🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
*And*
*Written*
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}
*WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg
*FREE PAGE*
*Page: 9*
*Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*
....Tafiya mai ɗan nisa sukayi sannan suka isa wani ƙaton shago dake cikin unguwar sabulen wanka SHAHEED ya siya da duk abubuwan buƙata wanda zasu nema tare da siya ma BABY chocolete, masu yawa sannan suka nufo gida, suna shigowa suka samu NABIL parlour zaune da alama yana tashi yaga basu nan ya dawo parlour da damuwa akan fuskarsa ganin basa gida, shigowarsu yasanyasa washe baki ya ce, "Hamma ina kuka tafi kuka barni a gida.?
"kanti.! SHAHEED ya basa amsa ataƙaice yana shiga bedroom ɗauke da BABY toilet ya shiga har lokacin da nepa dan NIGER suna samun wuta ba kamar NIGERIA ba, hita ya kunna yayi zafi sannan ya dawo ɗaki ya kwashe bedsheet ya wuce da shi toilet inda Allah ya taimakesa katifar nada leda gogewa kawai zaiyi, dire BABY ƙasa yayi tare da ƙwallawa NABIL kira amsawa yayi tare da shigowa bedroom SHAHEED ya ce, "ka ɗauki BABY ku tafi parlour" da "tohm.! NABIL ya amsa tare da kama hannun BABY suka wuce parlour, wanke bedsheet ɗin da BABY ta ɓata da fitsari yayi fes da kayansu baki ɗaya wayanda suka ɓaci, sannan ya fita ta bayan gidan ya shanya, dawowa cikin gida yayi har lokacin suna parlour zaune miƙewa BABY tayi tana bin SHAHEED kamar jela har suka iso bedroom, tsumma da ruwa da omo yasa yana goge ledar katibar data ɓata sai daya tabbatar katifar ta fita fes, ya kunna fanka dan tasha iska da wuri, ya zubar da ruwan datin a bathroom ya dawo bedroom BABY dake tsaye ya nufa ya kamata ya cire mata kaya yayi bathroom da ita, gashin kanta dake kitse sili ɗaya ya warware ya sakar mata shi ya zubo sosai dan BABY akwai gashi sosai har ya so yafi ƙarfinta gata yarinya, shower ya kunna mata ruwan ya fara jiƙata, yamotse fuska BABY tayi tana turo baki shampoo ya zuba ma kanta yana cucuɗasa dan yafita da kyau dan yayi dati, ƴar wahala da suka sha kwana biyu tuni ya fita hayacinsa da dauɗa, saida ya wanke kan tas, ya ƙara kunna shower daya kashe yana mata wanka ya wanketa fes ta fita ya naɗota cikin towel.
Yana direta saman sofa ya shiga bathroom ya rage kayan jikinsa yayi wanka ya jima yana wanka kamar me canza fata, shima ya wanke nanaɗaɗiyar sumarsa fes da shampoo gami da ɗauro alwala ya fito ɗaure da towel a waist ɗinsa ya leƙa parlour ya ce, "NABIL zo kayi wanka.! tashi yayi ya shigo bedroom kaya ya cire ya shiga toilet lokacin SHAHEED na shafe jikin BABY da lotion mai ƙamshi, yana gama shafeta da mai ya shiryata cikin duguwar riga yellow mai hannun vest mai ɗauke da manya Flower mai maɗauri ta baya, ya naɗe mata gashin kanta da towel saboda ya tsane ya daina ɗigar ruwa, sannan ya goge mata gashin sosai yasa comb yana sharce mata shi, yana miƙewa mai ya shafa ma kan ya miƙe sosai dan gashin BABY irin wanda yanayinsa yake kamar anyi famin ne yana da sulɓi bashi da tauri ko ƙaɗan kuma bashi da nanaɗewa, miƙewa yake sosai ribbon SHAHEED yasa ya kama gashin tsaf.
