💓💓"Fati Masifa"💓💓
🔛 "Babi na {{2⃣}
Episode {2⃣}Typing........✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍
🔛 story and written by 🔛
WALIYULLAH
MUH'D
ABDULLAH
As Mash~Waleed
NASIHA NESauqi yana tare da tsanani.
Mai haquri yana cim ma daxi.
Mai kyauta ba ya
rasawa. Kowa ya ji tsoron
Allah, Allah zai yi ma sa
mafita. Manta da damuwa ka
fuskanci rayuwa. Kowa ka gani
a duniya akwai abin da ya dame
shi.
✔ Gamon Katar✔***LAFIA BARE-BARI***
"Lokaci ne na Damina zaune suke cikin Daki in banda kuka babu abinda take"
"Kawartace Zaune a gefenta sai Faman Lallashinta take amma tamkar Zugata take
"Haba Hajara sai kace yarinya karama kin tasani gaba sai faman kuka kiketayi kinki ki fadamin meke faruwa, ki sanardani wata kil mu samu Mafita"
Sassautawa tayi da kukar da takeyi tayi tare da share kwallar da ya cika mata ido ta juya ta fuskanci kawarta wanda itama ita take kallo"
"Cikin raunanniyar murya tace" Muklisa ina cikin damuwa mara misaltuwa ABBA yana son saka zuciyata cikin kunci, Abba yana son salwantar da rayuwata, Muklisa ki duba Ashekaru irin nawa shine Wai na fidda miji idan ba haka ba ABBA yace aure zayyimin"muklisa ni wai abba zayyiwa aure auren ma da wanda ban sani ba bansan Halayyar saba,na takaita miki yanzu haka wai yasa abokin sa ya tura dansa don yazo yaganni yana zuwa za'a saka rana wai da zarar na gama G.S.S.3 za'ayi bikin Don (ALLAH) MUKLISA ABBA ya kyautamin idan kowa ya kini ina tunanin umma zata tsayamin amma wai UMMA tanaji Abba yace zai yimin aure amma ta kasa cewa komai" kukan da ya kwace mata yasa ta kasa karisa maganar"
Wanda aka kira da MUKLISA
"cikin tausayawa ta dube kawar nata tace" Hajara kalleni"
"Daga rinannun idanunta tayi wasu zafafan hawaye na kwaranya a farar fuskarta ganin haka yasa MUKLISA cewa"Hajara ki daina kuka don ba kuka ya kamata kiyi ba, nasan cewa (ABBA)bai kyauta ba sabida A tunani irin nawa ABU BIYU basu da riba SOYAYYAR da babu Aure Da AUREN da babu soyayya" Nasan cewa ana samun Kalu bale da yawa game da AUREN da aka gina shi akan soyayya to amma wani irin zama kike ganin za'ayi idan akace Anyi auren da babu soyayya,kinga auren dole bashi da fa'ida amma ga da mai biyayya ba abin aibu bane dafa kafadarta tayi tace kawata, Abu daya zan iya gaya miki shine kiyi hakuri Don hakuri Haskene sannan Arayuwa akwai abinda kake tunani alkhairi ne agare ka amma sai ya kasance ba alkhairi bane, akwai kuma abinda kake tunanin cewa ba alkhairi bane sai shi kuma ya zamto alkhairi So hajara kada kiyi fushi da zabinda iyayenki za suyi maki wata killa shine alkhairi Agare ki"Hajara"ke kawatace a matsayin kawarki idan har bazan so abinda zai cutar dake ba ya kike tsammani agun iyayenki"
"Kina tunanin cewa abba zai zaba miki abinda zai cutar dake ne" Hajara idan abba bai inganta rayuwarki ba wa kike ganin zai inganta rayuwar ki"ki sani mutani biyu Ba'a samun kamar su" UWA DA UBA"wa kike tunanin zai iya inganta rayuwar wani Don ya fishi,
"Wa kike tunanin zai iya tallafawa wani ya samu nasara Arayuwar sa Ba tare Daya bukaci wani abu Daga wajen wannan bawan(ALLAH) bah, wa kike tunanin zai iya Taimakawa mutum Bayan wancan ya samu Nasara sai yaki taimakawa wanda yayi sanadiyyar samun nasarar sa, kinga Ai maganar gori zai tashi" amma UBA shine yake ke iya taimakawa dansa ya inganta rayuwarsa har dan ya cimma Nasara Arayuwarsa ba tare dayaji haushin hakaba"abin nufi ki sani UBA yana iyayin aikin GADI da kudin gadin zai biyawa dansa kudin Makaranta DAN yazo ya zama babbar Ma'aikaci"yana samun kudi wand ya kamata ya inganta Rayuwar UBAN amma sai kiga DAN daga shi sai YA'YANSA da MATAN SA A haka UBAN bazai mai gori bah kinga daga nan Babu kamar UBA"sannan da kina cewa Umma tanaji tayi shuru ki sani"
