WATA KADDARA

65 4 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
                   *WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
      *And*
          *Written*
                  *By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}

       *WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
         

https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg

   *FREE PAGE*

*Page: 19*

            *Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*

          .....Tana shiga aji malamin su na shigowa aka fara gudanar da darasi, da alkur'ani aka fara kana akayi fikihu da tauhidi kuma Alhamdulillah duk ta fahimci karatun, sam bata da wata matsala kan ƙarin malaman da suka shigo misalin ƙarfe 6:00pm aka tashe su tare da ƴan ajinsu suka fito tana zuwa bakin ƙofar makarantar ta hango motar NABIL fake da sauri ta ƙarasa ta buɗe murfin motar ta ce, "hamma ina wuni.?
  "Lafiya lau ya karatu kuma.?
"Lafiya lau hamma, me yasa hamma SHAHEED bai zo ɗauka ta ba.? harara NABIL ya doka mata ya ce, "ai dama yana zuwa ɗaukar ki makaranta duk ranar monday"
  "na tuna yau monday"
"da kyau tunda kin tuna kuma karki dameni da surutu yanzu na cilaki waje, dan ba zan ɗauki surutun ki ba, wannan sai dai hamman" baki HANIFA ta turo gaba ƙasa-ƙasa ta ce, "dama waye zaiyi hira da kai"
"me kika ce.? NABIL ya faɗa yana waigowa girgiza kai HANIFA tayi ta ce, "banyi magana ba"
"Da kyau.! ganin sun nufi wani mall HANIFA ta ce, "hamma me zamuyi anan.?
"idan kin fito kin gani" fitowa tayi NABIL na gaba tana biye da shi suka shiga mall ɗin ɓangaran kayan mata suka nufa abayas.
              Abayas ne jere reras masu azabar kyau na mata, basket ɗin zuba kaya NABIL ya ɗauka ya ce, "BABY zo ki gani" matsowa BABY tayi sosai tana kallon kayan bakin washe dan ba ƙaramin kyau suka mata ba ya ce, "zaɓo mun riguna masu kyau"
    "Toh hamma ni zaka siyamawa.? harara NABIL ya doka mata ya ce, "na taɓa zuwa dake siyayar kayane, toh ba naki bane wata zaki zaɓa mawa" baki HANIF ta turo gaba tana gunguni tana ɗaukar kayan duk da NABIL yace ba nata bane ta tsaya ta zaɓo abayas masu kyau kusan kala biyar ta ce, "wannan yayi Hamma.?
     "a'a ƙara biyar" ƙara kala biyar tayi masu kyau suma ta loda cikin basket, basket ɗin suka ja zuwa wajen biyan kuɗi HANIFA ta ce, "yanzu shikenan Hamma haka zamu fita baka siyamun komai ba.? ba tare da NABIL ya tanka ba ya gama biyan kuɗin suka fito tare niki-niki da kaya, fuskar HANIFA tam kamar zata fashr haka ta tura leda hannunta back sit ta koma mazaunin gaba NABIL ya shiga ya ja motar.
          Gab da magrib suka shigo cikin gida motar SHAHEED na fake da alama shima bai jima da dawowa daga gym ba, kayan da suka siyo NABIL ya kwashe ya shige da su cikin gida BABY na biye da shi a baya.
