🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
*And*
*Written*
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}
*WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg
*FREE PAGE*
*Page: 17*
*Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*
...Da gudu ta haye sama ƙofar wani ɗaki ta nufa ahankali ta murɗa ƙofar ɗakin ta tura kanta, ƙamshi da sanyi AC ya doki hancin ta, lumshe idanunta tayi dan a duniya babu abinda ke mata daɗi sama da ƙamshi turaren Hamman SHAHEED parlour ta faɗo wanda kana shigowa zaka ci karo da tamgameman hotonsu baki ɗaya sai na HANIFA da SHAHEED sun saki murmushi a tare, labulen parlour ta shiga ɗaɗagewa saboda parlour yayi duhu sosai, ɗakin ta nufa ahankali ta murɗa ƙofar ɗakin ta shiga can saman gado ta hangosa kwance yayinda kansa kawai ta iya hangowa da ya lulluɓe da bargo, labulen ɗakin ta shiga ɗaɗɗagewa fuskarta ɗauke da murmushi SHAHEED dake kwance ahankali ya motsa saboda hasken daya haske masa idanu da ƙarfinta ta ɗaga murya ta ce, "Hamma..! SHAHEED dake kwance haka yaji sautin muryarta har cikin dodan kunnasa ɗaga murya ta kumayi da ƙarfi ganin bai motsa ba ta ce, "Hamma na SHEED..! dafe da kunne SHAHEED ya miƙe a furgice jin muryar shalelensa afurgice ya sako da ƙafafunsa daga saman bed ɗin cikin sauri yana zura bedroom slippers dan sam baiyi tunanin a ɗakin take kwaɗa masa kira ba, daga shi sai sleeping robe maroon ɗaure igiyar sleeping robe yake cikin azama, yayinda gaban ƙirjinsa ke bayane wadda ya bayana packs ɗinsa dake kwance raɗa-raɗa sosai ya ƙara girma ya zama cikaken namiji mai cikar zati wanda duk macen da tayi tozali dashi sai ta san ya amsa sunasa, ba mata kaɗai ba ko maza ƴan uwasa sai sun kalesa saboda ƙira da Allah ya halita ajikin SHAHEED dan SHAHEED sam bashi da makusa dan ya haɗu ƙarshe musanman yanzu da hutu ya kuma ratsasa ya ƙara faɗi da buɗewa saboda gym.
Hanyar ƙofar ɗakin ya nufa da sauri dariya HANIFA ta saki ƙasa-ƙasa ganin alamun bacci bai sakesa ba, dan idanunsa still na lumshe wayanda eyes lashes ɗinsa sun kwanta pink lips ɗinsa ya ɗan ciza yana takawa da sauri har ya isa parloursa, da sauri HANIFA tabi bayansa ganin yana sauri shima zai buɗe ƙofar fita daga part ɗin baki ɗaya ta ƙanƙamesa ta baya, ajiyar zuciya SHAHEED ya saki cikin muryar mai masifar daɗi da shiga rai da jan fasali ya ce, "BABY..! ƴar dariya BABY tayi cikin ɗaga murya ta ce, "Hamma na SHEED ina kwana" toshe kunne SHAHEED yayi da duka hannayensa yayinda HANIFA ta danna da gudu zatayi waje ya damƙota ƴar ƙara ta saki gami da rumtse idanunta cike da tsoro yayinda SHAHEED ke binta da idanu, buɗe idanunta duka tayi ahankali ta turo baki gaba SHAHEED ya ce, "yaushe zakiyi hankali.? ƙasa da kanta HANIFA tayi ganin babu alamar wasa kan fuskar SHAHEED ya cigaba da cewa, "ban hanaki shigowa ɗakina babu knocking ba.? ahankali HANIFA ta ce, "ka hana"
"Toh me yasa baki jin magana.? ƙara ƙasa da kanta HANIFA tayi ta ce, "kayi haƙuri hamma" ɗaga hannunsa SHAHEED yayi ya sakar mata ranƙwashi ƴar ƙara ta saki "aushh.! tana sosa hula kanta idanunta raurau ta ce, "da zafi wallahi har cikin ƙwaƙwalwata"
