WATA KADDARA

105 2 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
                   *WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
      *And*
          *Written*
                  *By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}

       *WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
         

https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg

   *FREE PAGE*

*Page: 24*

            *Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*

             ..........A hankali ta ƙarasa Dining area yayinda SHEED ke zaune yana danna wayarsa kujera ta ja ta zauna ta ce, "gani hamma" kallon ƙasan idanunsa ya mata gami da miƙa mata plate ya ce, "oya cinyesa yanzu" kallon abincin da hamman ya zuba mata take cikin raunin murya ta ce, "ya mun yawa Hamma.! ɗago idanunsa SHEED yayi yana kallonta yarda tayi kala tausayi spoon ya ɗauka yasanya cikin abinci ya ɗebo fuskarsa babu alamun wasa ya ce, "haaa.! buɗe baki BABY tayi babu musu tana karɓar abincin kamar me shan magani sai da tayi kusan rabin abincin kana ta ɗauki spoon ta ɗebo ta nufi bakin SHEED ta ce, "uhmm.! buɗe baki yayi shima yana amsa abincin ba wai dan yana jin yunwa ba sai dan ita ɗin ta samu ta ci abincin da yawa, a da ya rasa meke damun BABY naƙin abinci yasha kaita asibiti likitoci su dubata su tabbatar masa da lafiyarta lau sai dai sukan masa gargaɗi da ya dinga tursasata cin abincin saboda rashin abinci zai iya haifa mata matsala babba, sai dai zuwansa asibiti na karshe da HANIFA ya shiga tashin hankali ba ɗan kaɗan ba saboda sakamakon daya fito da aka mata ƴan gwaje-gwaje shiyasa koda wasa baya bari ta zauna da yunwa yana iya bakin ƙoƙarinsa yana kula da ita kamar ɗiyar cikinsa, shiyasa kullum yake kafa-kafa da ita kamar ƙwai domin ganin cewa tana cikin ƙoshin lafiya, yayinda mugun tausayinta ke jigila da shi sanin halin da HANIFA ke ciki wanda babu wanda yasan haka sai shi daya kaita asibitin sai kuma Umma ita kanta ranar ta shiga ruɗani, jin abinda likita ya faɗa wannan dalilin yasa kullum SHAHEED ke lura da ita yana kafa-kafa da ita, sai da suka share plate ɗin SHAHEED ya tsiyayo fresh orange juice a glass cup ya miƙawa BABY rabin cup ɗin kawai ta iya sha ta miƙa masa cup ɗin ya ce, "wakika barmawa lemon.? kanne idonta ɗaya tayi tana nunasa da yatsa ta ce, "kawo ka gani" amshe glass cup ɗin tayi ta ce, "haaa" harare SHEED ya doka mata ya ce, "kin rainani ko BABY" girgiza kai tayi ya ce, "good shanye" kafawa tayi a bakinta tana dariya ƙasa-ƙasa ta shanye ta aje cup ɗin ta ce, "shikenan ba" ta faɗa tana tattare plate ɗin da suka ɓata da cup ɗin.

        Cikin ƴan kwanakin nan sosai Aunty AISHA ke shigewa HANIFA fiye da da zuwanta gidan su HANIFA biyu bayan zuwa HANIFA sau ɗaya, Umma kuwa sosai take yabawa da nutsuwar AISHA dan yarda take ƙanƙan da kai gaban Umma dan wani abun har da ƙarima haɗawa take, idan ko ta zo gidan ta samu Umma na aiki zatayi uwa tayi makarɓiya ta amshe tanayi duk da akwai masu aiki, SHAHEED kam sam bai damu da ita ba harkokinsa kawai yake sai BABY ta jonasu wajen rawar kanta sannan yake ɗan tsayawa, tun dai baya wani damuwa da sha'anin AISHA har ya ɗan fara saurarata kaɗan tana yawan kira BABY a waya daga bayama sai ta tsira kiran SHEED lokutan data san BABY bata kusa da shi, idan ya ɗauki wayar duk saita diririce tana ƴan kame-kame haka dai zasu gaisa sama-sama SHAHEED ya kashe wayarsa.