          Koda suka shigo parlour babu kowa sai tv dake faman aiki, ɗakinta HANIFA tayi direct tana shiga ta zare hijab ɗin jikinta gami da aje jakar hannunta, toilet ta faɗa ta ɗauro alwala ta dawo ɗaki ta shimfiɗa daduma ta tada sallah bayan ta idar ne ta samu damar sauya kaya, zuwa doguwar riga abaya mara shape ko kaɗan dan sam SHAHEED baya yarda a mata ɗinki mai bin jiki ko kaya mai nuna shape, dan aganinsa ya yarinyace ƙarama shagab to shape ɗin me zata nuna, kuma dama baya da ara'ayin ta dinga ɗinki me nuna shape, dan akwai wata rana da Mamar su NUSAIBA ta masu wani ankon biki wanda aka fito masu shape sosai riga da skirt a lokacin ma ƙirgen dangi take, amma haka SHAHEED ya dinga shiga yana fita daga ranar bata kuma sanya kayan ba, haka kuma daga lokacin bai kuma ɗinka mata riga da skirt ba, sau tari ma kayanta abayas sunfi yawa kuma irin bubu nan yake siya ma ready made ko kuma after babba sosai wanda duk nacin mutum bai iya ganin halita da ƙira da Allah ya ba HANIFA.
         Ɓangaran kayan baccinta ma haka ne manya yake siya mata wando da riga sun fi yawa wanda zata sake sosai acikin su, ko daguwar rigace sai dai siya mata wadda kamarta biyu sai su shiga dan girman rigar, tun abun na damunta yanzu kam har ya daina damunta, musanman da SHAHEED yace mata ita yarinyace har yanzu idan lokacinta yayi sai tayi duk abinda take so, shima ɗin a nasa ɓangaran saboda wannan suturun dayake yawan siya mata yasa sam baya ganin wani girmanta kullum kallon yarinya ƙarama shagab yake mata kamar ƴar cikinsa.
           Ɗakin Umma ta nufa, da sallama ta shiga, zaune saman daduma ta samu Umma tana lazumin, waje ta samu bakin gado ta zauna, har Umma takamala lazumin bakin ta gaba ta ce, "Umma kinga Hamma NBAIL ko.?
    "Me yayi shi kuma.? cewar Umma tana linke daduma HANIFA da baki yayi tsaho saboda yarda ta cinnosa gaba ta ce, "Umma mun fita dashi na rakasa siyaya amma har aka gama siyayyar bai siya mun ko tsinke ba" Umma dake zare hijab ɗin jikinta ta ce, "gaskiya Hamma NABIL bai kyauta ba, aiko ladan ganin ido ya baki"
   "Kuma Umma kala goma ya siya na abayas masu kyau ko ɗaya ya kasa bani fa"
      "Toh shi yanzu NABIL wa zai siyawa riga har kala goma ni BONONO.? ƴar shewa HANIFA tayi ta ce, "wallahi budurwa ya siyamawa kuma sai na faɗawa Hamma SHEED, ko shi bai da budurwa sai hamma NABIL" Umma ta ce, "ana maganar mutane masu himma wake sanya MAGAJI, yana zaune kema har kiyi aure baiyi ba"
   "caɓ ni kam banyin aure ina tare da Hammana SHAHEED ni shi zan aura ma" hanga me baki Umma tayi tana kallonta can ta fashe da dariya ta ce, "toh ke banda abunki HANIFA ina ke ina hamma ai ƙanwa bata auran yayenta, kuma Allah na tuba ina ke ina wannan tsohon ma arayuwar aure, ai sai ƙannan bayansa" baki HANIFA ta turo dan bata ɗauki maganar Umma serious ba ita dai kam ko aure zatayi Hamma SHAHEED zata aura, kamar yarda zuciyarta ke raya mata.
          HANIFA na fita Umma ta girgiza kai sosai take ganin yarinta na ɗawainiya da HANIFA ina ita ina SHAHEED lokacin da ƴan matanci zai bayana sosai a jikinta ai gani zatayi SHAHEED ya mata tsufa, bama SHAHEED ba ko NABIL ya mata girma sai dai ta lallaɓa da shi amma SHAHEED, abun ma dariya yaba Umma sosai ta ce, "yaro man kaza ita dai HANIFA haka Allah ya haliceta da son SHAHEED amma ta san sannu zata manta da wannan shirmen musanman taga SHAHEED yayi aure, ya zama babban mutum.

WATA ƘADDARAWhere stories live. Discover now