DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:Northern_life_stories.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littattafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis*
Part Two
Page SixSai abun ya bashi dariya don haka yasa dariya sosai manya fararen haqoran sa suka bayyana wani irin kyau da haiba na girman da ya sake yi suka bayyana shi daman mai kyau ne kuma bai cika dariya ba idan yayi sai tayi masa kyau sosai.
Basu wani jima ba suka yi sallama suka kashe wayar,ya kwanta yana lumshe idonsa dariyar Baby Eve ta dinga ratsa duhun daya lullube ganinsa,innocent cute face din ta na kama data Immileey sosai saidai ya kasa fahimtar kuma yarinyar da wa take kama sosai don dai kawai Immileeyn mahaifiyar ta ce qila amma kam tana kama da wani daya sani ba ita ba.
"Babyn nada kyau sosai." Ya samu kan sa da furtawa yana murmushi.
Wasa wasa kiran Mummy yayi wasa da Baby Eve ya zame masa jiki,itama kuma yarinyar ta saba dashi sosai duk sanda ya kira taga fuskar sa ta dinga murna kenan tana masa gwaranci dake dai tana da wayo sosai.
Juma'a ce da wuri su Immileey suka taso daga sch kuma basu da islamiyya sai yamma mallamin dake biya musu a gida yake zuwa tana zaune lungun gadon Mummy tana tilawa Mummyn ta shigo da Baby Eve da waya tana face time da Lameen,sai tsalle take tana son kamo wayar ta ajiye ta tana dariya lokacin da Lameen din ke mata wasa ta dora kan mirror inda bazata iya kamowa ba amma suna ganin juna.
Immileey tunda Mummyn ta shigo taji muryar Lameen taji ranta ya dan sosu da sauri ta zura earpiece a kunnenta ta cigaba da bin karatun cikin muryar sheikh shuraim,da farko bai ganta ba dukda wayar na kallon tane direct har saida yaji karatun ta a hankali sannan hankalin sa yakai kanta.
Sosai er qaramar muryarta mai sanyi ta dinga ratsa dodon kunnen sa tana zagaya kwanyar sa,duk da wasa yakewa Baby Eve hankalin sa nakan karatun tane har takai qarshen Suratul Maryam sannan ta rufe qur'anin ta cire earpiece din ta ajiye ta miqe tana ma Mummy sannu.
Ta kalle ta tana dariya tace "Kin gama kenan?"
Ta daga kanta tana juyawa tace "Eh Mummy."
Mummyn ta sake cewa "Ki gaishe da Hamman ku mana."
Ta juyo tana kallon wayar ta gama qagauta ta bar dakin tana yaqe tace da sauri sauri "Ina yini."
Kadaran kadahan ya amsa da "Lafiya."
Duk da yayi qoqarin basarwa a zahiri tana jin yanda idon sa ke yawo a jikinta mai sanye da doguwar baqar riga armless kasancewar ana zafi,ta dan kama jikinta ta sama ta qasa ne ta saki kanta sanye da turban ja mai stones a gaba,da sauri tabar dakin tana amsawa Mummy da "Toh."
Don tace in taje ta kira mata Amnah.
❤️
Ya cigaba da wasa da Baby Eve bayan fitar ta ita kuma Mummyn ta cigaba da duba wasu atampopi da da alama ba a dade da kawo mata ba.Amnah ta shigo da murnar ta tana dariya ta zauna kusa da Baby Eve tana fuskantar sa tace "My Jaan."
Shima yana dariyar yace "My Jaan how far."