WATA ƘADDARA

79 3 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
                   *WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
      *And*
          *Written*
                  *By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}

       *WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
         

https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg

   *FREE PAGE*

*Page: 13*

            *Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*

          ......Kama hannun SHAHEED BABY tayi tana kallonsa tana murmushi ɗaurata saman cinyarsa yayi ahankali ya ce, "daga yau suna ki HANIFA, HANIFA Hamma SHAHEED" ɗaga kai BABY tayi ta ce, "HANIFA Hamma SHAHEED" SHAHEED ya ce, "sunaki.?
    "sunaki.! ja mata karan hanci SHAHEED yayi ya ce, "suna ki" dariya ta saki ta ce, "suna ki" baki ɗaya dariya suka saki NABIL ya ce, "ƴar ƙauye me maimaita magana ana nufin ke ce HANIFA toh.? harara BABY ta dalla masa tana murguɗa masa baki ta ce, "SHEED.! tana nuna NABIL SHAHEED ya ce, "rabu da shi zanyi maganisa ne.
   
    Daddare koda su Umma zasu kwanta sai da aka sha fama da HANIFA dan bata san zancan kwana da Umma ba, da dibara da komai Umma ta lallaɓata ta kwana da ita.
         Tun daga lokacin HANIFA ta dawo ɗakin Umma da kwana kuma sannu ahankali ta fara daina fitsarin kwance, duk da cewa Umma sai da tasha fama kafin BABY ta saba kwana da ita dan sau tari sai ta fara bacci SHAHEED ke tafiya ɗakinsu, ko kuma ta tafi ɗakinsa sai tayi nisa bacci ya maidota ɗakin Umma ahaka dai har ta fara sabawa.
    
         ******
   
    Zaune take ta sanya hoton ILHAM gaba yayinda wasu hawaye masu mugun zafi ke gangarowa saman fuskarta wadda tayi ja saboda tsabar kuka, TOFIK dake kusa da ita yasanya hannu yana goge mata hawayen kan fuskarta ɗagowa tayi tana kallon yaran nata TOFIK MUBINA ISLAM ta ce, "shikenan ƙanwar ku ta tafi, har yanzu babu wani labari, tun ina irga kwana har na fara irga wata, daga wata ɗaya na koma irga watani shikenan ƴata ILHAM ta tafi kamar wata ƴar tsana ba ƴar mutum ba." Abba da shigowarsa yanzu kenan ya samesu cikin wannan halin wanda tun bayan tafiyar ILHAM gidan ya koma haka, dan sam Mama bata farin ciki kullum cikin kuka take wanda yanzu ya zamar mata jiki zubar da hawayenta Abba ya ce, "insha Allah ILHAM zata dawo gare mu fatana Allah ya bayanata ZALIHA" Mama dake kuka wiwi ta ce, "uhmm Allah yasa" Mama ta faɗa cikin sakin kuka zama kusa da ita Abba yayi ya ɗaura kanta saman kaffaɗarsa yana shafa bayanta alamar lallashi yana cewa, "don Allah ZALIHA ki rage kukan nan ko dan abinda ke cikin ki, Allah kaɗai yasan dalilinsa na bamu wannan cikin bayan ya ɗauke ILHAM, bai ɗauke ILHAM daga gare mu ba sai daya baki wani cikin, ya kamata ki zama mai godewa rahamar Allah duk da cewa abun da ciwo, bamu san rayuwar da ƴar mu ke ciki ba shin ta mutu tana raye wani hali take ciki." tsananta kukanta Mama tayi mai sauti babu irin tunanin da batayi wanda yafi hakan muni, ta ce, "shikenan ILHAM shikenan ta tafi har yau hukuma ta kasa komai akai, ina jin ciwon rashin ƴanta KHABIR, ina jin ciwo" Mama ta faɗa araunane tana kuka mara sauti sai zalla hawaye idanunta har kunbura sunyi jajur dan kuka ɗagata tsaye Abba yayi ya ce, "insha Allahu hukuma zata gano inda ILHAM dake har yanzu ban cire tsamani ILHAM zata dawo  ba, ki dai kuka kin ji Maman Twins" Abba ya faɗa yana sanya hannu yana gogewa hajiya zaliha hawayen kan fuskarta sannan ya maida kallonsa kan TOFIK ya ce, "TOFIK ku kwaso kaya a booth" fita sukayi yayinda su Abba sukayi bedroom yana aikin lallashin Mama da cikinta ya kai 4month ya ɗan fito.
   
