Shafi na 9

121 9 0
                                    

*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
           _[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
  _[Karamci tushen mu'amala tagari]_
     Email-Karamciwritersass@gmail.com

Visit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb

_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_

*Not Edited⚠️*

                    '''Shafi na 9'''

________________📲 Da sallama ta buɗe murfin motar ta shiga ta zauna.

"Jannat ya naga kin ƙara zugewa" Mommy ta yi maganar tana kallon ta.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Mommy ina yini?"

"Jannat ka da ki kawar da maganata ta hanyar gaisuwa"

"Mommy! Am begging you, please forgive me despite what happened, bana son ɓacin ranku" ta fada tana sharar hawaye.

Da fa kafaɗarta Mommy tayi ta ce "Jannat ki kwantar da hankalinki, in dai ni ce na yafe miki and  everything is going to be alright"

Ƙara fashewa tayi da kuka mai ƙunar rai, Mommy ɗan shafa bayanta tare da ce wa "It's okay, am always with you ki share hawaye kar muje asibiti su gane kina da damuwa"

"Thanks you Mom am so glad."

Murmushi kawai tayi sannan ta tayar da motar suka fara tafiya.

"Wane asibiti ne?"
"Nassarawa"
"Okay"

"Mommy, Safina na ta complain baki shiga ba"

"Ba yau ba, amma daga asibiti, zamuje gidan Farhan"

"Gidan Khalil?"
"Nam fa, ko ba zaki raka va ke ma?"

Shiru tayi bata ce komai ba.

Jannat ita tayiwa Mommy jagora har ɗakin da Sa'ad yake. Da sallama suka shiga, Umma da Hannatu suna har haɗa kaya.

"Ina yini Umma" Jannat ta furta cikin girmamawa. Itama cikin sakin fuska ta amsa sannan suka gaisa da Mommy.

Sa'ad ma sauka yayi har ƙasa ya gaida Mommy, ita kuma ta duba shi.
  "Ba dai har anyi sallama ba?" cewar Mommy.
  "Sun ce dai yau zasu bamu, shiyasa muke haɗa kaya" Umma ta bata amsa.
  "Allah ya bashi lafiya"
  "Ameen ya rabbi"

"Shiru ne ya ɗan biyo baya kafin Umma tace "Hannatu zo muje ki rakani naga ko likitan ya dawo"

Miƙewa tayi suka fita, itama Mommy tashi tayi tace "Jannat bari na amsa waya ko?"
"To Mommy"

Tana fita ta matsar da kujerar ta kusa da gadon, ta ƙara kallon Sa'ad ta ce "Ka faɗa da yawa"
"Dole, Jannat a kanki zan iya mutuwa fa"
"Haba dai"
"Gashi kuwa kin gani, da ace kinyi aure kin barni da shikenan sai dai kiji labarin mutuwa ta"
"I see Allah ya baka lafiya." Ta faɗa tana murmushi.

"Ameen, amma i wish you know how my heart were hurt for something i desire, and how am disturbed with pain and couldn't sleep either wallahi Jannat kasa faɗa miki nayi ina sonki but abin is hurting me ta ciki sosai."

"It's Okay, yanzu dai am all yours, amma what have you planned for our life? I mean after marriage, what kind of better life have you arranged for us?" ta faɗa tana ƙara ƙura masa oily eyes ɗin ta.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce "Jannat kenan, bani da arziƙi amma still i arranged you many things in life. I will try to avoid what will make you angry, i will become your happiness, i will try my best not see you shading tears"

SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅Where stories live. Discover now