WATA ƘADDARA

79 1 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
                   *WATA ƘADDARA*
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*Story*
      *And*
          *Written*
                  *By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
{'''we are here to educate our readers, alƙalami yafi takobi'''}

       *WATTPAD*
*salmamasudnadabo*
         

https://t.me/joinchat/VeIADhya0PsbdP9QSD1MDg

   *FREE PAGE*

*Page: 25*

            *Wannan littafin na kuɗi ne for those of you da suke san karanta littafin complete zaku turo 300 kacal a account number na 2261453630 ummusalma mas'ud nadabo zenithbank sai kiyi/kayi screenshot na evidence of payment ki/ka turo ta number na ta WhatsApp 07063683025 sai nayi adding ɗinki/ɗinka a group ɗin da nake posting, zaki iya turo katin Mtn for those of you da basu da account*

                ........Washe gari da safe HANIFA na tashi wanka tayi ta shirya ciki wata doguwar rigar atamfa wanda aka ɗinka mata babu shape ko kaɗan, ɗinkin kamar irin na tsofafin nan jaka tsaye gata da uban girma hata hannun kayan dogone kuma mai faɗi, kamar irinta biyu zasu shiga ciki, ba kowa bane da wannan aikin ba sai SHAHEED dama shi ɗinki in dai namiji zai kaima sai kayi haƙuri, bale kuma shi SHAHEED da gangan yake cewa ayi mata wadatacan ɗinki, bai sun gani tsiraici shiko tella ya zage yayi su duk su mata yawa, kuma ko sau ɗaya SHAHEED bai taɓa cewa ɗinkin baiyi ba kuma bai taɓa ɗinka mata riga da skirt ba, sai da zani kuma riga ayi a wadace mai girma wuyan ne kaɗai ƙarami sai uban kalaɓi, shiyasa kafin ta sanya atamfa abune mai wahala dan basa mata kyau ko kaɗan, saboda yanayin ɗinkin tafi ganewa ta sanya after ko abayas, ƙasa ta sako bayan ta tamke kanta tamau kamar ƙulin goro kitchen ta ƙarasa jin motsin Umma a kitchen ta ce, "Umma ina kwana."
  "lafiya lau HANIFA, kin tashi lafiya.?
"Lafiya lau Umma" kallon kayan jikinta Umma tayi ta ce, "yanzu saboda Allah wannan atamfar ma irin wannan ɗinkin MAGAJI ya bada akayi.? wannan ai cin mutuncin atamfa ne" Umma ta faɗa cike da takaici HANIFA dake ɗauko ruwa cikin fridge da fruit ta ce, "Umma kuma ƙawaye na duk ba haka ake masu ɗinki ba, amma ni hamma sai ya kai amun ɗinki mara kyau" BABY ta faɗa tana turo baki, Umma ta ce, "gaskiya yau zan masa magana wannan wani irin ɗinki ne saboda Allah ko INNO dake datijuwa bata sanya wannan kayan ba" INNO dake gefe ɗan murmushi tayi tana jefa ƙosai cikin fryingpan ta ce, "gaskiya kam ko ni aka ba wannan rigar maleji zanyi da ita kam, dan nafi ganewa kayan zamani, ko na samu jawari ɗan uwana mu daidaita" ƴar dariya Umma tayi tana girgiza kai yayinda Umma ke sheƙa koko, BABY na haɗa fruit salad dan shi take son sha BABY ta ce, "yanzu INNO har aure zaki kumayi bayan kin tsufa, har da jikokin fa.?
         "atoh HANIFA miji ya zo ai sai mu lallaɓa daga ciki ko" sosai abun yaba HANIFA dariya Umma kuwa har suka gama aiki a kitchen tana bitar yarda aka wulaƙanta atamfar, dan super ce mai tsada ta kai 30k amma SHAHEED ya kai an wulaƙanta.
             Atare suka jera komai a dining na breakfast Umma ta ce, "HANIFA ki ƙarasa ki tasamun su hamman ki yanzu, baccin ya isa haka" gyaɗa kai BABY tayi tare da nufar ɗakin NABIL, koda ta murɗa ƙofar ɗakin NABIL gam tajita a datse knocking ƙofar ɗakin tayi da ɗan ƙarfin cikin ɗaga murya ta ce, "hamma NABIL ka tashi inji Umma" ƙara buga ƙofar ta ɗanyi da ƙarfi buɗe ƙofar NABIL yayi da idanunsa ɗauke da bacci yana murza idanunsa gami da haushin HANIFA daya ƙumesa dan ya tsani a tasheshi yana bacci, kuma dama jiya ta ƙona masa rai sai zafin ya haɗe biyu, ware manya idanunsa yayi kanta.
             Tun daga sama har ƙasanta ya fara kallon HANIFA dake cikin uwar babba riga, ga idanunta sunsha glass sun ƙara girma ta cikin glass ɗin dariya ce ta kwace masa babu shiri ya ce, "BABY wannan wasu irin kayane haka.? kin ganki kuwa kamar aljanna babu kyan gani, wallahi tsoro kika bani lokacin dana ganki" turo baki HANIFA tayi ta ce, "na ji ɗin babu komai ai hamma na SHEED ne ya ɗinka mun" taɓe baki NABIL yayi riƙe da ƙugu ya ce,  "na gani ai wannan aiki ai sai shi ɗin, ƴan mata na wayewa amma ke kullum cikin duhun kai, ni wallahi kunya ma zan ji na nunaki matsayin ƙanwata da wannan shiga taki kamar ta ƴan buri kin kama kai kin tamke kamar ƙulin goro" NABIL ya faɗa yana sheƙewa da dariya, wani irin kuka HANIFA ta saki tare da yin sama fuuu ta wuce Umma kan NABIL Umma ta waigo ta ce, "ka shiga hankali NABIL.! sosa ƙeya NABIL yayi yana cewa, "Allah kau Umma baki kanta ba" NABIL ya faɗa ya guntse dariyarsa saboda kallon da Umma ta watsa masa.

WATA ƘADDARAWhere stories live. Discover now