"Duk son da DA" yakewa UWA be kai kwatan-kwacin wanda UWA take mai bah, UWA ita take manta kanta a addu'a ta shagaltu dayiwa ya'yan ta'
"UWA CE danta zayyi laifi tace sharri akayi masa"idan kuma an kama shi REDHANDED akan laifin da yayi"UWA zata mai UZURI tace tsautsayine "HAJARA-ki sani Duk duniya babu wanda zasu iya nuna miki so da kauna kamar iyayen ki'amma a haka kike musu GURGUWAR fahimta gaskiya kawata bazan iya baki shawara akan ki bijirewa iyayenki ba Domin(ALLAH)yana yarda da yardar su sannan yana fushi da fushin su"Umma dake tsaye kofar dakin ta natsu tana sauraran su tana mamakin irin kaifin hankali da basira irin na muklisa'wannan yana DAYA daga cikin dalilin da yasa take Son muklisa ko yaushe ta kasance kusa da Yarta Hajara"
"Share hawaye dake gangaro mata tayi tun farin maganar kawar nata duk jikin ta yayi sanyi sai da tayi jim kadan sannan ta motsa bakinta da yayi mata Nauyi duk da haka tanaji a zuciyarta cewa tana da ja akan maganar muklisa"tace Muklisa banaki zancenki bane amma ina da yakinin baki san yanda ake ji bane idan za'ayiwa mutum auren dole wallahi muklisa dakin san irin yanda zuciyata ke zugi dakin tausaya mini'sannan bana da wani buri face in zauna da mijin da zamu kasance a tare har karshen rayuwata kuma hakan zai faru ne idan na auri mijin da nake so DON wallahi bana tunanin zuciyata zata iya samun sukuni idan aka hadani da mutumin da ba shine zabina ba Muklisa ina takaita miki wallahi inaji a jikina har idan na aure mijinda bana so to Babu Makawa Nasan ni Yar WUTA ce"
"Subhannallah don(ALLAH) hajara ki daina fadin haka"
"Muklisa dole na fada sabida gaskiya nasan cewa Bazan iyayin masa biyayya wanda zai sa na samu aljanna ba'kuma yin haka zai sa (ALLAH) zaiyi fushi dani kinda dolene wuta ta tabbata agareni" don yanzu haka ni kadai nasan abinda zuciyata keyi muklisa ke kawata ce kinsan baxan iya boye miki komai ba to wallahi ji nake idan akamin auren dole nima dole zan kashe miji i will definently kill the bastard
Umma dake labe bakin kofa Dafa kirji tayi take lamarin yarinyar ya fara bata tsoro
"toshe mata baki muklisa tayi'haba HAJARA stop this ribbish ki daina fadan haka mana sai kace karamar yarinya ANNABI(S.A.W)yace faal yaaqhul khairan Aulii yaasmut) ki fadi alkhairi ko kiyi shuru"why are you behaving like abnormal person
Ko kinsan cewa ba lalle bane yanda mutum ya tsara rayuwar sa yake samu ba sai yanda (ALLAH)Ya tsara masa'Hajara ki godewa (ALLAH)da harke Abba ya baki zabi idan kina da wanda kike so ki fidda me zakice ga Wanda kuma basa sanin mijin da za'a auran masu sai ranar aure sannan zasu ganewa idanun su mijin wasuma sai akawo su gida sannan zata gan wanda aka aurar mata amma haka zaki gani suna zaman lafiya sassauta muryar ta tayi taci gaba da cewa Kawata kar son zuciya yasa kice zaki sabawa iyayenki ki daure kiyi masu biyayya Hajara ko kinsan rashin Biyayya da kyautatawa mahaifa yana cikin mafi girman zunubi
Hakika Annabi(S.A.W) yayi mana umarni kamar yadda(ALLAH)da kansa yayi mana umarnin akan yin biyayya da kuma kyautatawa mahaifa da kuma hani daga sabawa masu da kuma cutar dasu,sabawa mahaifa da rashin kyautata masu yana cikin mafi girma zunubai da akewa yiwa (ALLAH)anan duniya Annabi(S.A.W) ya baiyana mana illa da girman laifin mai sabawa Mahaifansa let me tell you the small one Mai Cutar da mahaifansa Tsinanne ne inji Manzon(ALLAH)(S.A.W) haka kumaDaga Abu Hurairaita R.A yana cewa :-"Annabi(S.A.W) yana cewa:-
(La'antacce ne mai cutar da mahaifansa ko mai sabawa mahaifansa)HAJARA ko kinsan (ALLAH)bawa kallon mai sabawa Mahaifansa a ranar alqiyama".
