🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
*And*
*Written*
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}
*WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg
*FREE PAGE*
*Page: 20*
*Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*
......Tun fitowarsu break take jin kanta wani iri, haka dai tayi break adaddafe suka koma class, NUSAIBA na lure da ita, saboda ko magana sosai yau ɗin batayi ba, ƙarfe 1 daidai aka fito dasu sallah, zuwa lokacin abun yasoma fin ƙarfin tunanin HANIFA saboda wani irin ciwo da cikinta ke mata wanda ya haifawa ƙafafunta nauyi daƙyar take ɗaukar jikinta sharfa-sharfa, lokaci ɗaya wani irin zazzaɓi ya rufeta, koda ta idar da sallah cusa kanta tayi tsakankanun cinyoyinta ta saki kuka mai sauti, don bazata iya jurewa ba, sosai mararta ke murɗawa, kamar zata ɓale ta fito gawani sabon ciwon ciki me tsananin azaba da takeji, jikinta ban da rawa babu abinda yake sai zufa dake keto mata tana sauke numfashi kamar tayi tsere ganin irin yarda take kuka yasa NUSAIBA da HINDU ƴar set ɗinsu kamata suka fice daga cikin masallaci, aƙasan wata bishiya suka zauna su dukansu, cike da kulawa haɗi da damuwa HINDU ta dubi NUSAIBA wacce idanunta sukayi raurau alaman itama kuka takesonyi, "Ki kula da ita NUSAIBA barinaje na faɗawa principal" kai kawai NUSAIBA ta iya kaɗa mata alamar taji, saboda itama zuciyarta cike take da rauni haɗi da tausayin halin da HANIFA ke ciki, don zuwa yanzu numfashinta har seizing yake kamar zai ɗauke,Sauri HINDU keyi don taga ta isa office ɗin head master kamar daga sama taji anƙira sunanta, tana juyawa tayi tozali da malama AISHA, da sauri taƙaraso wajen malama kallonta malama AISHA tayi, ganinta aɗan hargitse yasanya malama cewa, "ina zaki tafi kina sauri ko kallon gabanki bakiyi.? sannan kuma ina kuka shiga ke da ƙawayenki har na shiga lesson.?
"Aunty HANIFA ce batada lafiya sosai, yanzuma office ɗin principal zanje amso mata magani." idanunta malama ta ɗan waro tare da cewa, "Tana ina.? meke damunta.? muje kinunamin inda take ko" sam malama AISHA ba ruwanta shiyasa ɗalibai da yawa ke girmamata, musanman yanzu da jininsu ya zo ɗaya da HANIFA ba komai ke burgeta da yarinyar ba sai shegen rawan kanta da surutun ta, musanman yarda ta lura da yarinyar ta fifita kyakyawan yayanta akan kowa wanda ke matuƙar burgeta, sosai taji babu ɗaɗi jin batun bata lafiya.
Lokacin da malama taga HANIFA na kuka baƙaramin tausayi ta bata ba, ba tare da ɓata lokaci ba malama ta taimaka mata ta miƙe tana raira kuka, ita da kanta ta je office ɗin principal tasanar dashi cewa zata kai HANIFA asibiti, dan ciwon nata kamar ya wuce kulawar makaranta, su NUSAIBA ne suka sata acikin motar makaranta school bus suma suka shiga, driver motar ya ja da mugun speed kamar yarda malama ta umarcesa yayi, zuwa lokacin gaba ɗaya hankalin HANIFA yasoma gushewa, ban da kuka babu abinda take rairawa.
A babban haraban asibiti driver yayi parking, zuwa lokacin sam HANIFA bata da wani ƙarfin da zata iya ko da taka ƙafarta ne, da taimakon malama suka ƙarasa cikin asibitin tana riƙe da HANIFA, Emergency aka wuce da ita, take aka shiga bata kulawa.NUSAIBA da HINDU baki ɗaya basa cikin nutsuwarsu, ganin haka yasa malama lallaɓasu tare dace musu su koma makaranta zata kula da HANIFA, babu yarda suka iya dole haka suka hau school bus suka koma makaranta, sai dai kuma gaba ɗaya hankalinsu naga HANIFA har acikin ransu basason wani abu na cutarwa ya sameta.
YOU ARE READING
WATA ƘADDARA
ActionKo wani bawa nada tasa zanan ƘADDARA sai dai shi tashi tasha banban data saura, komai ya farune daga ranar da mahaifiyarsa ta kwanta ciwo, ya buga ya nema domin sama mata kuɗin magani dana asibiti duk da yana matashin saurayi mai ƙarancin shekaru ɗa...