🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
*And*
*Written*
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}
*WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg
*FREE PAGE*
*Page: 14*
*Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*
.......Washe gari koda HANIFA taje school malamar su na ganinta ta ce, "ke zo nan" miƙewa HANIFA tayi ta ƙarasa wajen malama ta ce, "malama gani" kallonta malama tayi sama da ƙasa ta ce, "wato ke ce wadda yayanta ke ɗaure mata ƙugun iskanci a makaranta ko.? girgiza kai HANIFA tayi ta ce, "Hamma ba haka yake ba malama.?
"yi mun shuru munafuka mara kunyar ƙarya daga ke har yayan naki baku fi ƙarfi na ba, kuma mindin kika mun laifi sai na ladaftar dake" malama ta faɗa ta jan kunna HANIFA ƴar ƙara ta saki ta ce, "malama kiyi haƙuri" ta faɗa tana son fashewa da kuka sakinta malama tayi ta ce, "wuce ki ban guri kafin na sauya maki kamannin da yayan naki zai kasa gane ki" da sauri HANIFA ta koma sit tana son yin kuka bakin ta gaba har aka tafi break ko abinci break ɗinta bata ci ba wata ƴar class ɗin su wadda sit ɗin su ɗaya ta ce, "HANIFA bakiyi break ba, me yasa.?
"Bana jin yunwa, kuma Hamma ya zo ɗaukana sai na faɗa masa abinda malama tamun"
"Kiyi haƙuri HANIFA"
"bana haƙura sai Hamma ya ramamun" HANIFA ta faɗa cikin jin haushi ta tashi ta bar ƙawarta nan tsaye ta wuce class.
Misalin ƙarfe 12:00pm aka tashe su HANIFA tare da ƙawarta suka fito ƴar sit ɗin su, suna fitowa filin makarantar ta hango machine ɗin Hamma da sauri ta ƙarasa wajen machine ɗin fuskarta kumbure tak take jira ta fashe da kuka, SHAHEED da tunda ta nufo machine ɗin yake kallonta tana isowa ya sauka daga saman machine ɗinsa ya ce, "me ya faru BABY naga fuskar ki haka..? turo baki HANIFA tayi ta ce, "ba malama bace ta kusa kasheni ba har kunne na ta ja mun ban mata komai ba, kuma tace sai tayi magani na har ma da kai" HANIFA ta faɗa tana son fashewa da kuka SHAHEED da annurin fuskarsa ta ɗauke ya ce, "haka malamar tace."
"Eh haka tace, wasu maganganun nata bana ganewa ma tana ta zagi na kuma tana zaginka" kama hannunta SHAHEED yayi ya ce, "mu je na gyara mata zama.! malama dake ƙoƙarin fitowa daga office ɗin malamai ɗago idanun da zatayi sukayi ido huɗu da SHAHEED da fuskarsa ke tamke babu alamar fara'a kanta, tsuru-tsuru malama tayi tana kallonsu kafin malama tayi wani yunƙuri SHAHEED ya kwasheta da mari, ji kake tas tas hagu da dama baki ɗaya hankalin mutane wajensu ya dawo saboda saukar marin, nuna malama yayi da ɗan yatsa ya ce, "duk rashin kunyar me rashin kunya bai isa ya taba mun BABY ya kwana lafiya ba, shashasha wadda bata iya kula da ɗalibanta ba.! SHAHEED ya faɗa yana watsa mata mugayan idanunsa ya kama hannun BABY ya ce, "na cire ki daga makarantar nan daga yau.! baki ɗaya idanun mutane kansu SHAHEED ya koma daya ɗauki BABY ita kanta BABY batayi tunanin hukuncin da zai ɗauka ba, dariya ta saki suna hawa saman machine SHAHEED ya ja machine ɗinsa bayan ya baɗe malama da ƙura.
Suna isowa gida da gudu ta danna parlour tana dariya jin zuciyarta take fes ganin cewa duk iskancin data shuga akwai me ɗaure mata ƙugu, saman kujera ta faɗa tana dariya tana sauke numfashi tana kwallawa Umma kira fitowa Umma tayi ta ce, "har an dawo kenan" bakin HANIFA washe ta ce, "Umma kin san yau me ya faru a makaranta.? girgiza kai Umma tayi ta ce, "a'a BABY sai kin faɗa mun" dariya HANIFA ta kuma saki tana shewa tana faɗawa Umma abinda ya faru zaro ido waje Umma tayi ta ce, "Shi MAGAJIN yayi haka.? dariya HANIFA ta saki ta ce, "Umma baki gani ba yarda ya ɗauke malama da mari, wallahi na ji daɗi Hamma ya mun daidai kuma ya cire ni daga makarantar su" HANIFA ta faɗa tana cire safar ƙafarta SHAHEED ya shigo kallonsa Umma tayi ta ce, "abun da kayi daidai ne kenan ko MAGAJI.? a haka zaka koyawa HANIFA tarbiya SHAHEED.? SHAHEED dake saurara Umma ya ce, "dukanta fa tayi ba laifin tsaye bana zaune har ta kusa kasheta, ko ba haka bane BABY.?