"ai dama dan ki ji zafin nayi" SHAHEED ya faɗa yana sakinta ƙasa ƙugunta ta riƙe ta ce, "wash hamma ka kara mun ƙugu" HANIFA ta faɗa tana dafe kujera ta miƙe yayinda SHAHEED ke bala mata harara bakinta gaba ta ce, "kayi haƙuri Hamma don Allah" HANIFA ta faɗa tana kama kunnayenta kamar zatayi kuka SHAHEED ya ce, "ya isa.! ihu zata saki SHAHEED ya watsa mata idanunsa gumtse baki tayi tana dariya ƙasa-ƙasa kamar munafuka, tana son kwashewa da dariya dan sam SHAHEED baya kyau da ɗaure fuska amma me ta kasa saboda yarda ya kafeta da idanunsa, ƙwalla mata kiran da Umma tayine ya sata zaro ido ta ce, "ya Allah na makara takwas saura, hamma ina jiranka a dining tare zamu tafi school yau" HANIFA ta faɗa tana fita da gudu cikin ɗaga murya
Tana sakowa ƙasa Umma ta maka mata harara ta ce, "ya maki kyau sai ki zo ki karya ki wuce makaranta," sumu-sumu HANIFA ta ƙaraso dining ta zauna ta ɗauki slice bread tana shafa masa butter, NABIL ne ya fito sanye cikin suit black da jakar system, kujera ya ja ya zauna ahankali BABY ta ce, "Hamma NABIL ina kwana"
"lafiya lau BABY yau kin makara zuwa makaranta" ɗaga kai HANIFA tayi tana tura bread bakinta, tana kallon side ɗin Umma cikin ƙasa da murya ta ce, "yau hamma na SHEED zan bi mu tafi"
"da kyau shalele yau ba me taɓa ƴar gaban goshin Hamma" ranƙwashi Umm ta sakar mata akai ta ce, "zakiyi da jiki koko, sai na saɓa maki HANIFA, wace irin makaranta zaki tafi takwas saura, ki maida hankalin ki." BABY dake dafe da kai tana sosawa tana turo baki gaba, ƙamshi turarensa mai matuƙar sanyi da taushine ya doki ƙofufin hancin su idanunta HANIFA ta ɗago waƴanda sukayi raurau ta zube su kan SHAHEED masha Allah he look damn handsome, yana sanye cikin navy blue suit yayi azabar kyau, baki HANIFA ta hangame tana tunanin duk duniya babu mai kyau irin na Hamman ta, cikin tsanin rawar kai ta dafe ƙirji ta ce, "wayyo Allah na Hamma na SHEED yayi kyau" ta faɗa tana wani lumshe ido da sauri ta miƙe kamar a zungureta sam babu wani nutsuwa tayi kan SHAHEED wayarsa dake gaban aljihunsa ta zare iphone 11 pro max direct camera ta nufa ta ce, "don Allah hamma ka tsaya muyi hoto don Allah" HANIFA ta faɗa tana ƙanƙamesa sauke ajinyar zuciya SHAHEED yayi ya ce, "ya Allah, Allah ya shirya mun ke" ya faɗa ya jan kumatunta hoto mai kyau ta masu NABIL dake zaune shima ya ce, "nima bari na zo na raɓa ayi dani" da sauri ya shiga suka fara ɗaukar hoto Umma dake tsaye takaicin su baki ɗaya ya gama cikata pillow kan kujera ta ɗauka tana cewa, "wannan wani irin iskanci ne yarinya lokacin makaranta har ya wuce tana zaune kuna biye mata, saboda ku kun ɗaure mata kugun rashin mutunci agari babu damar mutum ya mata magana,"Umma ta faɗa tana binsu tana maka masu pillow tana masifa, saboda yarda suka baƙanta mata rai, school bag ɗinta BABY ta ɗauka tayi waje da sauri ita da NABIL SHAHEED cup ɗinsa na coffee ya ɗauka yayi waje da sauri yayinda NABIL da BABY ke kwashewa da dariya Ummana tsaye riƙe da kugu tana hakki tana masifa.
Motar SHAHEED HANIFA ta nufa fakakiyar black banz ɗinsa wanda sai kyali take tasha wanki, bayan motar ta buɗe ta shige shima SHAHEED ya shiga NABIL kuma ya shige motarsa dake fake red jeep atare suka fice daga gidan.