          Zaune yake cikin office ɗinsa yana sanye da sky blue suit wadda tayi matuƙar amsar jikinsa he looks masha Allah, yana fama aikin danna system ɗinsa yana duba wasu new fashions jewelries da suka shigo har an fara yayinsu nigeria kafin su shigo niger, jewelries ɗin sun masa kyau matuƙa kuma yana da yaƙinin zasu shiga a niger idan ya kawo su duk da ba disinging ɗinsa bane, wayarsa kira iphone 11pro max dake saman table ce ta ɗauki ruri suna AMMIE ne bayana saman screen ɗin ɗan murmushi ya saki gami da ɗaukar wayar ahannunsa har saida ta katse kana yabi kiran da murmushi kan fuskarsa daga ɗaya ɓangaran AMMIE ta ɗauka da sallama tana cewa, "MAGAJI kana jina"
"ina jikin tsohuwa mai ran ƙarfe" daga ɗaya ɓangaran AMMIE ta yage baki ta ce, "MAGJIYA ya niger da BONONO.?
"Duka suna lafiya lau AMMIE"
"madallah haka nake son ji ai" can kuma AMMIE tayi ƙasa da murya tana cewa, "tsakanin ƙarya da gaskiya MAGAJI kaƙi ƙasar ka ta gado, tunda kasa ƙafa kai da su BONONO kuka bar ƙasa ko waiwaye, haka rayuwa zata dinga tafiya sai dai duk watan duniya kamun aike, amma babu labarin zuwanku mahaifar ku, me kake nufi ne MAGAJI..? AMMIE ta faɗa tana son yin kuka SHAHEED dake saurarata ya ce, "ya isa haka tsohuwa ina nan zuwa na ɗauke ki mu dawo nan niger gani ga ki"
  "wa ni babu inda zani nafi ganema ƙauyena wallahi, idan ka ganni niger toh bikin ka ya kawo ni" ɗan murmushi SHAHEED yayi ya ce, "aiko zaki jima baki zo ba ko"
  "Me kake nufi MAGAJI.? haka zaka zauna sinƙin fakitin makaɗin zindir babu aure, lafiyar ka ɗaya kuwa shekaraka nawa duniya kana gantalli babu aure, ita kuma BONONO ta zuba ma ido tunda kafi ƙarfinta, tun wuri ka canza shawara dan mindin ka zo babu maganar auranka ƙasa, duk wacce Allah ya bani sa'a na maka hannuna kanta aƙauye to babu musu ita zaka aura, ka ji narantse ma MAGAJI idan kuma ka ji wasa kayi gigin zuwa babu wata maganar aure ƙasa kaga ikon jala" SHAHEED dake saurara AMMIE  dake ratafo zance abun ma dariya yake basa goɗai-goɗai dashi kawai sai ya tsaya AMMIE ta masa auran dole, kamar a film ko a littafi haka AMMIE ta gama faɗan ta ƙarshe ya ce, "kiyi haƙuri AMMIE ki ɗan ƙara mun lokaci, in dai aure ne zanyisa tunda shine matsala" daga ɗaya ɓangaran AMMIE ta ce, "da kyau ka gaida mun da ƴar gidanka da HANIFA" da "toh..! SHAHEED ya amsa gami da kashe wayar yana kashe wayar kiran sabon layi ne ya shigo da kamar ba zai ɗauka ba ganin number nigeria kuma sai ya ɗauka tare da sallama, daga ɗaya ɓangaran aka amsa muryar namiji ce ta doki kunnasa ya ce, "SHAHEED ka gane mai magana.? SHAHEED dake zaune ya ce, "gaskiya ban gane ba kam"
"dama na san abune mai wuya ka ganeni tunda kana niger kana jin daɗin ka cikin daula sai dai muga news paper ka na yawo" SHAHEED dake zaune da mamaki ya ce, "toh fa, am serious bangane mai magana" RASHID dake ta ɗaya ɓangaran ya ce, "anyway am RASHID.!!! SHAHEED dake zaune with smile ya ce, "oh my goodness long time RASHID, ina ka shigane kusan 11years rabon dana sanyaka ido na".
      "Haka nima, ina nan nigeria gefe gudu kun barni kai da HAKIM kunata zumincin ku abunku ni kuma ina gefe" ɗan murmushi SHAHEED yayi ya ce, "yanzu dai na gane fushi ake dani, ayi mun haƙuri baki ɗayan ku na damu daku, kuma soon zan zo nigeria kaga sai muga juna ko"
     "toh Allah ya nuna mana am just waiting to see you as soon as" 
   "insha Allah zamu ga juna da bikin HAKIM" cewar SHAHEED da tsantsar farin ciki kan fuskarsa sun jima suna waya da RASHID na hira yaushe gamo, sannan SHAHEED ya datse kiran daga ɓangaran RASHID kuwa da tsaki yabi wayar dan ya ƙosa yaga SHAHEED ɗin news paper dake kusa da shi wadda ke ɗauke da ƙaton hoton SHAHEED ya duƙunƙune ya cila bola ya ce, "mu za'a dinga yima ƙaryar banza da bamu san asalin angulu bane da FASHI yayi arziƙinsa" RASHID ya faɗa cikin ɗacin rai yana takaicin yarda SHAHEED ya fisa kuɗi, har yana tunanin wace harkar ya faɗa har ya tara maƙudan kuɗin daya ke jin labari kamar wasa.
   
