_*🤷🏻♀️HATSABIBIYA🤷🏻♀️*_
*💖RAMLAT💖**_(Editing🤏🏼)_*
_*NA*_
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
*Ƴar Mutan Niger🇳🇪*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
~*DEDICATED TO*~
_My Jidderh ummu Lubnah_ _Wallahi Ke ɗin Me_ _Ƙaunatace, Ciki Da Waje Kiji Daɗinki Tawan Iya wuya Ana Jone Waje Ɗaya.🤝🏼😘_*Na Saukarwar Wannan Pagen* _Gareki Ƴar Gatan Mmn Sultan,_ Agsky Inajin Daɗin Zazzafan Comments Ɗinki, much love.💗
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
_*Chapter 5*_
Murya da naji tana ƙirana ne yasa na sauka ajiyar zuciya, cike da murnar ba mugun soja bane ya Ƙirani, na ƙarasa jikin ƙofar ina faɗin “My bro dan Allah, ka faɗamin gsky, kaga nifa ƴar gaban goshinka ce... Kai da waye anan?” Muryashi ya ɗan ɗaga murya yana faɗimin“Ramlat kifa yi maza ki buɗe ba lokaci wlh soja yanzu ya shigo tare da mukarabansa, ceton ki nazo yi.” Ai cikin rawar jikina na rawa na buɗe ƙofar shigowa yayi Tv yaje ya kasha ya kama hannuna cikin sauri yake tafiya dani, tsabar tsoro ya hanani nayi mgn, har muka fita rufe ƙofar yay ya zare key ɗin yana riƙe da hannuna muka fice.
gate ɗin muka ga sojoji kusan biyar atsaitsaye, face Ya Naseer ya haɗe ya murzawa ƙofar get ɗin key ya yaja Hannuna cikin sauri, mukabi ƙofar baya, direct part ɗin Dadata muka nufa.
Muna shiga ya hankaɗani cikin falon cikin faɗa yake cewa“Wai ke wata irin yarinyace da batasan ciwon kantaba? Me ya kaiki part d'in Abdallah idan da ya ritsaki kinsan irin hukuncin, da zai miki? To wai ina ma kika samu makullan gidansa?” Bakina na turo gaba ina murguɗawa nace“ Wai bro saboda naje motsa jiki shine duk kakemun wanan masifar?” na tambayesa ina tsaresa da kyawawan ƙananun idanuna.
Ya Naseer ya zaro manyan idanunsa😳yace “Ramlat! Yanzu in gama cetonki amma zaki fitsareni? Shigowata kenan da mota naga kin nufi part din Abdallah bayanki nabi har lokacin da kika shiga ko minti goma ba ayiba suka shigo, sa'arki ɗaya idan yazo sai ya jima part ɗin Yimnah wlh yau da kashinki ya bushe.” ya faɗamin yana hararata. Cikin jin haushin dawowar mugu nace“ To ngd azuba-zuba kai ko gajiya bakayi da surutu....”Murya Dadata mukaji tana faɗin“Kai Naseer! meye ka takurawa shalelena?” cike da shagwaɓa nace“ Dadata waifa dan naje part ɗin mugun soja nayi casu shinefa, ya rufeni da masifa.” na faɗa ina diddara ƙafafuna.
Dadatace dani“Au shine ya tsareki kamar kinyi sata?” kaina na ɗaga, ina murguɗa baki.
Ya Naseer baki ya saki galala yana kallonmu kafin yace“To yayi maku kyau ni dai bazan faɗi masaba, amma wlh ku guji ranar da zai damƙeta.” dariya nayi na kamo hannayensa, ina faɗin“Haba brona wasa nake maka fa, muje ka rakani part ɗinmu.” na ƙarashe mgnr cike da sangarta.