Ko aciki mota ban da surutu babu abinda HANIFA ke cika SHAHEED dashi kamar ya ɗaura hannu akai ya ce, wayyo Allah saboda surutun HANIFA sai dai ya dinga binta da uhm a'a yana duba news paper, birkin da driver ya cine ya tabbatar masu da sun iso makarantar su HANIFA, makaranta ce me shegen kyau ta ƴa'ƴan masu hannu da shuni a niger horn driver yayi mai gadi ya buɗe masu get suka kunno hancin motarsu ciki, HANIFA ce ta fito goye da jakarta mai gadi dake tsaye mamaki ya isheshi yana son ganin isasar data zo makaranta ƙarfe 8:30am na safe, darusa har sunyi nisa har ma anyi taran makara an gama, HANIFA na waigowa azuciyarsa ya ce, "dama sai ke ɗin dan babu me wannan ɗabi'ar ganin damar sai ke" SHAHEED dake zaune cikin mota HANIFA ta ce, "hamma don Allah kayima malama magana karta dokeni" HANIFA ta faɗa tana ƙwaɓe fuska agogon dake maƙale tsintsiyar hannunsa SHAHEED ya duba ya ce, "ki shiga ina nan biyo ki abaya ba mai dukanki okay BABY" ɗaga masa kai tayi da sauri tayi hanyar ajinsu tana raɓe-raɓe malamar dake masu darasi ce ta waigo tana kallon BABY, budurwace kyakyawa ajin farko farace sai dai farinta bai kai na BABY ba, sosai BABY ke jin shakar malamar dan babu ruwanta kuma tanada nutsuwa, gashi jinin BABY ya zo ɗaya da malamar shiyasa take ganin girmanta dan ta riƙe girmanta, zaman glass ɗinta BABY ta gyara ta ce, "ina kwana malama" kallonta malama tayi sama da ƙasa ta ƙaraso bakin ƙofa inda HANIFA ke tsaye tana jiran tak ta ruga ta ce, "me yasa yau ma kika makara.?
"malama Hamma SHEED ne ya dinga bacci kuma ni..! dakatar da ita malama tayi ta ce, "ba wannan dogan surutun na tanbaye ki ba wanene wancan" malama ta nuna SHAHEED dake tsaye bayan BABY ya riƙe waist waigawa BABY tayi dan bata san SHAHEED ya biyota a bayan ba kamar yarda yace ahankali ta ce, "Hamma nane SHAHEED"
"wato shike ɗaure maki ƙugun makara" malama ta faɗa tana aikawa SHAHEED harara daga nesa HANIFA tayi karaf ta ce "A'a malama shi hamma SHEED babu ruwansa kawai yana son far..!
"yimun shuru ba dogon surutu na tanbaye ki ba"
"Yi haƙuri malama" harara malama ta watsa mata ta ce, "wuce aji"
Da sauri HANIFA ta faɗa aji ta samu sit ta zauna ƙawarta NUSAIBA ta ce, "yau ma kin makara HANIFA har anyi darasi farko baki nan" dafe goshi HANIFA tayi ta ce, "duk ba laifina bane Hamma ne ya dinga bacci"
"ko kuma ke ce da shiririta dole sai kin jira hamman, ai kuna da driver kuma koda hamman kuka zo ai driver ke jan ku"
"toh ni nafi son tafiya da Hamma agefe na tafiyar tafi daɗi" HANIFA ta faɗa tana zaro littafi daga cikin jakarta NUSAIBA ta ce, "Allah ya shirye ke, baki ɗaya duniyar nan kamar ke kaɗai ke da yaya mu bamu da su" ƴar dariya HANIFA tayi ta ce, "na ji babu komai, aro mun littafin da akayi darasinsa bana nan"
"nina hanaki zuwa da wuri kiyi"
"Karki mun haka NUSAIBA" ganin malama ta waigo yasanya HANIFA shuru suka cigaba da ɗaukar darasi
**
Katafarin company ne wanda ya amsa sunasa company wanda daga saman company an rabuta SHAHAN JEWALRIES motar SHAHEED ce ta kunno kai cikin ƙaton campany, driver na daidaita parking ya fito idanunsa manne da baƙi glass yayinda sakariyarsa ke binsa a baya, da sauri har suka iso cikin company wanda yayi matuƙar ƙeruwa.