Gaban mirror ya direta yana kallonta ta cikin mirror sosai ta masa kyau yaga ƙoƙarinsa duk da gidan su babu mace, amma yana ganin yarda Ummansa keyi sanda tana da lafiya, shiyasa ya iya, baiyi tunanin zai iya haka da kyauta ba sai da yayi, murmushi BABY ta saki dimple ɗinta na lomawa ɗan yatsansa SHAHEED yasanya cikin dimple ɗin yana murmushi ya ce, "kinyi kyau BABY.! washe baki tayi sosai tana kallon SHAHEED ta mirror waigowa tayi tana ɗaga masa hannun ya ɗauketa, ɗaukarta yayi cikin muryarta mai cike da yarinta ta ce, "SHEED yayi kyau" ta faɗa tana murmushi shima ɗin murmushi yayi tare da direta ƙasa ya ce, "ki tafi parlour zan shirya ban da wasa da ƙura" ɗaga masa kai tayi tafita ba musu, lotion ya shafa ya shirya cikin red t-shirt da jeans sosai yayi kyau, NABIL na fitowa shima shiryawa yayi cikin shirt mai gida-gida da jeans, sannan suka gabatar da sallah suna idarwa SHAHEED ya haɗa masu tea suka zauna nan parlour suka sha.
Bayan sun gama break SHAHEED ya miƙe ya fara gyara gidan kakaɓe komai na gidan sukayi suka share tas, yayi mopping gidan lokaci ɗaya gidan ya fito ƙwal hata ciki kitchen ɗin ba laifi yana kyau kuma yana da ɗan girma har gas akwai aciki, goge komai na kitchen ɗin sukayi suka share fes, sun aikatu sosai shi da NABIL BABY dai na biye da su tana shan chocolete abunta, tasha kyau abunta kamar ƴar larabawa sai da suka kamala komai sukayi azahar a gida sannan suka fito daga gidan taxi SHAHEED ya tara masu zuwa asibiti.Sai da suka tsaya ahanya suka siya ma Umma kayan marmari da take away na abinci, dan sai dare zasu dawo, sannan suka ɗau hanyar asibiti suna isa ward ɗin da aka kwantar da UMMA suka nufa, suna shiga ɗakin suka tada nurse na duduba injina dake aiki kanta gaisawa sukayi da SHAHEED yana tanbayarta, "ya jikin UMMA.?
"Jiki da sauƙi sosai.! ta basa amsa ta cigaba da cewa, "sai dai har yanzu bata farka ba, amma ko wani lokaci tana iya tashi Allah ya bata lafiya" da "amin.! SHAHEED ya amsa nurse ɗinta fita kujera dake kusa da gadon UMMA SHAHEED ya ja tare da aje ledojin hannunsa yana kallon UMMA da oxygen ke manne a hancinta, saman hannunta dake ɗauke da ƙarin jini ya ɗaura hannunsa ahankali ya furta, "Allah ya ƙara maki lafiya Umma na" ya faɗa tare da maida idanunsa kan su NABIL dake zaune saman kujera dake gefen shi da BABY suna wasa, kansa ya ɗaura saman gadon ya lumshe idanunsa kamar me bacci, har aka kira la'asar UMMA bata tashi ba sosai SHAHEED ya damu da rashin tashin nata, har suka tafi masallaci suka dawo BABY na zaune da ita acikin ɗaki sam yau batayi kuka ba, ahankali ta fara sabo da komai saman kujera da SHAHEED ya tashi nan ta zauna ta zabga uban ta gumi tana kallon Umma dake kwance flat har lokacin ba labarin tashinta, ɗagata SHAHEED yayi ya ɗaura saman cinyarsa ya zauna saman kujera BABY ce ta ce, "SHEED wannan bata gajiya da bacci.? ta faɗa tana maida kallonta kan Umma shafa kanta SHAHEED yayi ya ce, "bata da lafiya.!
"me ke damun ta.?
"rashin lafiya" jim BABY tayi ta ce, "ina son ta tashi ta mun magana tun jiya bata magana, da idonta na buɗewa yanzu ya rufe SHEED"
"zai buɗe ne BABY.! SHAHEED ya faɗa yana kallon UMMA NABIL ma na tsaye daga gefen Umman ya ce, "hamma Umma har yanzu bata tashi ba"
"zata tashi NABIL zo ku ci abinci" SHAHEED ya faɗa yana miƙawa NABIL hannu ya kama ya dawo gefensa leda ya nuna masa ya ce ya ɗauko abincin su ci, take away ɗin NABIL ya ɗauko ya ce, "Baby zo mu ci"
"Na ƙoshi" ta faɗa ataƙaice leƙa fuskarta SHAHEED yayi ya ce, "Me kika ci da har zaki ƙoshi da abinci BABY.? ya faɗa yana shafa cikinta wadda ya lafe ya ce, "sauka na baki zaki ci ko.? girgiza kai tayi ta kuma cewa, "na ƙoshi.!
