WATA ƘADDARA

75 7 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
                   *WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
      *And*
          *Written*
                  *By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}

       *WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
         

https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg

   *FREE PAGE*

*Page: 18*

_wannan page naki gunjan kiyi yarda kike so dashi,_

            *Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*

  *NIGER NIAMY*

          .......Ana tashin su HANIFA da misalin ƙarfe 2:30 suka fito ita da NUSAIBA da alama gajiya tattare dasu suna tafiya suna magana har suka isa inda ko wani ɗalibi ke tsayawa domin jiran driver ko mai ɗaukarsa, masu hawa abin hawa kuma na ficewa daga cikin makarantar zuwa waje neman abin hawa, motar SHAHEED ce ta kunno hanci cikin makarantar da murna kan fuskar HANIFA ta ce, "laa kinga hamma ne ya zo ɗauka na da kansa, Allah sarki hamma na" ɗan murmushi NUSAIBA ta saki ta ce, "toh masu hamma sai mu ƙarasa nima ga driver nan can sai na gaisheshi na ƙarasa ko" cike da zumuɗi gami da rawar kai wanda ke ɗawainiya da HANIFA yanzu ta nufi motar SHAHEED ta ɓale murfin motar ta shige NUSAIBA dake tsaye ta ce, "hamma ina wuni.?
     "lafiya lau NUSAIBA." SHAHEED ya faɗa kasancewar ya san NUSAIBA sosai dan suna ƙawancen da HANIFA sosai, kusan ma ita kaɗai ce kawar tata wadda dai suka shaku SHAHEED ya cigaba da cewa, "ya karatu ina fatan kuna maida hankali.? HANIFA ce tayi karaf ta ce, "muna mai da hankali sosai hamma musanman yanzu da zamu zana JSSCE
      "are sure.?
      "Yess.! HANIFA ta furta tana juya idanunta jan kumatunta SHAHEED yayi ya ce, "Allah ya shirya mun ke BABY wannan rawar kan naki sai ke" dariya ta saki NUSAIBA ta ce, "toh sai anjima ki gaida mun Umma" SHAHEED ya ce, "ki shigo muyi dropping naki mana"
       "Driver na har ya iso nima sai da safe" zuro kanta ta window BABY tayi ta ce, "sai da safe ki faɗawa Mama ta mana gurasa gobe" NUSAIBA da ta ɗanyi nisa ta ce, "toh Allah yasa ki ci ƴar rainin wayau" dariya BABY ta saki ta maido kanta cikin mota waigowar da zatayi idanunta suka sauka kan SHAHEED, daya tsareta da ido fuskarsa haɗe yana kallonta noƙe kanta tayi saboda ta gane dalilin bacin ran nasa saboda ta leƙa window tana ɗaga murya ahankali ta ce, "kayi haƙuri Hammana na bari" ta faɗa tana ɗaura hannayenta saman kunna ta jan karan hancin ta SHAHEED yayi ya ce, "da kyau ba'a san mace da ɗaga murya ba, impact ma babu kyau mace na ɗaga murya ko ba'a faɗa maku a islamiya ba.? SHAHEED ya jefa mata tanbayar yana mai kafeta da idanu ya cigaba da cewa, "bana son wannan rawar kan BABY ki daina" ɗaga masa kai BABY tayi sannan driver ya ja mota sai da sukayi tafiya mai nisa BABY ta ce, "Hamma.!
  "Yes.!
"please Hamma mu biya shan ice cream don Allah" ta faɗa tana kama hannunsa.
         Hankalinsa SHAHEED ya maida kan driver ya ce, "BADAMASI ka wuce da mu palais de congrès" da "toh.! driver ya amsa tare da ɗaukar hanya.
          Suna isa HANIFA ta ɓale murfin mota ta fito shima SHAHEED ya fito da sauri ta ƙarasa wajensa ta ƙanƙame masa hannu tana murmushinta mai kyau ta gyara zaman ƙaton farin glass ɗinta, wajen saida ice cream suka nufa fuskar HANIFA washe SHAHEED ya zaro kuɗi ya siya roba shida huɗu aka sanya masa cikin leda, yaba BABY roba ɗaya ya ɗauki roba ɗaya suka zauna saman kujerin da aka tanada domin shan ice cream ɗin, buɗe nata HANIFA tayi cike da tsantsar murna tasanya spoon ta fara sha tana kaɗa kai ta ce, "akwai daɗi sosai"
"uhm" SHAHEED ya ce, yana shan nasa spoon ɗinta HANIFA takai masa baki ya amsa yana murmushi wayarsa dake gaban aljihusa ta zare ta kai camera dan sam bata gajiya da hoto BABY ta fara ɗaukar su suna shan ice cream, ice cream daɗi har hancinta sai daya samu dariya SHAHEED ya saki yana kai ɗan yatsansa saman hancin ta yace, "Duk shan ice cream ɗin ne har hanci" dariya BABY ta saki tana ƙoƙarin goge hancinta.
        Handkerchief SHAHEED ya zaro daga aljihunsa yana goge mata hancinta da bakinta, ƙarshe ya tura mata handkerchief ɗin cikin baki, furzo da handkerchief ɗin HANIFA tayi gami da kwaɓe fuska yayinda SHAHEED ke mata dariya, kukan shagwaɓa ta saki SHEED na mata dariya yana mata video ta snap yana dariya, can kuma yayi shuru yana kallonta sai yau ya ƙara ganin irin girman da BABY ta ƙara idan bai manta ba, yanzu shekara HANIFA sha huɗu ayarda tunaninsa ke basa dan lokacin daya ɗauketa bata wuce yarinya ƴar shekara uku a duniya ba, idan har lusafinsa yayi daidai shekara BABY shaɗaya rabonta da iyayenta, kamar irin rana ta yau da daddare aranar BABY ta shigo rayuwarsa, wadda yake daurewa a kowace daƙiƙa yake bata farin ciki, duk da yasan cewa shi babban mai laifi ne wajan BABY baya tunanin zata iya yafe masa duk ranar daya wayi gari ta gane waye shi gurinta, shine wadda ya ɗagawa iyayenta hankali arana kamar wannan, shine wadda san zuciyarsa yasa ya barota da iyayenta, akullum da wannan abun yake kwana yana tashi sai yake gani kamar ya zama mugu mutum wanda kansa kawai ya sani, da damuwar ƴan uwansa, wanda abun na masa ciwo fiye da lokunta baya, yakanyi danasani kwado-kwado.
           A koda yaushe nadamar abinda yayi ke damunsa a kullum tunaninsa halin da iyayen BABY ke ciki, ya san cewa ko ina suke a faɗin duniya tunanin BABY nan cikin ransu, inama ace zai iya gyara kuskuran daya aikata, ina ma aceee, BABY ce ta katse masa tunani da cewa, "hamma.! firgigit ya dawo hayacinsa, sai da suka gama shiriritar su suka kama hanyar gida.

WATA ƘADDARAWhere stories live. Discover now