☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
WANI HANIN GA ALLAH
(baiwa take zamowa)
🍂🍂🍂🍂🍂🍂MALLAKIN;
FATEEMA ZARAH MAZADU💕💕💕
AND
ASMA'U NAANERH (NASMERH) 💕💕💕MARUBUTAN:
1:ABINDA YAKE RAINA
2:A ZURI'AR MU
3:IN KE RABO NACE
4:AYISHERH
5:MRS BILAL
6:BARRISTER MUHAMMAD
7:WANI HANIN GA ALLAH. LOADING...........✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.**Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
***************
Page 📄fourteen1️⃣4️⃣(SHE'S GETTING TIRED😌💪READY TO FIGHT BACK)MAHEER yace“Ni ba wai bana sonta bane,,, amma rashin jinta, kasan bata ji ", SADEEK yace “Amma kasan yadda yarinyar take, zaka iya canza ta, sai kace dai ba namiji ba, kuma ai kana sonta dama nasani", tsaki MAHEER yaja sannan yace “nifa matsala ta da kai baka da hankali, nifa ba irin sonda kake tunani ba, kawai dai wasu daga cikin halin ta suna burge ni, kuma tana da ilimin addini, beside ma ni ba abunda zanyi da ita ta min ƙarama", SADEEK yace “kai kasani, idan tayi wari maji "
NI KUWA ASMA'U NAANERH NACE MUNA NAN ZUWA DAI, DAGA BURGEWA ZAKA CE KANA SONTA, KUMA YANZU GURI YA ƘURE, DAN FATEEMA ZARAH TAYI AURE TA BARKA🤣💃
*******'*************
Akwana atashi ba yawa gurin Ubangiji, yau MAHEER ya share kimanin sati biyu a Gembu, kamar yadda kuka sani MAHEER mutum ne da bai cika yawan magana, gidan duk baya mishi daɗi, kuma dangane da maganar FAHAMA, shi ya haƙura dan dama bawani sonta yakeyi ba, shi kawai ya damune saboda yasan irin haka ba daɗi, saboda haka shi yanzu harkar gaban shi yakeyi.Ta ɓangaren FAHAMA kuwa, yau kwanan ta uku a asibiti, yau dai kam jiki da sauƙi, zaune take tayi matashi da filo, Mommy ce ta shigo ɗakin, murmushi FAHAMA tayi sannan tace “Mommy kin shigo kenan ", Mommy tace “eh Wallahi, nayi meeting ne da matan commissioners, kinsan yau nashirya meeting dasu", “eh haka ne fa"FAHAMA ta faɗa tana kama hannun Mommy.
“Yauwa ƴata, zo nan Mommynki taji ɗuminki ", faɗawa tayi jikin Mommy da ta zauna kan gado kusa da ita, “Mommy na samu sauƙi, yaushe za'a sallame ni", Mommy tace “insha Allah, muna sarai yau za'a sallame ki ", murmushi FAHAMA tayi, wanda yafi kuka ciwo, Mommy ta lura da haka, “FAHAMA, ya kamata ki cire damuwa aranki, insha Allah rashin auren MAHEER alkhairi ne, ki yi imani da Allah, insha Allah Allah zai biya miki da mafi alkhairi", “Allah Mommy ba damuwa, nagode".
Rufe bakinta keda wuya, likita ya shigo, takarda sallama ya basu sannan suka wuce gida, acikin mota shuru tayi ta rufe idonta, dole ne rashin samun MAHEER ya dameta, arayuwarta bata taɓa soyayya ba, gida ana ta mata faɗa ta kai munzalin aure amma kuma batayi ba, ranar da ta fara ganin MAHEER agurin siyayya sai taji kamar ta cika, zuciyar ta, ta samarwa MAHEER babba masauki, sai gashi ƙaddara ta raba su.