   
          Misalin karfe 5:00pm na yamma kwance yake akan makeken bed ɗinsa wanda yaji bedsheet na alfarma, dagashi sai long pencil jeans, gaba ɗaya hankalinsa nakan laptop ɗinsa, wayarsa dake saman bed ce tasoma ƙara alaman shigowan kira, saida wayar takusa katsewa sannan SHEED ya kai hannunsa kan wayar sunan Umma ya gani na nayawo akan screen ɗin wayar yasanyashi ɗaga wayar da gaggawa, yana kara wayar akan kunnensa, Umma dake zaune cikin ɗakinta da waya hannunta ta ce, "MAGAJI kazo kasameni yanzu a ɗakina" ƙit takashe wayar batare data ji me SHAHEED ɗin zaice ba.
             Ahankali SHAHEED yasauke wayar daga kunnensa tare da sauke ajiyar zuciya, yana mamaki kiran da Umma ke masa, rufe laptop ɗin gabansa yayi tare da zuro ƙafafunsa ƙasa, wata bruberry button shirt fara ya ɗauka ya sanya ajikinsa, bedroom slippers yasanya aƙafafunsa kana yafice daga cikin ɗakin, tun da ya doshi ɗakin Umma yaji zuciyarsa na bugawa, sam baison sakejin wani abu dazai ɗaga hankalinsa, musanman kan tafiyarsu Nigeria.
           Zaune  bakin gado yasamu Umma tana jera kayan BABY da mai wanki ya kawo kasancewar tana islamiyya kuma dama sabin kayanta ɗakin Umman take aje su zama yayi saman sofa ya ce, "Umma gani" gyara zama Umma tayi tana kallon SHAHEED ta ce, "MAGAJI yaushe zakayi aure.? Shin har yanzu duk faɗin garin nan baka samo wacce kakeso ba.? Kai fa ba yaro bane a kullum  kara girma kake, ko NABIL a yanzu ya isa aure bale kuma kai, sai yaushe zakayi aure to.? Umma ta tambayesa babu alaman wasa akan fuskarta.
       Ɗan shiru SHAHEED yayi kansa ƙasa dan ya kasa magana Umma ta ce, "ba da kai nake magana ba" jim SHAHEED yayi dan shi yanzu sam babu wani aure a gabansa saboda har yanzu zuciyarsa bata gane masa wadda ya samu nutsuwa da ita ba ya ce, "Umma kiyi haƙuri har yanzu ban samo wadda hankali ya kwanta da ita bane, amma da zarar na samu zanyi auran." ya faɗi hakan cikin raunanniyar murya Umma dake saurarasa ta ce, "Shikenan babu ma buƙatar kasamo da kanka, ni da kai na ma sai na zaba ma wadda hankalina yafi kwanciya da ita, dan ba zan zauna gida da mutum kamar ka babu aure ba, sannan kuma maganar tafiya Nigeria dole idan muka je kaduna mu je katsina wannan karan baka isa ka ce bazaka je ba MAGAJI tashi ka ban waje" miƙewa SHAHEED yayi ya fice batare daya iya furta koda kalma ɗaya ba.
                  
