Babi na Daya {1⃣}

147 5 1
                                    

💓💓"FATI MASIFA {1⃣}"💓💓

🔛 "Babi na {1⃣}"🔛

Episode {1⃣}

🌐NASIHA NE🌐
Mutane biyu ne suka ci moriyar duniya: Wanda ya rubuta abin da ya kamata a karanta, da wanda ya aikata abin da ya kamata a rubuta(ALLAH) yasa abinda muka rubuta mai amfani ne.......

Typing........✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍

🔛 story and written by 🔛
WALIYULLAH
MUH'D
ABDULLAH

As Mash~Waleed

episode {1⃣}

**BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM**

Da farko ina farawa da suna (ALLAH) mai kowa da kowa mai yanda yaso ga wanda yaso ko ana so ko ba'a so tsira da aminci su tabbata ta shugaban halitta ANNABI(S.A.W)

Wannan littafin mai suna (FATI MASIFA)kirkirarran labari ne wanda banyi shi don ciin zarafin wani ko wata bah haka garurukan da nayi amfani dasu.....

So don(ALLAH)ga wanda wani bangare na littafin yayi dai-dai da rayuwar sa yayi hakuri akasi aka samu
Kafin mu shiga wannan littafin ga wata yar NASIHA akan abubuwa HUDU 4 masu amfani a rayuwar mu....

Masu sunan Fati kuyi hakuri

*HAKURI*

Hakuri kuma haske ne domin yanasa mai shi ya fita dg cikin duhun dimuwa dake ciki har ga kaishi ga harshen nasara. Allah yace kayi bushara ga masu hakuri. Kuma wani abun burgewa ga hakuri Allah ne da kansa yake tare da masu hakuri. Kuma cin nasara yana tare da masu hakuri.

*TSARKI*

Tsarki rabin imani ne domin shine rukunin ibadarh, idan babu tsarki babu ibadarh. Idan kuma babu ibadarh babu imani.

*SALLAAH*

Sallah annuri ce domin tanasa mai ita ya shiryu saboda ayoyi da yake karantawa da tawali'un da yake cikinta.

*SADAKA*

Sadaka dalilice ga ingancin imanin mai fitar da ita daga cikin dukiyarsa da kuma samun tarin ladarh ranar gobe kiyama.

ina fatan (ALLAH)ya bamu ikon yin aiki dashi

FATI MASIFA
Labari na Daya
Mafarin chakwakiya

****Bismillahi rahmanin rahim***"

Garin AWE wani gari ne daga cikin yankin NASARAWA karamar Hukumar LAFIA BARE-BARI bazance mai kauye bah don bunkasa ya wuce ace mai kauye Gari ne wanda ya kunshi dumbin al'umma yare da kabilu kala-kala sunyi tarayya acikin garin AWE local goverment zaman lafiya kuwa wannan ba'a maganar sa

Wannan ya samu asali ne sakamakon samun jarumin SARKI (HRH.ALH.ABUBAKAR UMAR )Mutum mai jajir cewa da son zaman lafiya a yankin sa hakan yasa cikin yankin babu maganar kabilanci ko bam-bamcin Addini
Wannan kenan......

*****KARFE 2:30 NA DARE*****

babu abinda kake ji sai kukan tsuntsaye ko ta ina amsakuwwar kukan sune wani katon tsuntsu mai faffadar fuska tamkar na mage sai kaiwa da komowa yake wannan, kukan sa yayi dabam cikin sauran tsuntsaye don kukan sa daban yake sai faman juya kai yake yana kururuwa idan ya kalli GABAS yakanyi wani irin kuka sannan ya juya YAMMA ya sake canza salon kukan nasa haka KUDU da AREWA sai faman kuka yake duk wani bangaren da ya juwa yakan chanza salon kukan sa....

Bayan wasu dan lokaci sai ga mutane sun fara bayyana DAYA BAYAN DAYA wasu suna futowa daga kasa wasu kuma daga sama wasu suna zuwa ne a suffar tsuntsaye wasu suna zuwa a suffar MAGE cikin suffar halittu kala-kala suna bayyana daga bisani sai su juya su zama mutune tsaye suke sun jere gaban BISHIYAR da wannan TSUNTSUWAR take ta tsuwwa WATO(AKIKI) ko (MUJIYA)yara ne kanana da samari sai tsofaffi dukkan su tsaye gaban bishiyar bayan kowa ya hallara sannan wannan (MUJIYAR) yayi shuru da kukan da yake yanayin shuru ya bace bayan bacewarsa kacokan su suka juya gun wani wutan tsafi dake famam ruruwa dukkan su zaga wutar sukayi tsirara babu kaya ajikin su sai manyan su wanda suke sanye da JAN kalle daure akan su sai zanin da suka daure a kugunsu duk wanda ka ganshi da wannan kyallen to mai matsayi ne a wannan kungiyar

FATI MASIFAOnde histórias criam vida. Descubra agora