🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
*And*
*Written*
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}
*WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg
*FREE PAGE*
*Page: 8*
*Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*
........Kamar yarda SHAHEED yayi tunani ba haka bane suna doso inda ya bada ajiyar ILHAM ya fara jiyo muryarta harta dashe saboda tsabar kuka tun ƙarfita take kukan, ƙarasowa wajen SHAHEED yayi abunka da fara fata fuskarta har tayi ja dan kuka ɓata fuska SHAHEED yayi cikin jan fasali ya ce, "BABY.! jajayen idanunta ta ɗago tare da fashewa da sabon kuka ta kawar da kanta ɗan murmushi nurse ɗin tayi ta ce, "wallahi tunda kuka tafi take kuka tana cewa Mama SHEED.! tausayinta ne ya dirawa SHAHEED hannu ya miƙa mata ya ce, "zo nan" maƙe ƙaffaɗa tayi tare da ƙara rushewa da kuka harda majina sosai abun yaba ma nurse ɗin dariya ta ce, "amma dai wannan ita ce ƴar autar ku.? da girmanta da komai take wannan fitina zatayi 3years fa" SHAHEED dake tsaye ya ce, "haka takeyi da girmanta da komai kamar ƴar yaye" SHAHEED ya faɗa yana doka mata harara itama ɗin manyan idanunta ta watsa masa tana jan majina hancinta, hannun SHAHEED ya kai zai ɗauketa, botsarewa tayi tare da sakin kuka da alama tayi fushi da SHAHEED ɗin bana wasa ba, tana tuture hannunsa tana cewa, "Mama SHEED ne" ta faɗa cikin fashewa da kuka mai ƙarfin gaske, kwantar da ita SHAHEED yayi saman kaffaɗarsa ya ce, "shhh is okay BABY am here am really sorry" ya faɗa yana dukan bayanta ahankali ajiyar zuciya ta shiga saukewa ta ƙanƙame rigar SHAHEED tana cigaba da sauke ajiyar zuciya da jan majina idanunta kuwa sunyi jawur saboda kuka NABIL ya ce, "sorry BABY" harara ta dalla masa shima ta kawar da kanta gefe shima ɗin harara ya doka mata ya ce, "ke kika sani" kallon da SHAHEED ya jefa masa yasaka sa cewa, "baran ƙara ba"
"good for you.! suna zaune nan aka fito da UMMA Alhamdulillah anyi aikin cikin sa'a, tana kwance flat saman gado da oxygen saman hancinta sai ƙarin jini da ake mata.
Ɗaki aka bata sannan suka shiga ɗakin suma ƙarasawa bakin gadon SHAHEED yayi yana kallon UMMA wadda fuskarta tayi fayau da ita alamar ciwo ya ci mutum sosai, kamarsa da UMMA kuwa kamar an tsaga kara dan dai ita fara ce sosai shi kuma SHAHEED chocolete colour ne shafa kan Umma yayi ya furta, "Alhamdulillah.! idanunsa cike da ruwan hawaye ko ba komai likitoci sun samu nasara ceto rayuwar Ummansa, shigowar nurse ne yasanya ɗago idanunsa nurse ta ce, "mara lafiyar ku bata buƙatar hayaniya, kuna iya bata waje ko da gobe da safe ne sai ku dawo dan nan bamu bari kwana da mara lafiya" jinjina kai SHAHEED yayi ya ce, "NABIL mu tafi gida ko" ya faɗa yana kama hannun BABY suka fice yana kallon Umma.Taxi ya tara masu suka shiga saida suka fara tsayawa ahanya wajen wani mai shayi, SHAHEED ya siya masu abinda zasu ci adaren dan raban su da wani abinci tun cake ɗin da suka ci a mota, yaga ƙoƙarin BABY sosai yarda ko sau ɗaya batayi ƙorafin yunwa ba, yarda ya lura da yarinyar bata da son abincin sosai sai dai tsabagyen fitina ta iya da kuka su kaɗai tafi ƙwarewa akai, mota ya dawo suka ɗauki hanyar gida unguwar tarwai take da wutar nepa titi unguwar yayi shuru taxi driver na parking su SHAHEED suka sauko tare da basa kuɗinsa.