*****************
FATEEMA ZARAH
Kwance take kamar kullum, tayi baƙi ta rame, amma duk da haka kyanta na nan.Shigowa FARHA tayi, da wani kallo take bin FATEEMA, “Ke dallah tashi kin wani bar mutane da yunwa, baki da aiki sai kwanci ", FATEEMA da ta fara gajiya da abunda FARHA ke mata tace “Ke da baki kwanci, aikin me kikeyi", “kut ni zaki gayawa magana" FARHA ta faɗa tana ɗaukar hannu zata kaima FATEEMA duka, riƙe hannunta tayi tace, “karki sake tunanin dukana, tunda ni ba jaka bace ", mamaki duk ya cika FARHA “FATEEMA ni kike gayawa magana haka", “eh an gaya miki ke wacece", “ni matar da MU'AZ zai aura ce " FATEEMA ZARAH tace “waye MU'AZ", “lallai yarinyar nan kin riƙa, to mijin ki nake nufi", “ohhhh, wai mijina kike nufi, to sai mi idan ke wadda zai aura ce, ni kuma matarshi ce, kuma bake ke aurena ba, mijina zaki aura baki da hurumin da zaki juya ni ", FARHA taji haushi sosai “Amma ai ke matar da baya so ce" ta faɗa, FATEEMA tace “and so, ko ba komai za'a ce me mata kika aura, kuma yarinyar da kika girma nesa ba kusa ba, Kinga ko kinyi abun kunya", FARHA ta rasa abun cewa, faɗa ta kama FATEEMA dashi.
Masu karatu kan kuce me FATEEMA ta kai FARHA ƙasa ta hau ruwan cikinta, dukanta takeyi kamar ba gobe, sai ihu FARHA keyi ba mai ceto.
NI KUWA NACE TURA TAKAI BANGO
MU'AZ ne ya shigo gidan, ihun FARHA ya jiyo daga parlor da sauri ya wuce inda yake jiyo sautin ihunta, yayi matuƙar mamaki daya ga ɗakin FATEEMA ZARAH ne, shiga yayi da sauri, ƙafarshi ya saka ya shure FATEEMA ta faɗi ƙasa, belt ɗinshi yacire yafara dukanta, tashi tayi, haɗa kanta yayi da bango ai kuwa nan take jini ya fara zuba, hannunta tasa ta dafe, kuka take kamar ranta zai fita, Allah yasani ta gaji da zama gidan nan, da daɗi da ba daɗi ta zauna, kuka Takeyi me tsuma zuciyar me sauraro, masu karatu da zan faɗa muku irin kukan wataƙila wasu daga cikin Fans ɗinta sai sunyi kuka.
*******************
MU'AZ ne yake wa FARHA dressing ciwon ta, sai wani narke mishi takeyi “yanzu baby bazaka ɗauki mataki ba, da Allah be kawo ka ba da yau sai buzu na ", dariya MU'AZ ya fara yi, harara ta kai mishi “dariya ma ta baka yi ko", “yo ai kece, kinsan bazaki haɗa ƙarfin rainon birni dana ƙauye ba me ya kai ki faɗa da ita, kinsan bani gida ", shiru tayi na ɗan lokaci sannan tace “tsautsayi ne", “to ai sai ki kiyaye ".
“Nifa duk ba wannan ba kawai kazo muyi aure in ya so daga baya sai ka sake yarinyar can", “hmmmm ke bazaki gane, na gaya miki baba bazai yadda ba", da wani mugun kallo take bin shi har ya ƙara sa maganar shi “to sai me idan mahaifinka bazai bari ba, sai ka shirya muyi aure aɓoye, in ya so daga baya sai su sani ", “Anya FARHA zan iya, bari dai Mugani", “ban gane ba 🙄, kana nufin sai ka gani ma, to wallahi baka isa ba, auren mu kamar angama wani sati " FARHA ta faɗa cikin tsiwa, shiru yayi dan be da tacewa sai yaga yadda zata kaya dan shi ba wani son ta yake ba.DAMA NASAN ZA'A RINA GASHI NAN, BA KOWANE NAMIJI BANE ZAI LALATAKI KUMA YA AURE KI, BALLANTANA MA ACE YASAN KE KARUWA CE.
FARHA kam ta halbo jirgin MU'AZ, saboda haka ta yanke hukuncin zuwa gurin Daddynta ta faɗa mishi, ko baya so wallahi sai ya aure ta.
********
MASU KARATU SHIN KUNA GOYON BAYAN WANNAN AUREN NA MU'AZ DA FARHA.TO MASU KARATU MU HAƊU A NEXT CHAPTER DAN JIN YADDA DADDYN FARHA ZAI CE.
VOTE
SHARE
AND COMMENTS
PLSSSS 🙏HAƊIN GUIWAR
PRINCESS FATEEMA & QUEEN NASMERH 🌼🌼🌼🌼🌼🌼
ALQALAMI YAFI TAKOBI✍️💕💕💕💕💕💕💕💕💕
YOU ARE READING
WANI HANIN GA ALLAH
Acciónthis book is all about life challenges, and If you're asking God for blessings and He's still not answering that prayer, it could be that you are not asking in faith, truly believing He will answer. for that u have to learn how to be content whatev...