🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
*And*
*Written*
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}
*WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg
*FREE PAGE*
*Page: 10*
*Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*
.....Da karan bani SHAHEED ya fara ƙoƙarin kunna gas, sai dai wuta bata kama ba, ganin kamar zaiyi ɓana ya yanke shawara neman NUHU sai dai kuma babu waya hannunsa, amma yana da layinsa a rubuce atakkada kasancewar ya basa layinsa kafun su rabu a asibiti, lokacin da suka kai Umma, kamar yarda ya basa acewarsa idan yana buƙatar wani taimako ya nemesa, fitowa yayi riƙe da hannun BABY, bedroom ya shiga ya ɗakawa NABIL duka dake kwance ya miƙe yana yamutse fuska SHAHEED ya ce, "ka kula da gida zamu fita ni da BABY.! jinjina kai kawai yayi har lokacin da sauran bacci idonsa dan NABIL akwai son bacci ya koma yakwanta, bayan sun fita wajen taxi SHAHEED ya tara masu cikin garin Niamey sukayi ba tare da SHAHEED ya faɗi ina zasu ba sai dai yana bin garin da kallon ko idonsa zai sauka inda ake saida wayoyi driver motar ne ya waigo ya ce, "ranka ya ɗaɗe ina zan aje ka"
"wajen saida waya" SHAHEED ya faɗa ataƙaice gami da sauke ajiyar zuciya jin driver motar ya iya wasa sosai kamar jakin kano, sam baiyi tunanin ƴan NIGER na jin hausa a ƙasar su ba, duk atunaninsa a NIGERIA suke koya ashe akwai hausawan NIGER, wani ƙaton plaza driver mota ya dire su ya fito ɗauke da BABY a ƙaffaɗarsa kuɗinsa ya basa sannan ya shiga shagon yana ɗan ɗari-ɗari ganin shagon babba sosai, da fara'a mutanan plaza suka tarbe sa dan SHAHEED yana da ruwan aje butter baka taɓa cewa daga ruga ya fito sauƙin sa kuma yayi karatu basa da duhun kai ko kaɗan, tanbayarsa sukayi me yake so ataƙaice ya ce, "waya.! wayoyi suka kwaso masa waƴanda ake yayi azamanin, hannu BABY takai kan wata waya open and close reza, da murmushi SHAHEED ya ce, "ita kike so BABY.? ɗaga masa kai tayi cikin jin daɗi kuɗin wayar ya tanbaya aka faɗa masa, nan ya lalo kuɗin ya bada cas tare da siyan sim dan komai ana siyarwa aplaza na waya, harda kati ya siya ya zuba a sim ɗin waya ya ara kafin yasa wannan charge ya kira NUHU suka gaisa sannan yayima NUHU bayanin abinda yake buƙata daga ɗaya ɓangaran NUHU yace karya damu yana hanyar zuwa gidan, katse wayar SHAHEED yayi ya miƙa ma mai waya wayarsa suka fito daga plaza BABY na riƙe da kwallin wayar da suka siyo ya tara masu taxi suka dawo gida.A parlour suka samu NABIL ya mimiƙe saman kujera ya kunna tv yana kallo, baki da hanci duka hangame dan ko sallamar su bai jiba miƙewa zaune yayi ya ce, "sannu da zuwa Hamma"
"yauwa NABIL NUHU bai riga mu isowa gida ba.?
"Eh bai zo ba.! rufe bakin NABIL yayi daidai da sallama NUHU iso SHAHEED ya masa har ciki shi da wani suka shigo mai refilling gas, kitchen suka shiga aka duduba gas ɗin komai nasa lafiya lau gas ne babu mutumin yayi refilling sannan, duk ya gwadawa SHAHEED yarda zaiyi using komai godiya SHAHEED ya masa tare da biyansa kuɗinsa, suka fito ya raka su har compound, BABY na maƙale da shi anan NUHU ke tanbayarsa ya jikin Ummansa "da sauki.! SHAHEED ya faɗa yana ba NUHU wasu ƴan canji washe baki NUHU yayi ya ce, "har da wata ɗawainiya SHAHEED kai da kake da mara lafiya" sosa ƙeyarsa SHAHEED yayi yana murmusawa ya ce, "insha Allahu Umma na samun sauƙi zan neme ka, ina son mu je kasuwa na buɗe shago na fara kasuwanci kan abinda kake ganin zai karɓu" washe baki NUHU yayi ya ce, "to, to gaskiya kayi tunani mai kyau SHAHEED gara ka fara kasuwacin musanman yarda kuɗin gado suke, basu da albarka idan aka sanya wasa sai ka ga duk sun ɓalgace a banza" SHAHEED dake saurara NUHU dan duk atunanin NUHU kuɗin gado SHAHEED ke ci kamar yarda wadda ya haɗasu ya faɗa masa kenan, sun ɗan jima suna tattaunawa kan kasuwancin da SHAHEED ɗin zai fara ƙarshe suka tsaida magana kan za'a fara nema masa shago kasuwa, sannan sai asan abunyi idan Umma ta samu sauƙi da haka sukayi sallama da NUHU ya dawo cikin gida.