Key SHAHEED ya murza ƙofar gidan ta buɗe suka shige ciki ya buɗe ƙofar parlour tare da kunna hasken parlour ya gauraye da haske ya kunna fanka, saboda zafin da yake ji, saman kujera ya faɗa tare da furta, "washh.! saman jikinsa ILHAM ta haye NABIL na gefensa kallon ledar da ya aje yayi ya ce, "NABIL sako ku ci abinci kai da BABY" sakowa yayi kamar yarda SHAHEED ya umarce sa ya buɗe ledar indomie ce dafafiya har da sosayan kwai ya ce, "BABY sako mu ci abinci" zamowa tayi daga jikin SHAHEED ta sauko ƙasa ta zauna tasanya hannunta suka fara cin indomie, SHAHEED da idanunsa ke lumshe yana kallonsu ta ƙasan idanu yarda suke cin abincin hannu baka hannun ƙwarya hannun ILHAM tasa ta ɗeɓo abincin gabanta ta ce, "SHEED abinci.? ta faɗa tana ɗebo indomie, ƙasa shima ya sauko ya jawo wata ledar ya buɗe, indomie ne ciki ya ƙara masu akan wadda suke ci yasanya hannu suna ci su ukun, sai da suka ƙoshi sannan SHAHEED ya tattare ledojin ya kai bola ya dawo ya miƙa masu drinks masu sanyi suka sha.
Bedroom ya shiga ya kwashe duka mayafan dake saman gadon, ya kakaɓe gadon da wata ƴar rigarsa kafin gobe su share gidan bathroom ya shiga shima duk yayi ƙura, famfo ya buɗe sai ga ruwa sosai ya ji daɗin ganin gidan akwai ruwa alwala ya ɗauro ya fito daduma ya shimfiɗa wadda ya zo da ita ya kalli NABIL ya ce, "shiga bathroom ka ɗauro alwala ka zo muyi sallah"
"toh.! ya ce gami da shigewa toilet jim sai gashi ya fito da alwala magrib da isha'i sukayi BABY na zaune gefensu tana wasa da ƙura dake ƙasa, suna idar da sallah SHAHEED ya koma toilet ɗin ganin harda hita cikin toilet ɗin ya kuna duk da baya gane french, amma wasu words ɗin suna shige da turanci ɗan lauyasu akayi, sai da hitar tayi zafi ya kuna shower ya ji ruwan da gumi babu zafi sosai babu sanyi, ɗaki ya dawo ya ɗauki BABY ya cire mata kayanta duka ya ja hannunta suka shiga toilet, kanta yasakawa leda dan baya son jiƙa mata gashi cikin dare kar mura ta kamata, ya sakar mata shower ƙwaɓe fuska tayi dan taƙi jini wanka ko a gida sai anyi yaƙi da ita take wanka, gashi kuma SHAHEED sarkin son tsaf baya son dati tana turo baki da matse ƴan hawaye ya ɗauraye ta tas da ruwa ya ɗauketa suka fito yana cewa, "ƙazama duk mara son wanka ƙazamine kamar BABY da bata son wanka" saman gado ya dire ta ya naɗeta da zani ya ce, "oya NABIL shiga kayi kai ma" sumu-sumu ya miƙe shima dan kamar ƴar uwarsa BABY yake kan wanka kallonsa SHAHEED yayi ya ce, "ƙazami mara son wanka ɗan uwan BABY" dariya BABY ta saki ta ce, "amami" harara ya doka mata ya ce, "sai na fasa maki baki ni sa'anki ne.? juyowa SHAHEED yayi yana kallonsa, da sauri ya shige toilet yana tura baki gaba da shigarsa bada jimawa ba shima ya fito, shima yana tuturo baki ko kallonsa SHAHEED bai ba ya cila masa wasu kaya wando da riga na bacci, itama BABY ya shiryata cikin pink kayan bacci tana kwance tana wasanita kamar da rana sai da NABIL ya shirya ya hayo gadon, sannan SHAHEED ya ɗauki wasu kaya yayi hanyar toilet miƙewa BABY tayi zumbur zata bisa ya ce, "toilet zai shiga BABY ki zauna da Hamma NABIL kafin na fito" ba musu ta koma saman gadon ta zauna SHAHEED ya ce, "good girl.! toilet ya shiga yayi wanka shima duk da jiƙa-jiƙa ne babu sabulu amma yafi babu sun ji daɗin jikinsu.
