🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
*And*
*Written*
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}*WATTPAD*
*salmamasudnadabo*https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg
*FREE PAGE*
*Page: 11*
*Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*
.......Abubuwa da yawa ne suka taru sukayiwa Umma yawa akai, a iya saninta basu da arziƙin zuwa asibiti irin wannan dan tasan SHAHEED bashi da kuɗi, zuciyarta sai saƙe-saƙe take har SHAHEED ya kai mata gora ruwan bakinta kaɗan tasha ta ture gora tana binsu da kallo, sosai yaranta suka mata kyau raurau idanunta sukayi tana kallon SHAHEED dake zaune bakin gado kusa da ita lura da yanayin Umman yasasa furta, "menene Umma..? girgiza masa kai tayi lokacin wasu hawaye masu zafi suka samu nasara zubo mata shar, zagayeta yaran sukayi cikin raunin murya SHAHEED ya ce, "menene Umma me ke maki ciwo.? girgiza masa kai Umma tayi tana shasheƙar kuka suma yaran kuka suka saki harda SHAHEED yana mai kuma tanbayar Umma me damuwarta, BABY kam ganin SHAHEED na kuka itama ta zage tun karfinta tana kuka ta ɗaura kanta saman cinyarsa, girgiza masu kai Umma tayi cikin muryarta mai rauni ta ce, "babu abinda ke damuna ganin ku cikin ƙoshin lafiya ya mun daɗi, baki ɗaya kun sauya, ba kamar kai BOƊOƊO har girma ka ƙara" Umma ta faɗa tana goge ma SHAHEED hawayen kan fuskarsa ta goge ma NABIL nasa ma BABY da kanta ke saman cinyar SHAHEED tana shesheƙar kuka, ahankali Umma ta ɗaura hannunta saman kan BABY ɗago jajayen idanunta BABY tayi, kallonta Umma take sosai can ta ce, "BOƊOƊO ina ka samo wannan yarinyar.? Umma ta jefa masa tanbayar, ƙirjin SHAHEED sai daya buga duk da yasan dole dama Umma ta tanbayesa duk lokacin data samu sauƙi, duk abinda ya faɗawa AMMIE shi ya kwashe ya faɗawa Umma jim Umma tayi ta ce, "amma yanzu idan iyayenta suka gane tana rugar mu suka je, basu samemu ba mai kake tunani MAGAJI.? SHAHEED da kansa ke ƙasa ya ce, "na faɗawa AMMIE ta faɗa masu muna NIGER, koda na barta can bazata iya zama ba Umma" jinjina kai Umma tayi ta ce, "Allah ya bayana iyayenta toh" da "Amin.! SHAHEED ya amsa can ƙasan.
Miƙa ma BABY hannu Umma tayi ba musu BABY ta tafi gareta tana murmushi Umma ta ce, "ya sunaki.? shuru BABY tayi tana nazari dan har ta manta sunata na gida kallonta Umma ta maida kan SHAHEED ta ce, "ya suna ta.?
"Ni ma ban sani ba, ina dai kiranta da BABY ne kawai" SHAHEED ya faɗa murmusawa Umma tayi gami da yunƙurawa zata tashi, SHAHEED ya taimaka mata ta sako ƙafafunta ƙasa kama ta SHAHEED yayi suka taka har bakin kewaye, kamar yarda Umma ta buƙata har ciki ya taimaka mata ta shiga sannan ya fito yana jira ta gama biyan buƙatun ta, wanke fuskarta UMMA tayi ta kuskure bakinta gami da ɗauro alwala bayan ta kama ruwa ahankali ta ce, "MAGAJI.! da "na'am.! SHAHEED ya amsa tare da shigewa toilet ɗin ya kama hannunta suka fito saman gado ya zaunar da ita gami da umartar NABIL ya shimfiɗa mata sallaya, hijab SHAHEED ya miƙa mata tare da kama hannunta ya zaunar da itama saman dadumar, a zaune Umma ta gabatar da salolinta bayanta idar SHAHEED ya ɗauki flask da cup ya haɗa mata tea mai kauri ya miƙa mata mug ɗin amsa Umma tayi tana kallon cup ɗin dan sam bakinta babu daɗi ahankali SHAHEED ya ce, "ki samu ki ci wani abu Umma" jinjina kai tayi gami da fara sipping tea ahankali ba laifi tasha rabin cup ta miƙawa BABY dake kusa da ita ba musu ta amsa tana sipping tea Umma ta ce, "a ƙaro maki da biredi.? girgiza kai BABY tayi shafa kanta Umm tayi ta furta, "masha Allah yarinyar na da kyau, lokaci ɗaya na ji ta shiga raina MAGAJI" Umma ta faɗa tana kuma faɗaɗa murmushinta.
Sai dare sosai su SHAHEED suka bar asibiti duk da sun so kwana amma ba'a bari, ita kanta UMMA taso su kwana nan kusa da ita sai dai likitocin asibitin sun hana babu yarda ta iya tana kallo suka tafi, zuciyar SHAHEED fal da farin ciki suka dawo gida, wanka da brush kawai sukayi kowa yabi lafiyar gado.
YOU ARE READING
WATA ƘADDARA
ActionKo wani bawa nada tasa zanan ƘADDARA sai dai shi tashi tasha banban data saura, komai ya farune daga ranar da mahaifiyarsa ta kwanta ciwo, ya buga ya nema domin sama mata kuɗin magani dana asibiti duk da yana matashin saurayi mai ƙarancin shekaru ɗa...