Kitchen ya nufa direct ya bar BABY parlour tana kallo ita da NABIL, fraying dankalin yayi da ƙwai ya zuba ma NABIL nasa a plate, ya haɗa nasa da BABY dan yana son ta ci abinci sosai, parlour ya dawo hannunsa ɗauke da plate NABIL ya taimaka masa ya amsa ya aje ya shiga bedroom ya ɗauko flask na ruwan zafi da kayan tea ya dawo, turawa NABIL abincin sa yayi gabansa ya haɗa masa tea ya basa, hannu ya miƙa ma BABY ta kama ya zaunar da ita saman cinyarsa yana bata abincin tana amsa, itama tana sanya hannunta cikin plate ɗin tana ɗebowa tana basa yana amsa, wannan karan yana ɗebowa ta girgiza kai alamar ta ƙoshi SHAHEED ya ce, "me yasa BABY baki son cin abinci zamu ɓata" SHAHEED ya faɗa yana ɓata fuska shuru BABY tayi tana wasa da hannunta mai maiƙon chips SHAHEED ya ce, "ki ɗan ƙara ko kaɗan koda tea ne okay" cup ɗin tea ya sanya mata abaki sipping biyu zuwa uku ta ture cup ɗin tana ɓata fuska ta ce, "na ƙoshi" kallonta SHAHEED yayi sosai ya ce, "mu ji cikin.? ya faɗa yana mamatsa cikin dariya BABY ta saki da ƙarfi ta miƙe da gudunta, bayan NABIL ta tafi ta ɓoye tana dariya, saita leƙo da kanta suna 4eyes da SHAHEED sai ta ɓoye bayan NABIL tana dariya miƙewa SHAHEED yayi yana cewa, "duk ki gama gudun zan kama ki ne" ya faɗa yana hanyar kitchen plate ɗin da suka gama using shi da BABY bayansa BABY ta bi tana cewa, "SHEED goya ni.! ta faɗa cike da shagwaɓa duƙawa SHAHEED yayi ta haye bayansa yana wanke plate ɗin da suka ɓata NABIL ya shigo kitchen ɗin shima, ƙeyar BABY ya tallaba cike da mugunta da kishi ganin yarda baki ɗaya ta kwace gatan daya ke samun wajen yayansa siririn kuka ta saki ta ce, "SHEED.! waigowa SHAHEED yayi, yayinda NABIL yayi fuska yana harkokinsa SHAHEED ya ce, "me ka mata.?
"ni kuma babu abinda na mata." karfin kukanta BABY ta ƙara SHAHEED ya ce, "sorry BABY idan ma dukanta kayi zan kama ka you know." NABIL dake huhura haci kamar baiyi komai ba SHAHEED na waigawa yayi mata gwalo ya ƙara miƙa hannun zai ja jela gashin kanta, SHAHEED ya waigo da gudu yayi parlour SHAHEED ya bisa yana cewa, "ai fa sai na rama mata duk ka gama gudun ka" parlour suka shiga zagayewa BABY na baya tana dariyar jin daɗi da sun kuskure kama NABIL ta ce, "SHEED.! da ƙarfinta tana dariyar jin daɗi kamasa SHAHEED yayi ya ce, "Oya juya mun ƙeyarka.! juyawa NABIL yayi yana hakkin gudun da suka sha yana cewa, "wannna mai sufar aljannu sherri take mun"
"juya mun keya kawai ai na ganka" juyar da shi SHAHEED yayi ya dadage ya fale masa ƙeya "aushhh.! NABIL ya furta yana kama ƙeya dariya BABY ta saki tana masa kwallo dalla mata harara yayi yana cewa, "ke ko na kama ki zaki sani wallahi" bayan sun gama abinda suke direct asibiti suka wuce.
Yau ma kamar jiya Umma na kwance har cikin zuciyarsa SHAHEED ke jin babu daɗi rashin tashin Umma, abun na damunsa kawai yana nuna rashin damuwarsa ne fili, dan kar yaran su shiga damuwa amma a baɗili yana mugun damuwa da jikin Umma, kujera ya ja ya zauna kusa da Umma dake kwance ahankali ya furta, "Allah ya baki lafiya Umma.! NABIL dake gefe ya amsa da "Amin.! kira sallah azahar ya sasu fita daga ɗakin suka tafi masallaci suka bar BABY tare da Umma.