haka kuma Daga Ibn Umar R.A yana cewa:-"Manzon (ALLAH) (S.A.W) yace:
(Mutane guda ukku Allah bazai kallesu ba a ranar alqiyama:-
-Mai sabawa mahaifansa
-Wanda baya kishin iyalinsa
Mai sabawa mahaifan sa baya shiga aljanna haka an sake karba Daga Ibn Umar R.A yana cewa:-Manzon (ALLAH)(S.A.W) yace:(..............Mutane guda ukku bazasu shiga aljanna ba a gobe alqiyama:-
-Mai sabawa mahaifa
-Mai kwankwadar giya
-Mai yin gorin abinda ya bada)
Haka babu mai shiga aljanna sai wanda ya kasance yana biyayya ga mahaifansa kuma baya saba masu bari na baki wani kissa kadan a zamanin ANNABI(S.A.W)Wani mutum yazo wajan Annabi (S.A.W)sai yace Ya Manzon (ALLAH) (S.A.W)"Na shaida babu abin bautawa bisa hakki da gaskiya sai (ALLAH) kuma kai Manzon (ALLAH) ne, kuma nayi salloli biyar na farilla, kuma na bada zakka kuma nayi azumin watan Ramada?? Sai Annabi (S.A.W)ya ce:Wanda ya mutu akan haka yana tare da Annabawa da Shahidai Siddiqai a ranar alqiyama matuqar bai sabawa Mahaifansa ba)
HAJARA"(ALLAH) baya karbar aiyuka na mai sabawa mahaifansa inji Manzon (ALLAH) (S.A.W) haka kumaDaga Abi Umamah R.A yana cewa:Manzon (ALLAH)(S.A.W) yace:
(Mutanan guda ukku(ALLAH) baya karbar aiyukan su na farilla da na nafila:-
-Mai sabawa Mahaifansa
-Mai gorin abinda ya bayar
-Wanda yake karyata Qaddara).
HAJARA Ki sani Sabawa mahaifa yana cikin mafi giraman zunubai inji Annabi (S.A.W)ina rokon maki (ALLAH) daya nisantar dake daga aikata abinda zai sanyaki sabawa Mahaifanki
"Umma da har yanzu take labe agefen kofar dakin don kar su ganta maraba da samun kawar arziki tana jinjina tare da farin cikin samun mutuniyar kirki amatsayin kawar yarta taso lokaci da yanayi dake garinyaba muklisa daman cigaba da convincing hajara game da taurin kanta amma hakan bazai yiwu bah sakamakon wani hadari daya hadu yamai da sararin samaniya wani irin baki ga kuma dare na sake shugowa don Goma ta kusan cika"
"Jefa kai da umma tayi cikin Dakin shi yasa muklisa yin shuru da natsuwa domin kunya da girmamawa har yanzu hajara share hawaye take"
"Muklisa ya kamata ki tafi gida haka karki biyewa wacanan wawiyar sai kace akanta aka fara auren" ki barta ki tafi gida kinga Hadari ya hadu yana barazanar zubar da ruwa ga kuma dare yayi nasan cewa yanzu haka auntyki tana nan tana jiraki balle kuma yanda wannan hadari ya hadu nasan yanzu hankalinta a tashe yake"kiyi sauri ki tare abin hawa kar ruwa ya tareki cewar umma da tana yiwa muklisa magana tana hararar hajara wanda sai faman hawaye take"
"To umma nan muklisa ta dauki hijab dinta ta saka"
"kunce hannun zanin tayi ta bata kudin mashin dagyar muklisa ta karba don ita tana da kudi a jikinta umma na mika mata ta futa daga cikin dakin"
"Haka itama HAJARA ta mike cikin sanyin jiki ta saka hijabin ta suka nemi haryar fita"
"Suna futa farfadan gidan sai da gaban Muklisa ya fadi ganin mugun hadarin dake sama ganin umma tayi tana kyara robobi domin tare ruwan sama tsugunawa muklisa tayi ta sallami umma"to muklisa ki gaida aunty ki da kuma dadin naki" to umma zasu ji shigowar Shigowar Abba yasa muklisa cikin ladabi ta sake tsugunawa tare da gaidashi"da fara'a Abba yace Ah'ah muklisa yau kece agidan namu ya kamata kiyi sauri ki koma gida kinga yanda hadari ya hadu ko'
"To abba ta mike"
"Hajara da ganin abba yasa taji wani bakin ciki ya cika mata zuciya yasa take shirin koma daki lura da hakan yasa umma ta yanka mata kira"komawa zakiyi ba zaki rakata bakin hanya ta hawa abin hawa bah"
"Tana sane tayi hakan don tunda ta hango abba shine ta fara daure fuska killa idan yaga ta daina walwala zai iya janye kudirin sa nayin mata auren dole don har yanzu bataji zata iya rayuwar aure da mutumin da bata son shi.
