yake tunani a yanzu, wata motace ta faka gaban tasu mai ɗan kyau wadda ke ɗauke da number NIGER, UMMA SHAHEED ya fara ɗaukowa aka sanyata cikin motar sannan ya tashi NABIL ya ɗauki ILHAM tare da sauran jakunkunasa dama ya biya motar da suka taho tare, ɗaga masa hannu mai motar yayi cike da tsantsar farin ciki SHAHEED ya ɗaga masa hannu, sannan motar su ta tashi ta lula cikin sahara nan ma motar gudu kawai take, yayinda ILHAM na saman jikinsa ya rufeta da maluluɓi sai da sukayi tafiya mai nisan gaske sannan suka ɓulo titi lokacin rana ta fito tarwai abunka da ƙasa mai sahara, motocin dake kan titin ne suka fara slow, sojojin NIGER ne suka fara tsaida motocin dake wurwucewa dayake driver ban su yasan kan komai, kuma dama anyi SHAHEED bayanin yarda komai yake yana zuwa kansu SHAHEED ya bada ticket ɗinsu su uku babu na ILHAM cikin hausar su da bata fita sojan yayi ya ce, "na wannan fa.? ya nuna ILHAM dake jikin SHAHEED kuɗi SHAHEED ya irgo masu kauri na NIGER mil 30 ya miƙawa sojan hannun suka gaisa yasaka masa kuɗin cikin hannunsa yana murmushi washe baki sojan yayi ya ce, "ku wuce.! ajiyar zuciya SHAHEED ya sauke yana leƙa fuskar ILHAM dake bacci jikinsa hankali kwance NABIL ne ya fara tashi daga bacci ya ce, "hamma zanyi fitsari.! mai mota ne yatsaida mota NABIL yayi fitsari sannan suka cigaba da tafiya.
Guzirin da SHAHEED ya musu ya buɗe jaka ya ɗauko drink da cake ya miƙawa NABIL, sannan ya leƙa fuskar UMMA da itama bacci take goshinta ya taɓa ya ji da zafi rau furzar da iskar bakinsa yayi, mai zafi yana fatan su isa cikin birnin niger da wuri, fatansa shine suna isa cikin gari direct asibiti yake son wucewa da UMMA buɗe idanunta UMMA tayi ta zuba su kan SHAHEED dake kallonta ahankali ya furta, "ina kwana.! jinjina kai tayi gami da kallon ILHAM dake jikinsa kwance shima ɗin kansa ya maida kan ILHAM idanunta buɗe ya gani tana kallon UMMA, murmushi ta sakarwa UMMA ta ɗaga mata hannu alamar bye-bye lumshe idanu UMMA tayi fuskarta sake da annuri cikin tsamun murya ta ce, "SHEED yunwa" ta faɗa tana kallon NABIL dake aika cake da drink, cake ɗin ya miƙa mata ta amsa tana ci tana ba SHAHEED yana amsa.
*NIGER NIAMEY*
YOU ARE READING
WATA ƘADDARA
ActionKo wani bawa nada tasa zanan ƘADDARA sai dai shi tashi tasha banban data saura, komai ya farune daga ranar da mahaifiyarsa ta kwanta ciwo, ya buga ya nema domin sama mata kuɗin magani dana asibiti duk da yana matashin saurayi mai ƙarancin shekaru ɗa...