Sai da suka wuce wani katon fili wanda aka ƙawata da jerin kujeri masu kyau guda biyu daga gefe an zagaye wani waje inda mai isar da anyi baƙo ke zama, sai wani steps na glass daya haura yayi sama, sosai company ya ƙeru daga saman kuma wajen ma'aikata ne suma ma'aikan ɓangare-ɓangare ne, akwai ɓangaran masu designing jewalries, sai ɓangaran ƴan media masu watsa duk wata sarƙa data fito daga company da fashions sai ɓangaran marketings masu fidda kaya ƙasashe da rabawa ƴan kasuwa.
Ƙaton office ɗinsa ya shiga wadda ke zagaye da glass baki ɗaya, wanda daga waje zaka iya hango wanda ke cikin office ɗin sanyi da ƙamshi kawai ke tashi cikin office ɗin ga komai very neat well Organise, saman kujerasa ya nufa yana rage suit ɗin jikinsa ya rage daga shi sai shirt light blue yayi hanging rigar saman hanga ya zauna saman kujera gami da jawo system ɗinsa ya kunna, daga gefen table ɗin kuwa hoton BABY ne dashi wanda yayi mugun kyau aka aje taƙanƙamesa tana dariya, sakatariyarsa dake biye da shi kamar jela tun farko ta ce, "ranka ya daɗe an fitar da kaya zuwa ƙasashen da muke kusa da su, na kimanin 2millons na sarƙuna fashions kawai, yau da safe kuma dilla gwala-gwalai ta sauka daga DUBAI, yanzu haka suna ma'ajiya sai ka zo ka duba sannan komai zai tafi" miƙewa SHAHEED yayi hannunsa zube cikin aljihu ya ce, "mu je na fara ganin kayan" yana gaba sakariya na bayansa suka ƙarasa ma'ajiyar kayan wanda malam NUHU ke kula da wajen SHAHEED na isowa malam NUHU ya washe baki SHAHEED ya ce, "ina kwana malam NUHU"
"lafiya lau barkan da isowa, kaya sun sauka yau da safe"
"Madallah ina fatan babu wata matsala.? SHAHEED ya faɗa yana miƙa hannun saman hot coffee da aka kawo masa wanda yasha milo da nascef ya ɗauki mug ɗin yana sipping malam NUHU ya ce, "babu wata matsala sai son barka yanzu zaka duba kayan ka irga idan akwai matsala ma sai mu gani duka ko" jinjina kai SHAHEED yayi gami da aje mug ɗin hannunsa saman tray ya miƙa hannun aka basa tap ƙira Apple company, yasan hannunsa jikin wata ƙofa ta buɗe gwalagwalai ne suka bayana suna mugun kyali da sheƙi sannan aka buɗe wasu kwalaye dake gefe ana fido da wayanda aka kawo SHAHEED na irgawa, yayinda ma'aikatan dake wajen suke taya lisafin wasu na jerawa cikin abinda SHAHEED ya buɗe haka aka gama irga gwalagwalen tsaf aka jerasu ma'ajiya duk wanda zai fita sai securities sun duba gudun ɗan hali, iska mai sanyi SHAHEED ya fezar ya ce, "well kaya sunyi duka, masu kyau kamar dai yarda na zana haka aka kawo mun su" Malam NUHU ya ce, "Alhamdulillah kayan sunyi kyau, sai ma kaga na nigeria wanda HAKIM ya turo abun ba'a cewa komai" SHAHEED ya ce, "kunyi magana kenan.?
"eh ya kira ta nan yace ya kira wayoyinka basa shiga, yana tunanin kana bacci sai yake faɗamun kaya sun sauka can ma har ya turo da hotuna su abun gwanin sha'awa" office SHAHEED ya nufa ya ƙarasa gaban system ɗinsa yana dannawa sakatariya ta shigo ta ce, "ranka ya daɗe babu wani aiki.?
"Babu kina iya komawa bakin aikin ki" da toh ta amsa tana maida masa ƙofa wayarsa dake ruri ya kalla HAKIM ne ya bayana saman screem ɗin ɗauka yayi wanda hakan ya bayana fuskar HAKIM kasancewar vedio call ya kirasa, SHAHEED ya ce, "heyy bro ya akayi.? daga ɗaya ɓangaran HAKIM ya ce, "ya kake.?
"Lafiya lau HAKIM yanzu malam NUHU ke faɗa mun kaya sun sauka ko.?