"ban yarda ba since morning ba komai cikin ki sai tea da bread, kina son mu ɓata.? girgiza kai tayi idanunta raurau SHAHEED ya ce, "then zauna ki ci abinci" zamowa tayi daga jikin SHAHEED ta zauna tana tsakura abincin SHAHEED na kallonta ya lura yarinyar sam bata son cin abinci ko dai bata jin daɗi ne ya tanbayi kansa, taɓa goshinta yayi yaji lafiya lau babu fever haka wuyanta, bata wani ci abinci ba ta ce, "SHEED na ƙoshi" ta faɗa kamar zatayi kuka kallonta SHAHEED yayi ya ce, "zo nan.! miƙewa tayi da saurinta tayi jikinsa da sauri ya dakatar da ita karta shafa masa miya, hannunta ya kama yana gogewa da tissue kallonta yayi sosai ya ce, "buɗe bakin ki haa" buɗe bakin tayi sosai ya gani ya ce, "bakin babu daɗi ne BABY.? girgiza masa kai tayi alamar a'a "to me matsala ki na rashin son abinci, ko abinci ne babu daɗi.? nan ma girgiza kai tayi jim SHAHEED yayi yana kallonta ya ce, "idan kina son mu shirya ki dinga cin abinci kin ji BABY." ɗaga masa kai tayi alamar to ya ce, "good girl.! NABIL kuwa share abincinsa yayi yasha ruwa ya tattare take away ɗin ya kai bola ya dawo ɗaki.Har dare yayi Umma bata tashi ba sosai hankalin SHAHEED ya tashi har yayi ma likita complain kan rashin tashin Umma, kwantar masa da hankali doctor yayi da cewa karya damu zata tashi allura da aka mata ne bai saketa ba har yanzu, jin abinda likita ya faɗa yasa hankali SHAHEED kwanciya sannan suka kamo hanyar dawowa gida.
Koda suka dawo gida wanka kawai sukayi suka bi lafiyar gado bayan sunyi wanka, washe gari tun da asuba SHAHEED ya tashi kamar jiya yau ma BABY tayi fitsarin kwance, sai daya fara kimtsata kana ya kimtsa kansa ya tashi NABIL suka gabatar da sallah batare da sun je masallaci ba, bayan sun idar saman sofa NABIL ya koma ya cigaba da baccinsa, SHAHEED kuma ya shiga gyara shimfiɗarsu BABY kuma na biye dashi sam babu bacci idonta, bayan ya kamala kimtsa ɗakin ya fito parlour direct kitchen ya nufa yana tunanin mai zasu dafa dan jiya ya masu siyayar kayan abinci ahanyar su ta dawowa gida, har da sauran kayan kitchen na buƙata dan babu komai kitchen ɗin daga drawers sai gas, dankali ya ɗauko ya fere ya zuba a roba ya ɗauraye ya aje gefe yana tunanin yarda zaiyi da gas ɗin dan bai iya ba, ko aƙauye da murhu suke anfani ko rusho shima ɗin a maƙota yake ganin rushon ɗin masu ɗan hali na ƙauye ke using da shi, jim yayi yana karantar yarda zaiyi*Follow me on facebook page n group*: *salma mas'ud nadabo*
*Follow me on IG*: *Salmerh 777*
*VOTE*
*COMMENT*
*SHARE*~Taku har kullum salma mas'ud nadabo~
YOU ARE READING
WATA ƘADDARA
حركة (أكشن)Ko wani bawa nada tasa zanan ƘADDARA sai dai shi tashi tasha banban data saura, komai ya farune daga ranar da mahaifiyarsa ta kwanta ciwo, ya buga ya nema domin sama mata kuɗin magani dana asibiti duk da yana matashin saurayi mai ƙarancin shekaru ɗa...