   
               ******
   
    A gurguje yake tura bread yana sanye cikin uniform ɗinsa na school yana cewa, "HANIFA kiyi da jiki ke kaɗai muke jira fa me kikeyi ne.? SHAHEED ne ya fito yana sipping tea da sauri-sauri yana cewa, "BABY what are you doning" Umma ce ta fito daga kitchen tana cewa, "a'a har yanzu bata fito ba na shiryata fa tsaf me ta tsayayi kuma.?
      "Umma taso mana keyarta please, ta san fa na makara kasuwa zan tafi kuma ina son aje su makarantar, naga yarda za'ayi duk da na gama komai classes kawai za'a basu," Umma ta ce, "matsala NABIL kumafa kun warware.?
     "Eh mun warware komai, insha Allah zasu ajesa jss one, sai na sama masa lesson teacher ya dinga koya masa french har ya goge tunda shine matsalasa"
     "toh ai shikenan bari na kirata to" kafin Umma ta kai aya HANIFA ta fito kanta acukurkuɗe duk ta haukatasa kamar Umma bata gyara mata ba, tana shirye cikin uniform ɗinta doguwar riga mai yar ciki, ƙugu SHAHEED ya riƙe yana kallonta daga sama har ƙasanta, aje mug ɗin hannunsa yayi saman stool ya ce, "zo nan.! fuskarsa tamke mannewa tayi da jikin ƙofar ɗaki tana raba idanu aɗan tsawace SHAHEED ya ce, "am talking to you my friend" da sauri ta taho tana mamatse hawaye Umma ta ce, "haka kika maida gashin naki HANIFA bayan na gyara maki shi" Umma ta faɗa tana dafe goshi NABIL dake tutura bread ya ce, "ai dama haka BABY take sam abu na burgewa bata so, tafi ganewa kanta akullum a haukace, kuma duk idan zamu fita sai ta mana african time da wani ƙaton kanta kamar jirgi" NABIL ya faɗa yana bala mata harara kama hannunta SHAHEED yayi tun kafin yace, mata kan zil ta fara matse hawaye ba tare daya kalleta ba ya ce, "NABIL ɗako mun kit ɗinta na gyaran gashi tunda ta rantse na zama bawanta" ɗaki NABIL ya shiga ya fito da kit ɗin SHAHEED ya buɗe yana cicin magani Umma ko dariya abun ya bata, tayi kitchen ta barsu nan raba mata gashin kanta biyu SHAHEED yayi yasaka mata ribbon ya mata two babies da gashin ya ce, "ungo maida kit ɗin ki dawo bawan naki ya gama" turo baki tayi tana tafiya kamar wadda kwai ya fashe mata aciki SHAHEED ya ce, "zakiyi sauri koko.? ƙara sauri tayi, jim sai gata ta fito.
           Umma da fitowar ta daga kitchen kenan ta miƙa mata lunch box ɗinta gami da shafa kanta ta ce, "a kula ban da wasa a maida hankali kan karatu.! ɗaga kai HANIFA tayi SHAHEED dake tsaye riƙe da school back ɗinta ya ce, "Oya mu je.! ɗaga masa hannun tayi alamar ya ɗauketa tana washe baki harara SHAHEED ya tsila mata ya ce, "ba'a ɗaukar naki, kiyi tafiyar ki da sayada atoh," turo baki tayi tana sonyin kuka gami da togewa jikin bango, ƙwafa SHAHEED ya saki sai kuma ya kai hannun ya ɗauketa.
           Machine dake fake compound ɗin gidan SHAHEED ya nufa ya ɗaura BABY gaba ya tada machine ɗin NABIL ya buɗe masu get, Umma dake tsaye daga bakin ƙofa tana ɗaga masu hannu, har NABIL ya maida get ya kule ya hau bayan machine SHAHEED na tsakiya suka ɗau hanyar school suna tafiya BABY na cewa gudu "Hamma na SHEED.! aiko SHAHEED biye mata yake suna gudu idan sun wuce masu abun hawa ta masu gwalo ko ta juya idanunta, kamar yarda sukeyi ita da SHAHEED da alama BABY ta fara zama mai ƙiriniya dan baki ɗaya sanyin nan nata ya tafi duk wanda ya ganta sai ya gane cikin maza ta taso, suna isowa school office ɗin princinpal suka nufa bayan sun gama duk abinda suke aka haɗa NABIL da wani malami yakai sa JSS1, SHAHEED ya basa kuɗin break kana ya wuce aji, wata malama dake ɗaukar su HANIFA a Nursery class princinpal ya kira ya ce, "malama ki wuce da wannan anjinki.! har malama sunyi gaba SHAHEED ya ce, "malama waigowa" malama tayi fuskarta sake SHAHEED ya ce, "ban yarda da dukan BABY mara dalili ba, idan kuma hakan ya faru zan zo har nan na rama mata" kallonsa malamar tayi gami da kallon BABY data haɗe gira sama data ƙasa hannunta naɗe a ƙirji, tana kallon malama sannan ta maida kallonta ga SHAHEED da fuskarsa ke tamke yana kallon malamar ya ce, "ko sai na maimaita, ban amince a taɓa mun lafiyar BABY ba, taɓata kuwa daidai yake da cireta a makarantar nan tare da ɗaukar mumuna mataki.! azuciyarta kuwa malama ta ce, "wannan wani irin yaya ne ko uba dan SHAHEED ya tsere mata dan zai iya haihuwarta inda shi macece, princinpal dake zaune ya ce, "kuna iya tafiya malama, insha Allah makamancin hakan ba zai taɓa faruwa ba ranka yadaɗe.! SHAHEED dake zaune suka gama tattaunawa da princinpal wanda mamakin SHAHEED bai sake sa ba.
   