"Yeah sun sauka yanzu na gama dubawa"
"Madallah ina fatan babu matsala.?
"Babu wata matsala SHEED kawai dai kai ɗinne ya kamata ka zo nigeria haka, ka ga yarda nake rolling company, idan akwai matsala ma sai ka duba ko" harara SHAHEED ya maka masa ya ce, "you are not serious idan ma zaka cigaba da abinda kake ka cigaba dan ban zuwa, so kake aiki ya kashe ni.?
"A'a ka dai zo ka duba daga nan sai mu fara shirye-shuryen bikina ka ga yana matsowa please SHAHEED" ya mutse fuska SHAHEED yayi ya ce, "naji naji zan zo but ba yanzu ba, kuma saboda biki kawai zan zo" yar dariya HAKIM yayi ya ce, "hakan ma na gode albishirin ka.?
"Gora.!
"kunna ka nawa.? ɓata fuska SHAHEED yayi ya ce, "matsalata da kai kenan ni kawai ka faɗa mun"
"Jiya mun haɗu da RASHID.! waro idanu SHAHEED yayi ya ce, "are you serious HAKIM.?
"Wallahi kau ka gansa yarda ya ƙara girma baki ɗaya ya canza, jiya mun daɗe muna hira yaushe gamo"
"Oh my godness me yakeyi yanzu.?
"shima yanzu business man ne kamar yarda ya faɗa mun ya zama ɗan kwangila suna haɗa abubuwan gini, kuma na san company nasa yayi suna nigeria shima ba laifi"
"Masha Allah yaushe zaka haɗa mu da shi kasan me za'ayi ka turo mun number sa" da "toh.! HAKIM ya amsa sai kuma suka cigaba da wata maganar kan kasuwancin su.
******
NIGERIA ABUJAZaune yake cikin tsararen office ɗinsa har yanzu mamaki bai gama sakinsa ba tunda ya tabbatar da wake da shararan company nan na jewelries da gwalagwalai SHAHAN, wani abu ne ya tsaya masa a maƙoshi dan sam ya kasa haɗiyewa tunda yayi tozali da HAKIM cikin alfarma, har ya so ya fisa hutu tunaninsa inda yafi tsayawa cak shine yarda zai ga SHAHEED yarda ya koma, tun da ranar da suka haɗu sosai HAKIM ya saki baki ya zayane masa SHAHEED ke da wannan dukiyar jarinsa babu yawa ciki, wato bayan sun rabu ƴan sanda basu kamasa ba kamar yarda yake tunani, tunaninsa ɗaya ne how comes SHAHEED yayi wannan dukiyar, shi da mahaifiyarsa ko lafiya bata da shi, ahankali ya ɗaga glass cup yana kurɓar wine data sha ƙanƙara ya ce, "SHAHEED..! sai kuma ya saki murmushi ya ce, "inaaaaa ba zaiyu ba wallahi, ni kai na fashi nawa nayi kafin na haɗa wannan company...! ya faɗa yana mai ƙara zooming system ɗinsa da hoton company SHAHEED ya bayana tangameme ahankali RASHID ya ce, "me yake aikatawa da har ya fini kuɗi bayan kaso ɗaya muka samu tare da shi, me yasa yanzu zai fimu dukiya.? dole na gano yarda akayi SHAHEED ya fini dukiya akan me zai fini...! RASHID ya faɗa yana wani ɗacin rai lokaci ɗaya office ɗinsa ya gundiresa miƙewa yayi ya fito daga office ɗin baki ɗaya wanda company nasa ba laifi ya ƙeru ya haɗu iya haɗuwa amma baƙin ciki da hasada yasa na SHAHEED yake hasashe...
*Follow me on facebook page n group*: *salma mas'ud nadabo*
*Follow me on IG*: *Salmerh 777*
#VOTE
#COMMENT
#SHARE~Taku har kullum salma mas'ud nadabo~
YOU ARE READING
WATA ƘADDARA
ActionKo wani bawa nada tasa zanan ƘADDARA sai dai shi tashi tasha banban data saura, komai ya farune daga ranar da mahaifiyarsa ta kwanta ciwo, ya buga ya nema domin sama mata kuɗin magani dana asibiti duk da yana matashin saurayi mai ƙarancin shekaru ɗa...