      
            Koda SHAHEED ya koma ɗaki saƙa wannan yake yana kwancewa baki ɗaya ma duniyar yarasa wa zai kawo a matsayin mata yake, can cikin zuciyarsa kuma wani tunani ya ɗarsu wanda yake gani shi ne mafita duk da cewa bai wani ba abun mahimmaci ba amma yafi masa auran dole sau dubu, wayarsa dake rining ne ta katse masa tunani suna Aunty AISHA ne ya bayana da kamar ba zai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka, daga ɗaya ɓangara Aunty AISHA ta rangaɗa sallama tare da gaida SHAHEED amsawa yayi ataƙaice ya ce, "gashi BABY bata nan tana islamiyya"
"Au haka na manta yau saturday, ya kake to.?
"Lafiya lau ya kuma weekend.?
"Weekend Alhamdulillah gashi nan munata sha kafin monday mu koma hidimar ɗalibai"
   "Allah ya taimaka toh" jim SHAHEED yayi dan bai san me zai ce mata ba haka ita ma dama duk kauɗin data kirasa suka gaisa sai ta rasa abin cewa, toh shima SHAHEED rasa me zai ce mata yake sau tari duk da ya gane take-taken ta tuntuni, shawara da zuciyarsa ke basa ya yanke dan hakan yafi masa sau dubu da abinda AMMIE ke faɗa da Umma saita kansa SHAHEED yayi cikin muryasa mai daɗin sauraro  ahankali ya ce, "gobe kina free malama AISHA.? Aunty AISHA dake zaune ai ji tayi kamar SHAHEED ya kwaranya mata ruwan sanyi saboda tsabagen farin ciki yau ita SHAHEED ke tanbaya tana free dan zuciyarta tuni ta saƙa mata wannan tanbayar daga zuciyarsa ta fito zuwa laɓɓansa cikin kashe murya ta ce, "ina free"
"okay ki shirya gobe ina son zamuyi wata magana dake idan babu damuwa" cikin siririyar muryarta ta ce, "toh" kana SHAHEED ya kashe wayar, gami da bin ta kallo abu ɗaya zuwa biyu ke burgesa da yarinyar tana da nutsuwa kuma shi a tsarinsa mutum ne mai matuƙar son mace mai nutsuwa da sanin ya kamata, na biyu kuwa shaƙuwarta da Umma da BABY shi yafi komai sanya masa nutsuwa da ita ba wai dan yana jin wani abu game da ita ba, sai dan kawai ya samawa Umma farin ciki zai kawota amatsayin wacce yake son aure.
                  Da daddare zaune take tsakiyar gadonta tana sanye da kayan bacci pink waƴanda sukayi matukar amsarta, kanta na ɗaure da hula wadda ta rufe yalwatacan gashin kanta, idanunta na manne da glass ta baza litattafai gabanta na makaranta islamiyya, da alama assignment take ko daga yanayin yarda ta maida hankalinta kan littafan zai nunawa mutum nazarin assignment take, knocking ƙofar ɗakinta da akayi ne yasanyata ɗago brown idanunta waƴanda ke manne da ƙaton glass ɗinta wanda ke rage kusan rabin kyan HANIFA saboda yarda ya mamaye fuskarta dan yana da girma kuma zagayayene ta ce, "A shigo.! SHAHEED ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo fuskarsa sake kamar kullum bakin gadon BABY ya samu waje ya zauna BABY dake kan gadon idanunta ƙur kan nasa wayanda suka ƙara girma ta cikin glass, sosai SHAHEED ɗin ya mata mugun kyau yana sanye cikin wasu black kaya masu taushi riga da wando irin wayanda suke zuwa tare, ƙafafunsa na sanye cikin bedroom slippers rarafawa tayi daga saman gadon ta ƙanƙame masa wuya yayinda take shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa mai daɗi da sanya nutsuwa idanunta lumshe ta ce, "hamma na SHEED barka da dare ka kyauta daka zo adaidai wannan lokacin, dama na kasa Assignment nawa ka ga yanzu sai ka mun ko Hamma.! HANIFA ta faɗa cike da rawar kai, zare hannunta SHAHEED yayi dake saman ƙaffaɗarsa ya ce, "zo zauna muyi magana first" ya faɗa yana jawo hannunta zuwa bakin gado zama tayi gami da zabga uban tagumi taci serious tana kallon SHAHEED.
           fuskantar HANIFA SHAHEED yayi sosai ya ce, "ya kike ganin Aunty AISHA ina nufin halinta da mu'amalarta a school.? cike da rawar kai HANIFA ta ce, "Aunty AISHA tana da kirki sosai hamma, kowa fa na sonta a makaranta malamai ɗalibai saboda kirkinta hamma, kuma ita ke mana MSS a school fa, kai malama AISHA tayi ɗari bisa ɗari hamma" SHAHEED dake saurarata ya ce, "nima sai na ji ta burge kaɗan kamar yarda ta burge HANIFA dai" washe baki HANIFA tayi kaɗan can SHAHEED ya ce, "BABY kina son zama da Auntyn ki AISHA..? fuskar BABY da murmushi ta ce, "ina so mana yaushe zamu je gidan su.? SHAHEED dake kallonta ya ce, "zama fa na har abada dani dake da ita kamar na wancan hoton kuma a gidan mu" HANIFA da bata gane nufin SHAHEED ba, tanƙwashe ƙafafunta tayi da farin ciki kan fuskarta ta ce, "shikenan itama zata zama ƴar gidan mu hamma, mamar su zata yarda ta dawo nan to.?