Ya Naseer murmushi yayi yana janye da hannuna muka fice, ina faɗin“ Dadata zan dawo. Dada tace “To shalelena. Tafe muke ina riƙe da hannunsa, sai idanu nake ƙif² dasu, tsoro ya cikani. Harabar gidan ko ina sojoji sai hararasu nake dan haushi, wani matashin sojane ya bini da kallo baisan ina lure dashi ba, ta tsinin ido. Ai kuwa na tsaya cikeda tsiwa nace “Kai!! Ƙaramin soja wlh ka kiyaye kallon Ramlat dan ba sa'arka bace, ko wanda ya taraku ana tsoron kallona yake... Saboda ina gaba dashi bare kai karamin alhaki... Kujishi da idanunsa irin na ƴan cirani.” cikeda ɓacin rai naga ya nufomu ko gezo banyiba daga inda nake tsaye Naseer ne yajani yana faɗin“Wai ke meye zai sameki? Wlh ogansu idan yaga kina musu rashin kunya jibgarki zaiyi.” baki na turo gaba, ba tare da nayi mgn ba, ya jani muka tafi, sai kuma naji abin ya ciyoni.
Munzo daidai ƙofar su Yimna Abdallah ya fito cikin kakinsa na soja, wanda yayi mutiƙar yi masa kyau tamkar ka saceshi dan kyansa. Ina cikin masifa My“ bro yo ni wanan ƙaramin alhakin zai rainawa hankali, da kabari na koya masa hankali yo bashi ko Abdallah mugu...” ban kai ƙarshan mgnr ba, idanunmu ya sark'e da na juna, nida mugun soja. Ai bansan lkcn da na saki ihuuu ba iya ƙarfina, ina ririƙe Ya Naseer jikina har rawa yake.
Shiko ko Soja suna haɗa idanu na farko ya kawar da kansa gefe, dan shi idan ba dole ba to sam ya bayason abinda zai haɗa su da ita.
Ko kallon inda suke bai ba, yasa kai ya fice, saboda ma'aikatan gidan sun fara nufo wajan nasu. Jajayen lips ɗinsa ya ciza, aransa yana faɗin“Akwai ranar ƙin dillanci shegiya mai zubin karuwai, sai na shayar dake gubar azaba mafi muni, arayuwarki. part d'insa ya nufa cike da takun kasaita yake tafiya. “Wata ƙatuwar ajiyar zuciya na sauke ganin mugu ya wuce bai kulamu ba.. Ai ganin ya tafiyarsa na saki Ya Naseer na zuba da gudu iya karfina nake gudu ban zame ko inaba sai cikin parlour'n ɗinmu. Cikin sa'a Papi na zaune jikinsa na faɗa ina shasheƙar gajiya.
Riƙeni yayi yana faɗin “ Ramlatuna! Daga ina kike keda wa kike gudu haka?” fashewa nayi da kukan munafurci, nace“ Wlh papina wanan mugun sojan ne ya takurani ya tsaneni bayason ko ganini yanzu ma gani nayi yazo daga bulaguro.. Wai kai da naka naje gaishesa wlh papina ba kaga cin fuskar da ya min ba, abin baya faɗowa saboda gudun fitina...”ji mukayi ana dikira ana salamcewa, Mummy ce tana faɗin“Ke!! Wlh Ramlat! Kiji tsoran Allah ƙarya kike soja baya shiga harakarki abanza-banza...” Papi netari numfashinta“ Wai ke Rahma me Ramlat ta miki? Ai sai kibar yarinya ta gama bayaninta.. Oya ci gaba ina jinki. Bakina na turo gaba nace“Papi mubar maganar kasan uwar ɗakinsa ce yanzu sai ta kwashe tas ta faɗa masa.” na ƙarasa mgnr ina matsar ƙwalla. Dariya papi yayi yace“To shikenan mu bari ɗin... Mummy tana hararata tace“Ni ko zakici ƙaniyarki mara's kunya kawai.” ban kulata ba, nace da papina.