"Fuska babu walwala ta juwa tazo nufi kofar fita binta da ido Abba yayi yana mamaki irin halinda hajara ta tsuro dashi kwana biyu na yawan fushi dason kadai cewa ita daya da rashin son futa waje' girgiza kai yayi (ALLAH)ya kyauta" ya wuce dakin sa"umma tabi bayan sa"
"Duk yanda muklisa sun so samun abin hawa abin ya gagara sunfi kusan 20 minute suna tsaye babu abin hawa ga kuma hadarin da ke sake tasowa gaba daya sama ya bata rai"
"Kallon mukilsa hajara tayi tace kawata ina tunanin mu fara tafiya idan yaso indan mun hadu da mai Adai-daita saiki hawa don naga kamar nan babu alamun gilmawarsu"
Gaskiya kam is like the sky has pregnant murmushin yake hajara tayi don ta tuna da wani malamin sune amakarantar boko Sir Aliyu AJAX wannan yana daga cikin saran Sa inbadan halinda zuciyarta take ciki ba da babu abinda zai hanata dariya fahimtar hakan yasa muklisa yin shuru "Haka sukaci gaba da tafiya tana cigaba da bawa hajara shawara" kawata don kinga Abba shine kin wani bata rai"
"Muklisa ki barni kawai baki san damuwar da nake ciki bane"
"Hajara kenan natsalana dake naci baki dauki shawarar dana baki ba kenan ko hajara kiyi hankali da zuciyarki fah ki sani cewa Arayuwa idan kin tuna baya akwai abinda yake sakaki cikin damuwa idan Kuma kika hangi abinda zaki tarar nan gaba zakiji tsoro to ki kalli sama chan ne inda mai war-ware matsala yake abin nufi ki kaiwa(ALLAH)kukan ki don bana tunanin yawan fushin da kike shine zaisa Abba ya canza ra'ayinsa kamar yanda na gaya miki ki roki (ALLAH)idan alkhairine Auren (ALLAH)ya tabbatar ya hada zuciyoyin ku idan kuma ba alkhairi bane (ALLAH) ya zaba miki abinda yafi alkhairi ya baki zabinki wanda lokaci daya zaku aminta da junan ku" jin wannan addu'ar yasa hajara sakin wani murmushin jin dadi wanda yasa muklisa kallonta"itama murmushin muklisa tayi da alamu kawar taji dadin addu'ar da tayi mata sai fama maimaita amin hajara take tana murmushi wanda kana gani kasan na farin ciki ne"tabe baki muklisa tayi don ta lura kawarta tafi son irin wannan hirar yasa itama kawai ta biye mata ta kalle ta haba hajara sai kace an baki kujerar makka irin wannan dariya haka amma na tambaye ki mana?"wai wani irin miji kike burin samu Arayuwarki"
"Wani shewa tayi tare da rufe fuskarta da tafin hannunta har da dan tsallenta tayi" kallo muklisa ta bita dashi tace ke hajara muna wajene fa kike irin wannan tsallen don (ALLAH)ki kama kanki"
"Sauke wani nan nauyan ajiyan zuciya tayi wanda yake kunshe da nishadi tace Muklisa bari kawai ba zaki gane bane wallahi ji nake ina ma ace ABBA ne yayimin irin wannan tambayar da nafi kowa farin-ciki" tabe baki muklisa tayi kyaji dashi ni dai bani amsar tambayata"
"Wayyo kawata tambaya mai dadi mai saka nishadi"gaskiya da farko kawata ina son miji wayayye wanda ya iya soyayya sannan ina son miji mai tsoron (ALLAH) Mai kuma kula da addini sabida miji mai addini shine komai zayyi zai miki ne tare da tsoron(ALLAH)"
"tabe baki muklisa tayi hmm su malama hajara amma me yasa kika zabi son miji mai addini??"