Umma dake kwance ahankalin hannayenta suka fara motsawa BABY dake zaune ƙasa tana wasa, ganin hannun Umma na motsawa kamar da wasa yasata, miƙewa ta nufi bakin gadon tana kallon fuskar Umma amma still idanunta rufe, Ahankali breath ɗinta ke fita, yayinda numfashinta ke sauka sannu-sannu ahankali take buɗe idanunta kaɗan-kaɗan wayanda suka mata taushi tana bin ɗakin da kallo ko ba'a faɗa mata ba ta fahimci asibiti take, sosai idanunta suka sauya kala daga farare zuwa kalan ja, sannan lokaci guda suka ƙanƙance sai tarin eye lashes dake samansu wanda yayi wara-wara, sauke idanunta tayi kan kyakyawar yarinyar dake bakin gadon tayi wadda ke sakin murmushi gashin kanta duk ya warwatse ya zubo har bayanta, idanunta manya ƙwayar cikinsu brown dimple ɗinta na lomawa ta ƙara matsowa kusa da Umma sosai ta washe haƙoranta duka, hannunta BABY ta ɗaga ta mata bye-bye still tana murmushi, lumshe idanunta Umma tayi wani irin ciwo da nauyi ƙirjinta ke mata jin wani abu take ya tamke mata ƙirji kamar ya tokareta, ba komai bane sai belt ɗin da aka tallaɓo gaboɓin ƙirjinta dashi, sauƙe wata gajiyayyar ajiyar zuciya Umma tayi, ahankali ta ɗan yunƙura tana ƙoƙarin cire oxygen ɗin dake hancinta dan duk ya dameta, BABY dake gefe ahankali ta ce, "Umma.! tana kuma leƙa fuskar Umma da ko magana ta kasa saboda yarda bakinta ya mata nauyi sam ta kasa gane BABY dan ta mata kyau ba kamar lokacin da tana cikin ciwo ba take ganinta, a yau sai ta ganta kamar wata ƴar larabawa murmushi ƙarfin hankali Umma ta saki hakan yayi daidai da shigowar su SHAHEED ɗago manyan idanunta BABY tayi da sauri ta nufi SHAHEED tana nuna gadon tana cewa, "SHEED Umma..! da sauri SHAHEED yayi bakin gadon cikin tsantsar farin ciki ganin Umma ta farka idanunsa ne suka kawo ruwan hawaye na tsantsar farin ciki, Umma kuwa sosai mamakin sauyawar ƴa'ƴanta ke bata mamaki ganin yarda suka murje kwana biyu ba kamar SHAHEED da yayi kamar black american, NABIL kuwa ya ƙara jajur.
Hannunsa SHAHEED yakai kan wani ɗan abu jikin gadon Umma, ba'a fi minti 4 ba saiga wata Nurse tashigo cikin ɗakin da sauri, ganin idanun UMMA biyu tayi kanta, waje SHAHEED yaba nurse ta ƙarasa kusa da Umman sosai ta zare mata oxygen ɗin dake saman hancinta, da taimakon SHAHEED Umma ta yunƙura nurse ta jingina mata pillow tashiga tambayarta jikin nata, da kai kawai ta iya amsa mata, ganin haka yasa tafita da hanzari don ƙiran Dr.
Baƙaramin daɗi Dr yaji ba sakamakon jin cewa UMMA SHAHEED ta tashi, dan yana ganin ƙoƙarin yaron sosai yarda yaketa faɗi tashi tunda suka zo asibitin, ba dangi uwa bare na uba daga shi sai ƙannansa, da ƙwarin gwiwarsa haka ya nufo ɗakin da UMMAN take kwance.
Checking ɗinta yayi sosai sannan ya tambayeta ko akwai wani abu dake damunta, kai kawai Umma ke iya girgizawa, sannan Umma ta masa nuni da ƙirjinta daidai inda aka ɗaure mata da belt, alamar nanne kawai ya takura mata sosai, sannu doctor yamata ya ce, "insha Allah komai zai zama lafiya lau da sannu" jinjina kai Umma tayi sannan doctor ya fita murmushi SHAHEED yayi ya ce, "mi warti Umma" jinjina kai Umma tayi ahankali ta ce, "zan sha ruwa.! bottle na ruwa SHAHEED ya ɗauko mata ya buɗe ya bata, kallon robar Umma take tayi, tana mamakin ina SHAHEED yayi kuɗin siyan ruwan gora.....*Follow me on facebook page n group*: *salma mas'ud nadabo*
*Follow me on IG*: *Salmerh 777*
#VOTE
#COMMENT
#SHARE~Taku har kullum salma mas'ud nadabo~
YOU ARE READING
WATA ƘADDARA
ActionKo wani bawa nada tasa zanan ƘADDARA sai dai shi tashi tasha banban data saura, komai ya farune daga ranar da mahaifiyarsa ta kwanta ciwo, ya buga ya nema domin sama mata kuɗin magani dana asibiti duk da yana matashin saurayi mai ƙarancin shekaru ɗa...