"Haka ne Hamma malamar muguwace fa Umma" gyaɗa kai Umma tayi ta ce, "hmm.! tayi ciki ta barsu nan suna raba idanu dariya BABY ta saki tana toshe baki kumatunta SHAHEED ya ja miƙewa tayi tsaye tana ɗaga masa hannayenta alamar ya ɗauketa ɗaukarta yayi cak ya ce, "kina son makarantar kona canza maki wata BABY.? girgiza kai BABY tayi ta ce, "bana so a canza duk ƙawayen cikin makarantar basu so na sun fi son malama."
"aiko an gama shima NABIL na dawowa ya gamata sai dai a nemo maku sabuwa wadda tafi wacan kyau ma ko" ɗaga kai BABY tayi tana murmushi ta kuma ƙanƙame SHAHEED.
Daddare suna cikin dinner yayinda SHAHEED ke feeding HANIFA tana amsa tana basa ya ce, "NABIL na cire ku daga wannan makarantar." NABIL ya ce, "me yasa Hamma.?
"Saboda zasu kashe BABY.! zaro ido NABIL yayi ya ce, "wani mara mutuncin ne ya taɓaki BABY.! HANIFA da bakinta ke gaba tana tauna abinci ta ce, "malama ce har hamma sai da ta zaga"
"aiko wallahi sai na mata rashin mutunci gobe-goben nan" harara Umma ta cila masa ta ce, "saboda gaku taran mahaukata kai kayi hamman naku shima dake biye maku yayi, me kuke son maida mun gida.? gidan marasa mutunci ko me" baki ɗaya ƙasa sukayi da kan su girgiza kai Umma tayi ta ce, "Allah ya kyauta...
Kamar yarda SHAHEED ya faɗa sai daya canza masu school ya sama masu wadda tafi wacan kyau, shima nan sai daya buga kashedi aiko ba'ayi wata ba malamin su ya zane ƴan ajin su BABY aiko da kuka BABY ta zo da SHAHEED ya zo ɗaukarta, aikuwa ya kama malamin ya masa duka shi da NABIL, daga nan ya cire su daga makarantar ya sake masu wata, Umma tayi faɗa sosai kan abinda sukayi sai da sukaga ɓacin ranta su duka sannan suka samu ta sako.
Babu abinda ke samun SHAHEED ban da buɗi Allah yasanyawa kasuwancin sa albarka, sosai shagonsa ke hamɓaka ahankali ya fara suna cikin kasuwa yayinda yake ƙara wani girma da kyau, BABY ma girma kawai take dan tsahon ƙafa ta fara duk duniya bata da farin cikin daya wuce SHAHEED duk da girman da take amma kullum shaƙuwa da son hammanta SHAHEED take, annurinta baki ɗaya ya tahalaƙa kan SHAHEED baki ɗaya ƙawa zucinta kansa yake, sam bata yarda yayi fushi da ita ba koda wasa duk abinda ya gwada baya so to itama taƙi abun har ma tafisa ƙin abun, haka shima ɗin SHAHEED duk abinda BABY ta gwada tana so in dai baifi ƙarfinsa ba angama, maganarta tamkar yanka wuƙa take wajensa daga maganar Umma sai na BABY, NABIL ma girma yake yayinda da suka zamarwa Umma tom and jerry shi da BABY duk da ya girme mata amma baya jin komai yake biye mata su rikita gida har sai SHAHEED ya shiga tsakanin su, ko Umma sannan, asannu mutane sun fara gane bad side ɗin su kan BABY dan zuwa SHAHEED biyu islamiyya yana rikici da malamai kan BABY haka shima NABIL da an taɓata kamar suna jira ko mayaka zasu fito a fara rashin mutunci, Umma tayi faɗa har ta gaji dan haka yanzu mutane da yawa na shakar taɓa BABY ta zama ƴar gwal.
YOU ARE READING
WATA ƘADDARA
ActionKo wani bawa nada tasa zanan ƘADDARA sai dai shi tashi tasha banban data saura, komai ya farune daga ranar da mahaifiyarsa ta kwanta ciwo, ya buga ya nema domin sama mata kuɗin magani dana asibiti duk da yana matashin saurayi mai ƙarancin shekaru ɗa...