🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
*And*
*Written*
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}
*WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg
*FREE PAGE*
*Page: 21*
*ina kuke mosaya na, masoya littafi na akoda yaushe idan marubuci zai fara yana farawa ne da masoyansa ma'aɓota karanta littafin sa mai nane burin mai rubutawa da nazari da ƙwaƙwalwa shine ya rubuta a karanta, a nuna masa irin ƙwazan da yayi wajan fashe baƙi da nazari wajan rubutu a kowa ce alumma aikin hannu da aikin ƙwaƙwalwa ya kan zama abu mai wahala, mutane su gane irin wahala da marubuci ke sha wajan zama ya tsara labarin sa, inayiwa masoya na kira da su nuna min cewa yes suna son littafi na tahanyar siyan littafi na naira 300 kacal, domin nuna min tsantsar soyayyar ku akan WATA ƘADDARA zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi screenshot na evidence of payment ki turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki a group ɗin da nake posting zuwa completed, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*
.....Da sallama ta shigo ɗan madaidaicin parlour gidansu wanda aka ƙawatasa da kayan more rayuwa daidai misali, mahaifiyarta dake zaune ta hakimce saman kujera tana kallon movie, ɗago kanta tayi ta kalleta gami da amsa sallamarta ataƙaice.
Tsili tayi da jakar hannunta gami da sakin ɗan gutun tsaki mahaifiyarta dake zaune ta ce, "lafiyar ki kuwa AISHA.?
"lafiya lau" ta faɗa a sanyaye tana mai zama saman kujera tana cewa, "na gaji sosai"
"Amma yau baki dawo gida da wuri ba ince dai lafiya.? mahaifiyarta ta jefa mata tanbayar asanyaye ta ce, "Lafiya lau Momi wata ɗalibata ce bata da lafiya, shine na kaita asibiti, amma kin san me ya faru Momi.? girgiza kai Momi tayi ta ce, "taya zan sani ai sai kin faɗa mun."
"ina zaune da yarinyar nan kawai sai yayanta ya zo ya ɗauketa, babu godi bare na gode, abun ya mun ciwo Momi, ƙarshe ma masifa ya mun, yayi kicin-kicin da rai, har yana wani cewa me kukayiwa ƙanwata a makaranta.? AISHA ta faɗa cikim son kwaikwayar SHAHEED Aunty KULUWA dake bayanta tun ɗazu tana jinta fashewa tayi da dariya ta ce, "in dai halin ki shishigi ne haka zaki dinga cin ƙaro da mutane irin yayan ɗalibar ki" aunty ta faɗa tana kuma kwashewa da dariya turo baki AISHA tayi ta ce, "Momi kinga aunty ko"
"Ni babu ruwana kun fi kusa"
"shima dai gaskiya bai kyauta ba Allah kuma ya kyau" cewar aunty KULUWA AISHA dake zare hijab ɗin jikinta ta ce, "hmm dan yaga suna da kuɗi ne, kuma fa kyakyawa ne ya haɗu" AISHA ta faɗa tana lumshe ido harara Momi ta doka mata ta ce, "baki da kunya ko.? tashi ki ban waje mara tsinki" Momi ta faɗa tana rarumo abinda ke kusa da ita da gudu AISHA tayi ɗaki aunty ta bita tana cewa, "bari ni na zo ki shaƙa mun wallahi..!****
Zaune take tsakiyar gado tana sanye da shirt ash me wuya V gashin kanta wanda babu kitso ya zubo gadon bayanta, hannunta na riƙe da mug tana sipping maganin da Umma ta dafa mata ahankali, ɗakin yayi gumi gwanin daɗi kasancewar an kuna mata hita dan taji ɗumin jikinta da akwai sanyi garin yau, turo ƙofar ɗakin akayi ahankali NABIL ya turo kansa cikin ɗakin ɗan murmushi ta saki shima murmushin ya saki, sai yake ganin ƙanwar tasa yau tayi kyau sosai kuma ta ƙara girma ko dan ya saba ganinta kullum cikin uwar abaya ko after dress da ƙaton glass wanda yafi ƙarfin fuskarta, ƙarasowa bakin gadon yayi ya ce, "ya jiki BABY.?
