*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Story by SaNaz_deeyah'''*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_Visit to like our page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_
'''Shafi na 4'''
Hannatu ce ta shigo ɗakin ta kalleshi murya ƙasa-ƙasa tace "Yaya kafin ta kirashi na kira nace dan Allah yace Mama ce ba lafiya, kuma ya nuna damuwa a tare dashi, dan haka na kashe matsalar. Yanzu kawo kayan in fita sai mu haɗu a waje in baka." Yaji daɗi sosai. Ya ɗauki baƙar ledar ya bata tare da cewa "Nagode Hanne" Karka damu" ta faɗa tare da zura ledar a Hijab ɗinta. Sai da tayi kamar mintuna biyu da fita sannan shima ya fita. A zaune ya tarar da Umma a falon. Zama yayi kusa da ita tare da faɗin "Umma na ɗan samu ƙarfin jiki, dan Allah ki barni naje ba daɗewa zanyi ba, kuma na daɗe ma ban leƙa waje ba, shiyasa nake son fita."
"Nayi waya dashi yanzu, naji alamun akwai damuwa ma a tare dashi, kaje ɗin amma ka kula da kanka"
"Insha Allahu." Ya faɗa cikin jindaɗi sannan ya tafi.
A ƙofar gida yaci karo da Hannatu. Ta miƙa masa ledar tare da faɗin "A gaida min ita, ace nayi kewarta sosai, insha Allahu idan Umma ta huce zan zo har gidansu sai a rakani gidan ta"
"Zan faɗa mata insha Allahu" ya faɗa yana murmushi. "To a dawo lafiya" "Allah yasa" ya wuce ita kuma ta koma cikin gida.
Gidan su Saminu ya fara zuwa lokacin ana ta kiraye-kirayen Sallar magrib dan haka sai da sukaje masallaci sukayi sallah sannan ya shirya, shima Saminu ya shirya sannan suka tari Napep zuwa _The Royal Evenue Event Center_ inda anan ne za'ayi kamu.
*****Hall ya cika damƙam babu abinda kakeji sai tashin kiɗa. Jannat da Khalil shigar blue sukayi, ita anyi mata irin gown ɗin nan ta amare Royal blue shi kuma shadda ya saka light blue. Sai ita kuma Safina ta saka White gown shima Ahmad shadda ɗinsa white. Ɗinkinsu iri ɗaya ne sai dai color ya banbanta su. Mazan kuwa Gethner ce a jikinsu. Kai kana ganin bikin kasan na manya ne. Kowa yayi shiga ta kece raini. Ƙawaye duk sun sha anko, sai kuma tsilli-tsillin mutanen da basuyi anko ba suma sun saka kaya ubansu. Mommy da Daddy kuwa suna daga gaba dan tables da ban aka ajje masu su da baƙinsu.
Biki ya ɗauki zafi an kira shahararrun mawaƙa sai baje basirarsu suke a gurin.
Ana ta hotuna wasu kuma na fili suna rawa. Da hannu Jannat tayi wa Farhan alama tazo. Ƙarasowa tayi ta ɗan sunkuya. "Farhan ya banga Sa'ad ba, ko bai kiraki ba?" "Ya kira yace min yana waje sai na bawa Jiddo ta kai masu guda biyar kamar yadda kika ce"
"Haba Farhan ke ya kamata kije da kanki fa" "Sis calm down zata bashi wallahi na bata fa"
"Okay" ta faɗa. Khalil ne ya kalleta Yace "Babe dance competition kin iya rawa kuwa ko ni ne zanyi winning?" Murmushi kawai tayi wanda ba har ciki ba, dan hankalinta yana can bakin ƙofa tana son taga shigowar su Sa'ad amma shiru.
Ta ɓangaren su Sa'ad kuwa ko da Jiddo taje da kallon wulaƙanci ta bisu dashi sannan tace "Wai wane Sa'ad a ciki ko kuwa masu gadin gurin ne ku?"
"Ke karki nemi ki faɗawa mutane magana" Saminu ya faɗa cikin ɓacin rai. Sa'ad yayi saurin riƙeshi tare da cewa "Ƙyaleta Saminu, taci darajar Jannat" "To dama idan bai ƙyaleni ba, ya zai yi dani, ko nayi kallar wadda zai iya bugu?" Murmushi Sa'ad yayi tare da cewa kece Farhan "Oho maka koma wacece ina ruwanka, gashinan guda ɗaya aka bani in baku, duk da dai babu class ɗinku a ciki" tana miƙa masa ta juya tayi shigewar ta.

BINABASA MO ANG
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Historical FictionGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...