Shafi na 8

134 8 0
                                    

*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
           _[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
  _[Karamci tushen mu'amala tagari]_
     Email-Karamciwritersass@gmail.com

Visit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb

_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_

                    '''Shafi na 8'''

________________📲Trolley ɗin ta ta janyo, Safina ta tayata suka ɗauke ƴan kayan da basu cikin trolley suka mayar ciki.

"Ina sauran kayan ki ne?"
Safina ta tambaya tana kallonta.
"Na barsu a gida, ban san ina zanje ba, ta ya zan ta maimaici, cewa Aunty Mamy nayi ta ɗebo min kala bakwai."
"Okay sai kawai ki riƙa saka nawa ko?"
Murmushin ƙarfin hali tayi, taji wani son ƴar uwarta ya mamaye ta.

                ****

Ɗago sleeping eyes ɗin sa yayi yana kallon abokin nashi daya shigo.

"Fahad ka ƙaraso kenan"
"Eh mana, dole na ƙaraso tunda na lura har yanzu akwai damuwa a tattare da kai duk kabi ka rame sai kace mace"
Kujera ya nuna masa sannan yace "Zauna dai mu yi magana."

Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da Fahad ya zauna. Sunkuyar da kai yayi ƙasa, Fahad ya zuba masa ido kawai yana jira ya faɗa masa damuwarsa.

"Fahad ina cikin damuwa, kuma kaine aboki mafi kusanci dani, dan haka kai ya kamata in fara tunkara, saboda neman shawara"

"Okay, go on me yake faruwa?"
"Fahad tunda na auri Farhan, amma bamu taɓa zama a matsayin mata da miji ba"
"Are you serious? Khalil kanka ɗaya kuwa"
"Ba zaka gane ba abokina, yarinyar she's just 17, and ƙanwar Jannat ce"
"If ace ma 10years gareta ina ruwanka, an mata aure kuma an san meke faruwa a cikin aure kayi enjoying kawai"
"Taya zan fuskanci Farhan"
"She's your wife ko ka manta hakan"
"Ƙanwar Jannat da take kallona a matsayin Yaya kuma ita zanje in kusanta? Ni fa shiyasa ko abincinta bana ci dan kar taga fuska"

Gyara zama Fahad yayi sannan yace "Kana cikin tsinuwar mala'iku indai ba zaka bawa yarinya haƙƙinta ba, maybe ma she has feelings on you, kana zuluntarta"

"Ina jin kunya gaskiya"
"Kai fa namiji ne, wace kunya a raya sunnah manzo Allah"
"(S.A.W), shikenan zan jarraba"
"Yau ba gobe ba"
"I'll do my best"
"Okay Allah ya taimaka, ya kuma baku zaman lafiya."

                   *****

Tana zaune a gefen gado tana waya, Jannat ta fito daga toilet, tana ɗaure da towel iya cinya.

"Mommy ga Jannat ɗin, yanzu ta fito daga wanka" Safina ta faɗa tare da miƙewa tana ƙarasawa inda Jannat take.

Hannu Jannat saka jikin towel ɗin ta goge sannan ta karɓi wayar ta kara a kunne hawaye cike da idanunta.
"Mommy.....!" ta furta lokacin da wasu hawaye masu zafi suka sauka kan kuncinta.

Daga ɗayan ɓangaren Mommy tace "Jannat meyasa idan na kira baki son ɗagawa?"

"Mommy bana son hankalin ki ya riƙa tashi, amma Mommy dan Allah ki bawa Daddy haƙuri a kan abinda na aikata"

"Kada ki damu, na san nan da kwanaki kaɗan zai huce yace ki dawo gida"

"To Mommy...!"

"Amma fa ki rage damuwar nan kar wani ciwo ya sameki"

SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅Where stories live. Discover now