   "Eh mana zata bari amma yanzu gobe zaki rakani na roƙi ita aunty AISHA.? SHAHEED ya faɗa yana ciza laɓɓansa ɗan murmushi HANIFA ta saki ta ce, "Zan rakaka mana kuma ta ganni zata amince ta dawo gidan mu fa, shikenan zan ƙara samun ƙawa" HANIFA ta faɗa tana kuma ƙanƙame SHAHEED zare hannunta SHAHEED yayi yana cewa, "BABY wata rana sai kin cire mun wuya naga alama" turo bakinta HANIFA tayi ta ce, "wuya kuma hamma.?
"Eh mana kin girma amma har yanzu baki nutsuwa irin na ƴan mata, ke ko hugining mutum zakayi sai ya ji ajikinsa kamar zaki cire masa wuya." SHAHEED ya faɗa yana dungure mata kai saman gadon ta faɗa dafe da goshinta har SHAHEED ya kai bakin ƙofa ta taso da saurinta tasha gabansa tana hakki ta ce, "hamma Assignment ɗin baka mun ba" SHAHEED daya zuba mata ido hannayensa cikin aljihu ya ce, "gobe babu islamiyya da safe BABY ki aje ki huta gobe da safe sai muyi tare, kafin ki rakani wajen malama ko" ɗaga masa kai HANIFA tayi gami da matsawa ya buɗe handle ɗin ƙofar ya fice daga ɗakin.
            Takawa tayi ahankali ta ƙarasa gaban tangameman hotonsu tana kallon hoton wanda sukayi su duka harda Aunty AISHA, hannayenta ta sanyata ta ɗauko hoton dake manne jikin bango SHAHEED na tsakiyarsu tana kallo, ahankali ta shafa fuskar hamma dake ɗauke da murmushi, sai dai har yanzu bata gane wani irin zama zasuyi tare ba su duka uku, hakan na nufi itama zata zama ƙawar hamma koya abun yake, sauke hoton tayi haka nan taji bata san ƙara ganin hoton ma tana kallon aunty AISHA ta wutsiyar idanunta wani abu ya tsaya mata cak a wuya biro ta ɗauko daga drawer ta saita fuskarta, turo ƙofar ɗakinta da akayi ne yasanya HANIFA waigowa da sauri tana ɓoye biron hannunta ta sakin hoton ya faɗi NABIL ne ya shigo ciki ɗakin da murmushi kan fuskar BABY ta ce, "hamma NABIL.! BABY ta faɗa tana turo baki saman sofa ta zauna tana facing NABIL dake bakin gado da mug hannunsa yana sipping coffee NABIL dake zaune miƙewa yayi ya ƙaraso kusa da HANIFA yana kallon kyakyawar fuskarta, kamar me karantar wani abu hannayensa ya sanya ya zare glass ɗin dake manne saman fuskarta gami da zare hula kanta gashin kanta ya watse gadon bayanta yana kallonta ya ce, "BABY kin fi kyau haka" NABIL ya faɗa yana zaro wayarsa dake aljihu ya ɗauketa hoto yayinda BABY ke sakin murmushinta me kyau, jawo hannunta yayi ya ce, "zo ki gani" gaban mirror suka tsaya yayinda NABIL ke kallonta yarda tayi mugun kyau ta cikin mirror ya ce, "ƙanwata kina da kyau sosai, idan babu wannan glass ɗin idan kika sanya glass ɗin nan komawa kike kamar tsohuwa" NABIL ya faɗa yana son fashewa da dariya, waigowa HANIFA tayi tana fuskantarsa ta ce, "hamma SHEED bai taɓa faɗa mun haka ba dan haka ban yarda ba" BABY ta faɗa tana son amsar glass ɗin hannun NABIL wanda fuskarsa ta sauya lokaci ɗaya cikin faɗa-faɗa ya ce, "ke komai akayi hamma SHEED hamma SHEED, kullum shi ya iya faɗin gaskiya, kullum shiya iya magana shi ya iya komai kullum nima hamman ki ne kamar yarda hamma SHAHEED yake, kuma dai gaskiya na faɗa maki" watsar da kayan hannunsa NABIL yayi ya fice daga ɗakin har yana buga mata ƙofa ɗaukar glass ɗinta tayi tana gunguni Allah yasa bai fasa mata glass ba, ɗaukar glass ɗin tayi ta maida kan fuskarta da hulata wadda NABIL ya watsar ta koma saman gado ta kwanta cike da mamaki NABIL shi kuma haka rayuwarsa take sam ba'a zama inuwa ɗaya da shi ayi hira sai hayaniya.

*Follow me on facebook page n group*:  *salma mas'ud nadabo*

*Follow me on IG*:  *Salmerh 777*

#VOTE
#COMMENT
#SHARE


~Taku har kullum salma mas'ud nadabo~

WATA ƘADDARAWhere stories live. Discover now