*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Story by SaNaz_deeyah'''*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_Visit to like our page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On Youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
_Gajeren labari da yake nuna illar mummunan furucin iyaye ga ƴaƴansu._
'''Shafi na 3'''
Tun ƙarfe 10 na safe ta gama shiryawa cikin wata atamfarta exculusive holland, red color, sannan ta ya fa gyalenta red, ta ɗauki pause. Duk da cewan light makeup tayi amma tayi kyau sosai kasancewarta kyakykyawa fatarta mai kyau da sheƙi, kuma komai ta saka yana mata kyau.
Farhan dake rubutu a jotter, ɗagowa tayi tana kallonta kawai. Safina kuwa tana kan gado a kwance tana waya da Ahmad ɗinta.
"Safina ki bani key zan fita" Jannat tayi magana tana kallon Safina.
"Yau fa bamu da lecture wai ina zakije?" Farhan ta jefo mata tambayar. "Zanje gidan su Sa'ad. Safina ki bani key please mana, sauri nake" "Excuse me, i will call later, zanyi magana da Jannat" tana faɗa ta katse. "Me zakiyi a gidan su Sa'ad?" "Safina zan miki bayani idan na dawo please sauri nake"
"Wai ba jiya kuka je ba?" Farhan ta sake magana. "Mtsww i dont have ur time, ina ruwanki" "Uhmm babu kam, ai ni kin saba gwasileni" Dariya tayi tare da girgiza kai. Safina kuwa janyo side drawer tayi ta miƙa mata key.
"Thanks you sai na dawo"
"Inzo inyi rakiya?" Farhan ta faɗa cikin tsokana. "Ba buƙata" "Nima dama ba zuwa zanyi ba dan inji me zaki ce ne" "Yanzu ai kinji" tana faɗa ta fice. Safina ta kalli Farhan tace "Ke dai Allah shiryeki da tsokana" "Gaskiya zanyi missing Jannat idan kukayi aure ko dan tsokana" ta faɗa tana cigaba da abinda take. Itama Safina girgiza kai tayi tana murmushi.******
A ƙofar gidansu Sa'ad tayi parking mota. Da sauri ta fita ta ƙarasa cikin gidan, bakinta ɗauke da sallama. Hannatu dake shara ta ɗago kai ta kalleta. "A'ah Jannat kece? Sannu da zuwa" "Yawwa Hannatu. Kawo na tayaki" Dariya tayi, tare da faɗin "Ah haba dai ki barshi ma"
"Umma na nan kuwa?" "A'a ta ɗan fita nan maƙota anyi haihuwa, amma yanzu zata dawo,Yaya yana ciki ki shiga"
"To" ta furta tare da wucewa cikin parlon.A zaune ta ganshi ya luna duniyar tunani bai ma san ta shigo ba. Zama tayi ɗan nesa dashi sannan tayi gyaran murya. Aikuwa da sauri ya ɗago ya kalleta. Ɗan murmushi yayi wanda bai kai har zuci ba. "Jannat yaushe kikazo?" "Lokacin daka lula duniyar tunani mana. Ai dama na san tabbas kana da damuwa amma kake ɓoyemin"
"Tayaya kika san ina da damuwa?" "Saboda nima na damu da kai. Yanzu dai ba wannan ba, wacece wannan yarinyar? Ni ka faɗa min zanje na sameta" Ta tambaya tana kallon cikin idanunsa._Duk sanda ta ƙara tambayar ka wacece to ka faɗa mata itace kake so, idan har tana sonka dole ta haƙura da wancan auren ta aureka, idan kuma baka faɗa ba zan ɗauki fushi da kai tunda kana nema so ya halaka ka._ ya tuna furucin Umma a daren jiya.
"Sa'ad nima ka sakani a damuwa dan Allah ka faɗa min wai wacece wannan"
"Kece....!" kawai suka ji an faɗa. Dukkansu suka juya suna kallonta. Shigowa tayi ɗakin ta ajje tsintsiyar a gefe sannan ta zauna tare da dafa cinyar Jannat.
"Hanne mene ya shigo dake ɗakin nan? Tashi ki fita" ya faɗa cikin tsawa.
Ita kuwa Hannatu cewa tayi "Wallahi bazan bari ka salwantar da rayuwarka ba dan haka sai na faɗa mata"Tasowa yayi da niyyar ya doketa, Jannat ta ɗaga masa hannu. "A'a Sa'ad tunda kai ka ƙi faɗa ka bari ta faɗa min" Jannat ta faɗa cikin sanyin murya.
"Duk abinda zai fito daga bakinta ƙarya ne, kada ki saurareta" Ya faɗa yana mai lafewa jikin bango kamar wani ƙadangare.
"Naji! Ina jinki Hannatu"
"Jannat kece Yaya yake so, kuma wallahi ya fara sonki tun ranar daya fara ganinki, sai dai kasancewarki ƴar masu kuɗi shiyasa ya kasa faɗa miki yayi ta dakon soyayyarki. Har abin ya kai shi ga kwanciya a asibiti. Umma tayi faɗa sosai domin dukkanmu muna sonki, tace lallai ya sameki ya faɗa miki. Ranar da yaje zai faɗa miki ya ganki da wani sai ya kasa faɗa, anan ma ya sha faɗan Umma, sai yace idan kinzo zai faɗa miki to zuwan da kikayi kuma sai gashi kin kawo mana I.V na bikin ki. Gaskiya Yaya yana cikin wani hali kuma komai zai iya faruwa" tana faɗa ta tashi da sauri ta fita gudun kar ya doketa.

YOU ARE READING
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Historical FictionGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...