“Papi kasan yanzu kawai a haɗa meeting a mana tsakani dashi, kasan fa mugune wlh idan ya kamani zalumtata zaiyi.” murmushi yayi yace“Ke dai kikace baki masa komaiba to meyasa kike jin tsoran haɗuwar ku bayan kinsa shalelen mummyn kine koda wani lokaci zaki gansa a nan.. Ai wajan Abbi ɗinki zaki shi zai muku tsakani.“ cikin zaƙuwa nace“To papi muje ka rakani...” “A'a jeki abinki.” mikewa nayi ina kumbure² bedroom ɗina na shige ina gunguni.
Wanka nayi na gabatar da sallah la'asar na kwanta ba jimawa bacci yayi awon gaba dani, duk da nasan babu kyau, baccin la'asar.
Abdallah yana zuwa part ɗinsa kai tsaye bedroom ɗinsa ya shiga, ya cire kakin sojoji ya ɗauki towel ya Shige toilet shower ya sakarma kansa idanunsa lumshe A hankali yake sauke tagwayan ajiyar zuciya. Ya jima sosai kafin yayi wanka ya fito, yana goge murɗaɗɗan jikinsa, maiyuka masu sanyin daɗi ya murza ya saka jallabiya, ya fesa turaruka masu mutiƙar kamshi yayi sallah la'asar, kayan shan iska ya saka ya fito parlour'n.
Kan wasu lumtsuma lumtsuman kujero dake cikin parlon ya zauna remote ya dauka ya kunna Tv yanaso ya ga labarai atashar CNN. Yana tsakiya da kallon, l yaji ƙaran waya, cikin mamaki ya kalli b
ɓangaran da yake jin ƙaran.. Ai kuwa idanunsa soka sauka akan wata waya mai masifar kyau tana neman ɗauki mike'wa yayi ya nufi gun wayar ɗauko ta yayi har lokacin ƙiran bai yanke ba. Picking ɗin call ɗin yayi ya manna wayar kan kunnensa, aikuwa yaji ance“Hello my Ramlat haka mukayi dake? Meyasa kike mun wulakanci? Yau kwana uku ina bin kanki amma kin ƙi saurarata, wallahi nasaka anyi maganin sa.. Ai yasan waye ubana agarin nan, duk iskancin sa bai isa ya ja daniba, kuma nasa an hanashi Shiga, duk wata Club da Muke zuwa bare hakan ta ƙara faruwa, yace shi bai busa miki hayakin sigari ba baima san bakison warin ba, please ki daure yau....” dif soja ya yanke ƙiran kanshi har juyawa yake jikinsa ko ina rawa yake, sbd tsabar baƙin ciki, dabas ya zauna kansa ya dafe yana faɗin “Innalillahi wa'innah ilaihir raji'un!! Acikin gidan namu aka samu tantiriyar yar iska haka? Wayarsa ya ɗauka ya ƙira wata number, banji mai yake faɗaba har ya gama ya miƙe ya fice daga parlon.
Ban tashi ba daga baccin da ya saceni sai kusan magarib, nayi wanka bayan nayi sallar magarib na shiyar cikin riga doguwa wta Ja marar hannu, ta shan iska, tayimin kyau sosai.. Sai fa lokacin na tuna wayana part ɗin Soja.
Wayyo ni Ramdede, asirina ya gama tonuwa ya zanyi?” na faɗa ina rarraba ƙananun kyawawan idanuna. Tunawa nayi ba fa lalle bane yaga, inda na ajiyeta. “To yanzu ya zanyi da masu ƙirana? Tsaki naja wlh idan yana so in ya kamani kar ya barni da raina. mike'wa nayi zuciyata ko ɗar babu, yau na sadaukar ko kasheni zaiyi wlh sai na fita, haka kawai jaraba.