            Malama kuwa da harara tabi HANIFA tana ayana yarda zata ci ubanta sai dai yayan nata ya kasheta, suna shiga class aka bata set ta zauna ba tare da tanka kowa ba, malama ta ce, "ga sabuwar student kunyi HANIFA ABUBAKAR." baki ɗaya hankalin ƴan class ɗin kanta ya dawo suna kallonta sannan kuma darasi ya cigaba.

          Misalin ƙarfe 12:00pm su HANIFA suka tashi daga school tana fitowa ta hango machine ɗin SHAHEED, washe baki tayi cike da tsantsar farin ciki.
       Takowa SHAHEED yayi wajenta ya amshi school back ɗinta da lunch box ɗin hannuta ya ce, "baki ɗaya BABY ta gaji ko.? ɗaga masa kai HANIFA tayi tana cewa, "na gaji sosai kam Hamma na"
"Sannu BABY.!
"Yauwa Hamma na"
"kina maida hankalin kan karatun ki sosai kuwa BABY.?
"Ina mai dawa hamma ai ka ce nayi ƙoƙari zaka siyamun keke"
"wannan haka yake zan siya maki duk abinda kike so shaleleta" SHAHEED ya faɗa yana ɗaurata gaban machine suka ɗauki hanyar zuwa gida.
      SHAHEED na parking machine HANIFA tayi cikin gida da gudu tana cewa, "Umma na dawo." Umma dake zaune tana kallon tv HANIFA ta faɗo jikinta tana cewa, "Umma na gaji."
"sannu HANIFA, ina hamman naki SHAHEED da NABIL"
  "Hamma NABIL mun barsa a makaranta, Hamma na SHAHEED na waje yana gyara parking machine a waje"
    "Toh madallah muje a cire uniform ayi wanka aci abinci ko" Umma ta faɗa ta jan hannunta SHAHEED ya shigo saman kujera ya faɗa ya zauna, tare da gaida Umma ta amsa ataƙaice har Umma sun shiga bedroom ta fito da sauri tayi kitchen tunawa da tabar miya kan wuta cikin ɗaga murya ta ce, "MAGAJI taimaka kayi ma BABY wanka na gama haɗa komai na wankan kuma gashi zan soya miya" SHAHEED dake kishingiɗe saman kujera ya ce, "toh.! miƙewa SHAHEED yayi ya nufi ɗakin Umma bakin dressing mirror ya hango BABY na ɓarna da hoda ya ce, "BABY me kikeyi haka.? ɗagowa tayi ta ce, "kwalliya hamma nayi kyau.? ta faɗa tana turo bakinta daya sha jan baki da kwalliyarta ta mahaukata ƴar dariya SHAHEED yayi ya ce, "BABY kenan ai ke kyakyawa ce sai dai ki ƙarawa kayan ƙwalliyar kyau" washe baki BABY tayi SHAHEED ya ce, "mu je ayi wanka"