"Da sauƙi."
"Me ke damun ki ne.? NABIL ya faɗa yana mai taɓa goshinta washe baki HANIFA tayi tana dariya ƙasa-ƙasa tana sipping maganinta NABIL ya ce, "faɗa mun mana hankali na baki ɗaya ina aiki yana kanki, dan dai ba zaiyu hamma ya dawo gida ba nima na dawo shiyasa fa na zauna, amma har jinina sai daya hau" NABIL ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya ahankali BABY ta ce, "hamma SHEED yace na girma" ta faɗa tana rumtse idanunta dariya NABIL ya fashe da ita ya ce, "wato yanzu kika girma ko BABY.? Jinjina kanta tayi cikin farin ciki yayinda NABIL ke cigaba da kwashewa da dariya, pillow kusa da ita HANIFA ta ɗauka tana maka masa shima ɗauka yayi yana maka mata, sauka tayi daga saman gadon shima ya biyota sukayi hanyar waje da SHAHEED sukayi kicibus, da idanunsa yake binsu yayinda BABY ke maida numfashi haka shima NABIL lokaci ɗaya yayi kicin-kicin da rai yana kallon HANIFA from head to toe dan sam baya son kutsin wasa, turo baki gaba BABY tayi ta ce, "hamma SHEED ka ga hamma NABIL ko yana mun dariya dan nace masa na girma..! BABY ta faɗa tana komawa gefen SHAHEED, shi kansa SHAHEED da fuskarsa ke haɗe sai da dariya ya kusa ƙwace masa saboda ganin zallah rashin nutsuwa na HANIFA da terare duk da yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen saita mata nutsuwa amma ina kamar yana kuma zugata, sam HANIFA bata jin kunya, kuma sai murna take ta girma, a iya saninsa mata kunyar asan suna al'ada suke amma sai gashi ita HANIFA murna take da terare.
Karan hancinta ya ja ya ce, "aiko dai BABY ta girma sai aure ba" ɓoye fuskarta tayi saman jikin SHAHEED yayinda NABIL ya ƙara fashewa da dariya yana sauka ƙasa yana cewa, "Umma ashe auta ta girma saura aure.? Umma dake zaune ta ce, "ai duk sai ta riga ku auran naga alama ba kamar kai MAGAJI na gaji da ganin ka Allah ma ya gani" HANIFA dake saurara abinda Umma ke cewa kwaɓe fuska tayi ta ce, "hamma tare zamuyi aure ko.? sam SHAHEED bai gane nufinta ba dan haka ya ce, "Eh mana tare zamuyi aure.? ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya, tsale tayi ta ƙanƙamesa janyeta daga jikinsa SHAHEED yayi ya ce, "zaki kadani BABY" bakinta ta turo gaba sai lokacin ta lura da cewa kaya iri ɗaya suka sanya da hamma SHAHEED ɗin ma shima ash shirt ce mai wuya V haka itama cike da rawar kai ta ce, "hamma ina wayarka.? aljihun wandonsa ya nuna mata baiyi aune ba ya ji saukar hannunta cikin aljihunsa ta zaro wayarsa, ta ce, "matso muyi hoto.? matsowa yayi sosai ta fara ɗaukar su zaro idanu sukayi a tare HANIFA ta ɗauke su, yayinda farin ciki ke shimfiɗe kan fuskarta jan hannunta SHAHEED yayi suka sako dining tana biye da shi, kujera ya ja mata ta zauna ya ɗauko ledar pizza daya siyo mata ya buɗe gabanta ya ɗauko yanka ɗaya yasanya mata a baki kutsira tayi tana lumshe idanunta ta ce, "uhmm ina son ka Hamma"
"nima ina sonki HANIFA hamma SHEED" cike da farin ciki ta ɗauko yanka ɗaya ta sanya masa a baki ya amsa shima yana ci NABIL ma hannun yasa ya ɗauka yana ci har BABY na kaɓe hannunsa ya ce, "ai wallahi sai na ci" kwaɓe fuska HANIFA tayi tana ɗibar pizza cikin wawa hannun biyu duka, baki NABIL yasanya tana can tana surutu yana cin ta ɗaya hannunta sai da yayi rabi ta ankara, ihu ta saki tana cewa, "ka ganshi hamma SHEED." ta faɗa tana didire ƙafa ranƙwashin NABIL yayi ƴar ƙara ya saki "aushh" yana sosa kansa BABY na masa dariya da gwalo, gashin kanta SHAHEED ya watsa dake hargitse ya ce, "mara son kitso ga son yawa babu ɗankwalli i hate this behaviours" SHAHEED ya faɗa yana haɗe fuska, kunnata HANIFA ta kama da hannayenta ta marairaice, janye hannayenta SHEED yayi murmushi ta saki tana kuma ƙara masa pizza sannan ta miƙawa Umma itama ta amsa.