Part ɗin Yimnah na nufa. Kutsa kauna nayi parlon, ko sallama banba, Yimnah tace“ Daga ina kike?” bakina na turo gaba idanuna na fara ciccirawa, kana kana kallona kaga mara gaskiya. Na gyara tsayuwata nace“Abbi nake nema qara na kawo gunsa. Yimnah tace“Dota qaran kuma? Waye ya taɓoki? Zo muje muyi sallar isha'i kafin baban naki yazo.” binta nayi mukayi sallar isha, fitowa falo mukayi, munzo ba jimawa Abbi ya shigo.
Tarosa nayi ina faɗin “Abbi ƙara na kawo maka fa.” na faɗa ashagwaɓe. murmushi yay yace “To waye ya taɓomin ke?” “Wlh Abbi sojan gidan nan ne ya addabeni ko fita ban isa nayi ba, ya kama jibgata kamar jaka.” na faɗa cikin kukan munafurci.
idanu Abbi ya zaro yana tambayata “Wai Abdallah dai? Tab barni dashi...” ƙamshin turaransa ya daki hancina, wanda yasa na waigo ina kukan ƙarya. Ai kuwa na hangoshi yana shigo da sallama. Ai bansan lkcn da na faɗa jikin Abbi ina ɓoye kaina ba, ban yarda na kuma kallon inda yake ba.
Soja bai sam bama Allah yayi ruwanta awajan. Abbi naji yana fadin“Yauwa Soja me ƙanwarka ta yima kake dukanta?” Se lkcn na ɗan leƙo da kaina naga yazo wannan ƙwala² idanun nasa, amma baiyi magana ba, na kalli Abbi sai naga ya kashe masa ido, baki na turo jin Abbi na faɗin“ To ina so daga yau bakai ba taɓata ko kasa iyi mata wani Abu.” dadine ya kamani jin mugu na faɗin“To Abbi zan kiyaye. Abbi yace “Da yafi maka. Muryar mugu naji yana faɗin“ Abbi ina son zamuyi magana zuwa gobe.” Abbi yace“Ok Allah ya kaimu mazajen fama.
Abbi ya kama hannuna muka zauna, soja na kusan Yimnah azaune, ta shafa kansa tace“To taso kaci abinci. Naga ya yamutsa fuska yace“Yimnah wlh banajin cin komai. Ya faɗa yana mike'wa ya musu sallama yana ficewa, yana zance zuci“ Wlh kafin na aiwatar da ƙudirina sai kinci ubanki dole sai kin sa kankance zan rama tinda na samu abin ramuwa mafi sauƙi, ko wani yace ki kuma zuwa part ɗina ba zakiba.
Tin ranar da Abbi yace ma soja kar ya taɓani agabana, naji daɗi sosai sai sabin isakanci nake inacin karena babu babbaka, a gidan iskanci kala-kala har bakin gate nake zuwa ina karairaya, nayitama sojoji rashin kunya nace ko xaku kamani ne kukaiwa maras kunyar soja ne? ko kallona basayi saboda sunsa idan ina jin mugunta narasa wa zan yima agidan nake nufosu.. Dan na taɓa riƙewa wani ido acikun su har gani ya fasayi, sai dakyat na rabu da ɗan banza.
Yau gidan namu cike yake da jama'a ana ta hidimar bikin mutum biyu wanda gobane daurin aure Ya Naseer, da kuma Ya sulaiman, nayi ɗinki sama da kala biyar, nasha gyaran jiki sai kace wata amarya, nasha kyau har na gaji gashina taje an canza masa kala an min wani ɗan banzan kitso kana ganin kitson kasan ba ƙaramar HATSABIBIYA bace xatayi shi.. Amma hakan bai hana nayi min kyau ba tamkar kasaceni, an min zanen ƙunshi ƙafa da hannu, wanda yayi mutiƙar min kyau, nida kaina nasan na haɗu ba ƙarya.