"Jim hajara tayi tana dan murmushi tare da nazari sannan tace"kawata ina da dalili sosai na son auren miji mai addini"Da farko Ina son auri miji mai addini saboda zai ke faɗa mini gaskiya a kodayaushe"
"Ina son auri miji mai addini saboda zai girmama iya'yena a koda yaushe saboda suma zaina daukan su kamar iya'yenshi"
"Ina son auri miji mai addini saboda zai girmama "ƴan uwana da kuma dangina"
"Ina son auri miji mai addini saboda yana ko'yi da Annabi MUHAMMADU (S.A.W)a kodayaushe zaike tayani aikace-aikacen gida sabida yana daga cikin koyi da sunnar ANNABI(S.A.W.) ina son auri miji mai addini saboda zai sha'yar dani madarar soyayya da kuma bonbitan soyayya a zaman takewar mu ta aure
"Ina son auri miji mai addini saboda zaike hanani aikata muna'nan ayyuka yana Tunasar dani game da tsoro (ALLAH)"Ina son auri miji mai addini saboda shi aka ɗaura'wa haqqin tsare'ni da "ƴa "ƴana daga shiga wuta a ra'nar gobe"
"Ina son auri miji mai addini saboda zai tausaya mini a rayuwata
"Ina son auri miji mai addini saboda zai riƙe mini sirrina a koda yaushe"
"Ina son auri miji mai addini saboda bazai cu'tar dani a zamanta kewar aure mu ba sabida yasan illar hakan"
"ina son auri miji mai addini saboda zai ke faɗa mini gaskiya akoda yaushe
"Ina son auri miji mai addini saboda "ƴa "ƴa na za'suyi alfahari dashi a ra'yuwa"
"Ina son auri miji mai addini saboda zaike umurtana da aikata kyawa'wan ayyuka"
"Gaskiya abinda na fahimta muklisa samun miji mai addini kyautane daga(ALLAH)"Sannan akarshe ina son miji wanda zai soni kuma ya dunga ban kulawa wanda bazai taba batamin rai ba"
"Dariya ne ya kubucewa muklisa na maganarta na karshe" kallon tsarguwa hajara tayi mata to me nayin min dariya"sai da muklisa tayi mai isarta sannan ta kalli ta lallai hajara kina ruwa ko nace kina da aiki yanzu kina nufin za'a iya samu miji mai kyawawan halayyan nan kuwa wanda bazai taba bata miki rai ba haba sai kace (ANNABI) duk mai irin halayyar annabawa fa kika lissafo kawata duk da cewa nasan babu abinda yafi karfin (ALLAH)ke dai kici gaba dayin Addu'a"
"Insha (ALLAH)sai na samu mijin mai irin wannan halayyar"
"Hahaha wani samu zakiyi bayan nan da Dan lokaci zaki zama Amarya da zararfa yazo kun hadu shi kenan fa kin zama amarya amma a hakan kike tunanin zaki samu mai irin halayyar da kika lissafo'
"jin haka yasa hajara hada rai"duk da tasan gaskiya ne muklisa ta gaya mata "fuskantar yanayin da taga hajara ta shiga annurin fuskarta duk ya sauya ta hada rai yasa muklisa cikin lallashi ta dafata"haba amaryar mai tsoron(ALLAH) mai kyawun halayya"
Take taji wani sanyi aranta"Dariyar jin dadi hajara tayi nan sukaci gaba dayin hirar su"murmushi itama muklisa tayi tace yana daga cikib abinda yasa hajara na burgeta bata da wuyan bata rai haka kuma bata da wuyan sauka
YOU ARE READING
FATI MASIFA
General FictionLabari Daya Mai Salo Daban-Daban Wanda Ya Kunshi Rayuwa, Soyayya, Cin Amana, Butulci , yarinta, girman kai, Izza matsalar aboki Da dai sauran su Kudai kada ku bari abaku labarin fati masifa