Washe gari Alhamdulillah jikin HANIFA yayi sauƙi yau ma kamar jiya tun 7:00am na safe ta tashi ta shirya cikin uniform ɗinta, goye da school bag ɗinta ta saƙo ƙasa, zaune a dining ta samu SHAHEED cikin ƙanana kayansa irin na sanyi dan garin yau an tashi da sanyi babu laifi, yayi bala'in kyau cikin navy blue kayan sanyin gashin kansa wanda ya aske sama-sama ya kwanta irin na fulanin usul yana sipping coffee pink laɓɓansa sai shining suke, rungumesa BABY tayi ta baya yayinda hannayenta ke saƙale a wuyansa ta ce, "hamma na SHEED ina kwana"
"lafiya lau HANIFA hamma SHAHEED, Kin tashi lafiya.?
"Lafiya lau hamma na" hannunta SHAHEED ya zare dake wuyansa ya ce, "zo zauna time na tafiya" kujera ta ja ta zauna slice ɗaya na bread SHAHEED ya ɗauka yana shafa mata butter ya miƙa mata ya ce, "humm.! amsa tayi tana ci ahankali, haɗa mata tea yayi ya miƙa mata amsa tayi tana sha, Umma ce ta fito daga kitchen ita da INNO da sauran kayan break gaishe da Umma sukayi ta amsa tana cewa, "madallah daga ke har hamman naki kunyi abun kai kun tashi da wuri" ɗan murmushi HANIFA tayi tana tsoma hannunta cikin zumar dake cikin ɗan bowl wadda Umma ta aje dan da zuma take shan tea, SHAHEED ne ya kaɓe hannunta sanin doctor ya hanata shan zaƙi turo baki tayi gaba SHAHEED ya ce, "kin sha drugs ɗin ki.? girgiza kai HANIFA tayi ba tare daya jira cewarta ba ya haura sama ya kwaso magungunata ya dawo dining da bottle na ruwa hannunsa, ɓallo magunguna yayi ya miƙa mata ta amsa bakinta gaba ta tura magunguna bakinta kana SHAHEED ya miƙa mata ruwa ta amsa ta shanye ya ce, "good girl, sai tafiya school"
"yau ba tare zamu tafi ba Hamma.?
"Eh ni ba yanzu zan fita ba ki je driver ya kai ki okay" ɓata fuska HANIFA tayi hakan yayi daidai da fitowar NABIL cikin sauri yana gyara zaman suit ɗinsa bread ya ɗauka yana tuturawa baki da alama ya makara zuwa aiki SHAHEED ya ce, "yauwa NABIL tunda ka fito da wuri kayi dropping BABY school" ɓata fuska NABIL yayi ya ce, "hamma..!
"bana son dogon magana, ta shirya kawai dropping nata zakayi" kallon HANIFA NABIL yayi yana hararar ta ƙasa-ƙasa tana masa gwalo a ɗan hasale ya ce, "sai mu je nayi dropping naki" miƙewa tayi Umma ta miƙa mata lunch box ɗinta tana gaba NABIL na baya har sunyi gaba zasu shiga mota SHAHEED daya biyo su abaya riƙe da suwaita ya ce, "HANIFA.! dawowa tayi ya sanya mata suwaita da safar hannu ahankali ya ce, "yau akwai sanyi" haƙoranta ta washe har dimple ɗinta na lomawa har tayi gaba kuma sai ta dawo da saurinta ta sumbaci goshin SHAHEED tana murmushi ta ƙara da gudu ta faɗa mota, SHAHEED na tsaye hannunsa zube cikin aljihu yana kallonsu, NABIL ya ja motar suka ɗau hanyar makaranta.