Misalin ƙarfe biyu na rana, wanka nayi na shirya cikin wata guntuwar riga wada ko guiwa bata zoba tsaki naja ciki mussing ɗin wayata ina lussafawa yau fa har kwana uku banida waya.. Allah sarki my khaleel I miss u yau zanyi iya yina mu haɗu zuwa dare..
Haniya naji tayi yawa a parlour'n su jaraba duk abin an cika guri da surutu bara natafi part din Dadata na kwanta na huta dan wlh yau sai naje casu.
Hijab na saka a saman karamar rigata, dogone har ƙasa na fito. Mutane nata aiki sai magana suke min banza na musu na fice Rabiyatu tace “ Yau ko yan iskan ne? Dariya sukayi sukaci gaba da harako kinsu.
Atsakar gidanmu ma ba wanda na kalla na ficewata direct part ɗin Dadata na nufa. Parlour'n shiru ba kowa, ƙiranta na fara“ Dadata! Kina ina ne?” Laure ce ta fito daga kitchen tana faɗamin “Ramlat Dada ta fita fa suna tare da baƙine tana part ɗinsu Alhaji ai.” bance da ita ƙalaba na nufi ɗayan ɗakun Dada mai gadon gargajiya me rumfa na cire hijab ɗin na haye na saki rumfar gun yayi duhu nayi kwanciyata dama ga gajiyar shegen kitson da aka min nan danan bacci yayi awon gaba dani.
Zaune suke a falo ta ƙirata“Mamah ina son komai ya tafi yadda ya kamata fa.” bushewa tayi da dariya tace “ Haba yarinya ai wallahi insha Allah sai haƙata ta cinma ruwa, kema taki ta cinma ai ni idan bana kaunar abu to wlh sai naga bayansa, ko ta halin ƙaƙane, tashi kije kici gaba da sha aninki cikin jama'a yanzu zanje wajan
( *boka makasheta*) yaushe zanbari ai sunyi kaɗan, yadda naci nasara hanata zama wani abu tin farko to yanzu hakance zata kasance.” bushewa sukayi da dariya ta mike ta fice cikin sauri mota ta dauka ta fice daga gidan.
Gudu take tamkar zata tashi sama cikin abinda bai fi 30 minutes ta isa wani gungurumin jeji. Anesa tayi parking ta fito wani tsauni ta haye daga nesa take hango, dandazon mutane, anabin layi guri ta nema nesa kaɗan da jama'a gundun haɗuwa da idon sani aƙalla tafi awa guda cur tana jira kafin ta samu ganin (boka makasheta,) Kamar yadda ta saba da baya da baya ta iso gunsa juyowa tayi ta lailayo uban zagi tamasa kafin ta shige ɗan ɗakin ta zauna gabansa, zatayi magana ya ɗaga mata hannu, yana faɗin“ Sanin kankine ba'a ba makasheta labari sai dai ya bayar.. Kuskure na karshe da zaki ƙara shine ki kuma zauwa kice zaki faɗamin abunda ya kawoki...” ya faɗa yana bushewa da wata mahaukaciyar dariya. “zaki samu duk abinda kikeso abu biyu zasu gagaremu... A cike da firgici tace “Ya kai la'anan ne makasheta meye wannan abu?” Wani ɗan ƙoko dake rufe yawa mgn, kawai ƙoƙon ya buɗe cikin muryasa marar daɗi yace“Ki kalli ƙoƙon. Kallon ƙoƙon tayi ai cike da firgici ta miƙe tsaye jikinta na rawa take faɗin“Yakai la'anan ne ka taimakeni bazanso haka ta faruba...” katseta yayi ta hanyar cewa “To da sharaɗi zaki zo na rinƙa anfani dake har tsawon kwana uku idan kin amince zansan yadda nayi...” cike da rawar jiki tace“Na amince biyan buƙata yafi dogon buri, tinda mijina basani zaiyi ba muyi wani Abu.....Hummmm....... _*Muje zuwa🧚🏽♀️*_