WATA KADDARA

64 2 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
                   *WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
      *And*
          *Written*
                  *By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}

       *WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
         

https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg

   *FREE PAGE*

*Page: 22*

            *Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*

           .....Yarda AISHA tayi tunanin SHAHEED sai yanzu da suka shiga mota ɗaya ta gane sam ba haka yake ba, baki ɗaya bad side ɗinsa kan HANIFA yake kuma ta lura da zarar ka nunawa HANIFA so da kulawa zaka siye zuciyarsa tsaf, kamar yarda ta karancesa ɗan zaman da sukayi kawai acikin mota ɗaya yanzu da suka sauketa.

                              ***
              Shiryawa take cikin wasu yellow sport wears masu ratsin white jikin wandon kayan daga gefe, sai ƴar cikin rigar yellow sai ta saman mai kama data sanyi ledace haka shima wandon yana da roba daga ƙasa wanda ya matse ƙafafunta, white hijab ta ɗauka ɗan ƙaramin bayan ta dunƙule gashin kanta yayi kamar ganmo ta sanya hijab gami da ɗaura yellow facingcap ta manna ma idanunta white glass sosai tayi mugun kyau  shigar da tayi shi zai tabbatarwa mai karatu cewa yellow house take a school kuma dama duk ranar thursday suke sport, abunka da fara fata sosai kayan suka mata mugun kyau tayi ƴar duma-duma da ita, goye da black school bag ta fito, ƙafafunta na sanye ciki white cambas sai agogon hannunta black wanda ya ƙara fito da zallah farinta har wani yellow take itama kanta, ciki ɗan ɗaga murya take cewa, "Hamma na SHAHEED..! SHAHEED dake tsaye gaban dressing mirror yana shiryawa cikin yellow kayan sport kamar na HANIFA yayi bala'in kyau facing cap yellow ya ɗauka yana sanyawa akansa ya ce, "ina zuwa BABY shiryawa nake" ya faɗa yana feshe jikinsa da turare, yau wasa su HANIFA zasuyi wanda kowa mahaifinsa ke zuwa ko yayanka ga waƴanda iyayensu basu raye, turo ƙofar ɗakinsa BABY tayi ahankali ya ɗago idanunsa yana kallon BABY dake kallonsa dan ba ƙaramin kyau ya mata ba har sai da ta sauke ajiyar zuciya, da sauri ta ƙaraso wajensa ta saƙala hannunta saman wuyansa suna kallon mirror ta ce, "Hamma na kayi kyau sosai" ta faɗa tana sakin murmushi SHAHEED dake sakin murmushi karan hancinta ya ja ya ce, "ke ma kinyi kyau HANIFA hamma SHAHEED" ɗage gira tayi gami da ɗaukar wayarsa dake saman dressing mirror tana ɗaukarsu ta cikin mirror, waigowa tayi sosai yayinda SHAHEED shima ya waigo suna fuskantar juna, har tsakiyar idanunsa BABY ke kallonsa sam ta kasa janye idanunta akansa takanji wani yanayi na musanman akan hammanta SHAHEED, wanda sam bata jinsa akan hammanta NABIL komai takan ji akansa na musanman sau tari takan rasa meke damunta akan hamman SHAHEED, amma tayi imani duk duniya bayan Umma babu kowa cikin ranta sama da SHEED ɗage mata gira SHAHEED yayi ƙasa tayi da idanunta hakan yayi daidai da ƙwalla masu kira da Umma keyi da sauri BABY ta fita daga ɗakin ta bar SHAHEED na ƙarasa sheri Umma dake tsaye ta shirya ciki tsadadiyar atamfarta lemon green da ratsin white brown ta yafa mayafi ko ina jikinta gwalagwalai tayi kyau sosai ta ce, "me kuma kuka tsayayi lokaci na ƙurewa fa" Umma ta faɗa kasancewa baki ɗaya gidan zasu tafi SHAHEED ne ya sako ƙasa NABIL shima ya fito cikin shirinsa na ƙananan kaya suka fice daga gidan, black jeep suka shiga su duka NABIL da SHAHEED na gaba Umma da BABY na baya SHAHEED ya ja motar mai gadi ya wangale masu get.

WATA ƘADDARAWhere stories live. Discover now