Suna zuwa bakin get ya faka turo baki HANIFA tayi ta ce, "idan hamma ya kawo ni baya aje ni bakin get, cikin makaranta yake aje ni" harara NABIL ya doka mata ya ce, "sai kuma ni ba hamma SHAHEED bane, NABIL nake zaki sauka ko saina karya ki, bakin san ina da aiki bane sauka" gunguni HANIFA ta fara tana ɗaukar jakarta NABIL ya ce, "me kika ce.?
"ban ce komai ba"
"Kima ce wani abun ma ki gani idan ban ɓaɓalaki ba, mara kunya" raurau da idanunta BABY tayi ta ce, "sai na faɗawa hamma na"
"kin daɗe..! NABIL ya faɗa yana mai jan ƙofar motarsa wadda BABY ke tsaye ya fusgi motar ya hau kan titi bakin ta gaba ta shige cikin school ɗin.
NUSAIBA na ganinta ta danno da gudu ta ce, "masha Allah jiki yayi kyau da yau ina cewa zamu je gaishe ki ni da HINDU" far da idanunta HANIFA tayi ta ce, "aiko na warke sumul"
"da kuka je asibiti me akayi.?
"Nima ban sani ba kawai na tashi na ganni gida, kusan wani abu.?
"a'a HANIFA sai kin faɗa" far da idanunta HANIFA tayi ta ce, "kuma Hamma na ya ce na girma" wata irin shewa su NUSAIBA suka saki yayinda BABY ma ke dariya shigowar uncle ya katse masu zance.
Darasin maths suka fara kana sukayi basic, da sauran topic kasancewar yau basu da aunty AISHA bata shigo ba, HANIFA kuwa ta so ganinta ta mata godiya har aka tashi break aka koma bata ganta ba, koda suka dawo class darasi ne ya cigaba da gudana, ba laifi su HANIFA na ɗaya daga cikin ɗalibai masu maida hankali dan haka kowani malami ya san su HANIFA, wasu da yawa kuwa da HANIFA hamma SHEED suke kiranta, dan sun san rashin m ɗin SHAHEED kan HANIFA zuwa makarantarsa kan HANIFA baya irguwa, shima dan Umma ta taka masa birgi ne da zuwa wannan lokacin ya gama zagayawa da HANIFA duka makarantun niamy.
Misalin ƙarfe 2:30pm da rabi aka tashe su suka fito tare da su NUSAIBA suna tafiya suna hira su dan suna da shegen surutu su duka, shiyasa idan suka haɗe agida SHAHEED ne kaɗai ke shanye hayaniyar su kuma ba dan basu damunsa ba kawai haƙuri yake saboda yana son farin cikin HANIFA.
Daleliyar motar SHAHEED ce ta kunno hancinta cikin makarantar su HANIFA, motar sai kyali take red jeep, HANIFA na ganin motar annurin fuskarta ya ƙaru ta ce, "hamma ya zo sai da safen ku"
"ki gaida gida muma ga driver mu can ya iso" da sauri HANIFA ta ƙarasa wajen motar tun kafun ta buɗe SHAHEED ya buɗe mata da sauri ta shige motar tana cewa, "kamun bazata kamun bazata hamma na SHEED.! ta faɗa gamin da faɗawa jikinsa ɗan murmushi SHAHEED yayi gami da ɗan tureta daga jikinsa ya ce, "yaushe BABY zata girma ne, baki san kina da nauyi bane, kin fa girma amma baki komai irin na ƴan mata" turo baki tayi tana matsawa daga jikinsa dariya SHAHEED yake yana cewa "har yanzu da sauran BABY zama ƴan mata gaskiya, Allah ya shirya mun ke" da "amin" BABY ta amsa tana mai kallon windown ta hango Aunty AISHA da alama abun hawa take nema, fuskar HANIFA da murmushi ta ce, "Hamma mu tsaya ga malamar mu can da alama abun hawa take nema tana da kirki hamma, ita ce ta taimake ni ta kaini asibiti Hamma" numfasawa SHAHEED yayi ya ce, "me kike so nayi mata to BABY.?