           Agurguje SHAHEED yayi ma BABY wanka bayan ta gama ciƙesa da ruwan wankan, suka fito tana naɗe cikin towel saman gado ya cilata, dariya take saki ta miƙe tsaye tana rawa ɗaure da baby pink towel ɗinta sai kanta da SHAHEED ya naɗe da ƙaramin towel, kit ɗinta ya ɗauko na kayan shafa dan siyaya yake mata sosai komai nata na daban ne kama daga kayan shafanta zuwa na gyara gashin kanta, kit-kit yake mata dole ka kalla abun ya baka sha'awa dan gata take samu wajen SHAHEED bana wasa ba, lotion ya ɗauko yana shafa mata itama tana rigimar ɗiba da kanta tana shafawa, har ya kamala shafa mata, uniform ya ɗauko mata na islamiyya riga da wando ash da hijabi yasaka mata ta fito fes, ɗaukar ta yayi cak  hannunsa riƙe da hijab ɗinta, suka wuce parlour suna zama Umma ta fito da trayn abincin su ta aje masu a parlour, shinkafa da miya ne ta saka spoon ciki zama tayi yayinda BABY ke saman cinyar SHAHEED suka fara cin abinci, SHAHEED na bata abaki Umma na bata, duk wanda ya bata amsa take cikin su, cikinta ta fara shafawa alamar ta ƙoshi Umma dake kallonta ta ce, "karki soma faɗa mun kalmar ƙoshi anan" turo baki HANIFA tayi idanunta raurau kamar zatayi kuka Umma ta ce, "haa.! buɗe bakin tayi ahankali ganin ba wasa kan fuskar Umma da SHAHEED dake kallonta Umma tasa mata abincin tana taunawa ahankali Umma ta ce, "da kyau shalelen Hammanta SHAHEED" Umma ta faɗa tana kallon SHAHEED ta ɗebo shinkafar ta nufi bakin SHAHEED ta ce, "hamm.! buɗe baki SHAHEED yayi ya amsa  BABY dake zaune saman cinyarsa itama ɗebowa tayi takai masa baki, ya masa yana sakar mata murmushi shima ya ɗebo ya kai mata baki ta amsa da wayau da komai yau BABY taci abincin da yawa ba tare da ta gane hakan ba, Hijab ɗinta SHAHEED ya zura mata ya kama hannunta suka fita zuwa kaita islamiyya, suna isa islamiyyar SHAHEED yayi parking machine ya sauko da BABY daga saman machine ya miƙa mata jakarta ta islamiyya ta amsa tayi hanyar aji tana tafiya ahankali tana waigowa tana ma SHAHEED bye, SHAHEED dake tsaye yana kallonta ya ce, "BABY yau kin mata da chocolete ɗin ki" tsayawa BABY tayi cak SHAHEED ya zo wajenta ya ce, "ga chocolete ɗinki nan BABY, ki maida hankali sosai ban da wasa kin ji" ɗaga masa kai tayi tana masa bye-bye yana mata har ya hau saman machine ɗinsa ya wuce kasuwa.

*Follow me on facebook page n group*:  *salma mas'ud nadabo*

*Follow me on IG*:  *Salmerh 777*

#VOTE
#COMMENT
#SHARE

~Taku har kullum salma mas'ud nadabo~

WATA ƘADDARAWhere stories live. Discover now