Cikin navy blue kayan bacci SHAHEED ya fito wando da riga mai dogon hannu, gashin kansa ya ƙara nanaɗewa irin na fulani sosai, sumar duk damshin ruwa hannunsa riƙe da kayansa daya cire ya aje su saman ƴar sofa dake cikin ɗakin ya ɗauki ɗaya daga cikin rigunasa mai taushi yana tsane sumar kansa da shi, BABY na zaune tana binsa da kallo wadda bacci ke ɗawainiya da idanunta amma saboda naci irin na BABY sai ta jira fitowarsa, ɗagowar da zaiyi sukayi ido huɗu tana gyangyaɗi ɗaga mata gira SHAHEED yayi ya ce, "bacci.? ɗaga masa kai tayi tare da sakowa daga gadon ta kama ƙafarsa ya ce, "toh shi bacci nan za'ayisa koma ki kwanta toh" maƙe ƙaffaɗa tayi tana riƙe da ƙafafun SHAHEED ɗaukarta yayi cak, NABIL da tuni bacci yaɗaukesa hannu ɗaya SHAHEED yasanya ya gyara masa kwanciya ya koma gefe sannan ya aje BABY tsakiyar su ya kwanta gefenta, kashe hasken ɗakin yayi yana jijigata alamar tayi bacci, idanunsa lumshe murginawa BABY tayi ta hanye saman ruwan cikinsa ta kwanta luf, shafa bayanta ya shigayi ahankali yana mamakin son jiki irin na BABY da yarda ta maidasa tamkar mahaifiyarta ɗawainiyar da yake mata yanzu baya tunanin ko mahaifiyarta nayi, saukar numfashinta daya fara jine ya tabbatar masa tayi bacci ahaka bacci ya ɗaukesa shima rungume da BABY jikinsa.Baƙaramun bacci suka samu ba mai cike da nutsuwa da sauke gajiya dan haka har missing sallah asuba sunyi, cikin su babu wanda ya motsa har gari yayi haske.
Misalin ƙarfe 9:00am na safe SHAHEED ne ya fara motsa idanunsa waƴanda hasken rana ya haska su, ya mutse fuska yayi gami da kare fuskarsa da tafin hannunsa, damshin daya fara ji jikinsa ne yasakasa yunƙurin miƙewa, BABY dake kwance saman jikinsa ta motsa wadda ta gama jiƙesa sharkaf da fitsarin kwance, cikin jan fasali ya ce, "ya Allah fitsari kika mun BABY..! BABY da tashin SHAHEED ya tasheta amma tayi lakur jikinsa sanin abinda tayi leƙa fuskarta yayi ya ce, "BABY..! cusa fuskarta tayi cikin jikinsa cakulkuli ya shiga yi mata dariya ta saki mai ƙarfi har dimple ɗinta na lomawa ya ce, "amalala mai fitsarin kwance" ɗagata yayi cak daga jikinsa ya direta ƙasa tana turo baki ya ce, "dubi yarda kika ɓata mun jiki BABY sai zarni fitsarin nake uhm" SHAHEED ya faɗa ya toshe hanci ƙwaɓe fuska BABY tayi tana kallon SHAHEED idanunta raurau da hawaye, duƙawa SHAHEED yayi yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi dan SHAHEED ba mutum bane mai yawan ɗaurewa ba, fuskarsa sake take musanman akan BABY yanzu, button ɗin rigarta ya shiga cire mata yana kallon fuskarta har ya kamala cire mata ya ɗauke kayan ya maidasu gefe, sannan ya sanya mata wayanda ya cire mata jiya yana son mata wanka amma babu sabulu kuma baya son mata jiƙa-jiƙa, toilet ya shiga ya rage kayan jikinsa ya maida nasa na jiya shima sannan ya fito, ɗaukarta yayi suka fice daga gidan.*Follow me on facebook page n group*: *salma mas'ud nadabo*
*Follow me on IG*: *Salmerh 777*
*VOTE*
*COMMENT*
*SHARE*~Taku har kullum salma mas'ud nadabo~
YOU ARE READING
WATA ƘADDARA
ActionKo wani bawa nada tasa zanan ƘADDARA sai dai shi tashi tasha banban data saura, komai ya farune daga ranar da mahaifiyarsa ta kwanta ciwo, ya buga ya nema domin sama mata kuɗin magani dana asibiti duk da yana matashin saurayi mai ƙarancin shekaru ɗa...