"ina so mu rage mata hanya ne hamma" HANIFA ta faɗa da murmushi kan fuskarta ta ce, "malam BADAMASI ka tsayar da mota.! tsayawa driver yayi ɗan nesa da Aunty AISHA ɓale murfin mota HANIFA tayi ta fita da sauri ta ƙarasa wajen malama ta ce, "aunty.! murmushi aunty AISHA ta saki ta ce, "HANIFA ya jiki.?
"Da sauƙi malama na warke ma kin gani"
"Masha Allah haka ake so ai, ina zaki yanzu"
"Gida zamu tafi ki zo mu sauke ki ni da hamma na" taɓe baki AISHA tayi ta ce, "na gode hamman ki bashi da kirki ko kaɗan" ɓata fuska HANIFA tayi ta ce, "ki daina faɗin haka aunty hamma na yana da kirki sosai kuma bari ki gani" jawo hannun malama AISHA tayi duk da tana tokewa BABY ta buɗe murfin mota ta shige tana riƙe da hannun malama da kanta ke ƙasa fuskarta tamke itama ta shiga ahankali ta ce, "ina wuni.! SHAHEED dake danna wayarsa ya ce, "lafiya" ataƙaice ɗan zungurinsa HANIFA tayi ta ce, "hamma wannan ce malama AISHA kuma tana da ƙirƙi sosai, ita ce ta kai ni asibiti ai na faɗa ma ko" jinjina kai SHAHEED yayi ya ce, "uhm.! shuru ne ya ratsa motar can HANIFA ta ce, "hamma malama tace mun jiya ka mata rashin kirki wai haka ne.? ɗago idanunsa SHAHEED yayi yayinda AISHA ma ta ɗago nata idanun dan batayi tunanin abinda HANIFA zata faɗa ba kenan, idanunsu ne suka sarƙe dana juna yayinda gaban malama ke mugun faɗuwa, ahankali ta janye idanunta daga cikin na SHAHEED dan bazata juri ganin ƙwayar idanunsa ba cikin muryarsa mai cike da ƙasaita da daɗin saurare SHAHEED ya ce, "am sorry for the misunderstanding Auntyn HANIFA" malama dake raɓe ba gane eglish take ba tafi gane french, shi kuma SHEED yana yawan manta niger french suke, ɗan murmushi tayi kawai tana mai ƙara kame jakarta, bayan sun yi tafiya mai ɗan nisa, driver ya tanbayeta gidan su ta masa kwatance, har ƙofar gida suka sauke malama da murmushi kan fuskarta ta ce, "na gode sosai.! har tayi gaba ta window HANIFA ta leƙa kanta ta ce, "insha Allah malama zan kawo maki ziyara ni da hamma na ko hamma" jinjina kai SHAHEED yayi malama kuma da murmushi kan fuskarta ta ce, "toh HANIFA sai kun zo" ta faɗa gami da shiga gida waigowa HANIFA tayi tana kallon SHAHEED ta ce, "ya kaga malamar mu hamma.? taɓe baki SHAHEED yayi ya ce, "gata nan dai.! ba tare da HANIFA ta ƙara magana ba har suka iso gida..*Follow me on facebook page n group*: *salma mas'ud nadabo*
*Follow me on IG*: *Salmerh 777*
#VOTE
#COMMENT
#SHARE~Taku har kullum salma mas'ud nadabo~
YOU ARE READING
WATA ƘADDARA
AçãoKo wani bawa nada tasa zanan ƘADDARA sai dai shi tashi tasha banban data saura, komai ya farune daga ranar da mahaifiyarsa ta kwanta ciwo, ya buga ya nema domin sama mata kuɗin magani dana asibiti duk da yana matashin saurayi mai ƙarancin shekaru ɗa...