Episode One

488 13 0
                                    

💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*DOCTOR'S FAMILY*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
'''®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓'''

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

_Thanks be May God bless everyone, peace and blessings be upon our leader Prophet Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, may God bless you and grant me the ability to write this book, may God grant me the ability to write what will benefit the nation ameen._

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY.*_

*LITTAFAN MARUBUCIYAR*
_NAFEESAT._
_BARRISTER IBRAHIM KHALIL._
_LABARIN DEEBIZAH._
_MALAMA LADI._
_JARUMAI_
_LUBABATU (ƴar ƙwallon ƙafa)._

.

*EPISODE One*

Doctor '' Al'ameen Abubakar Khabeer Cindo '' and his wife '' Prof. Nafeesa (Baby) Isma'il Audu, '' as you know in the story of * NAFEESAT * They live in Kaduna, and they still live in the city, owned by their five children.

*1_ DOCTOR NOOR (LAWAL AL'AMEEN ~YARON UMMEE NAFEESA~)* Wanda a yanzu ake kiran sa Big Dady, matar sa ɗaya *Hajiya Asiya (Hajiya) ƴa ga Muhsina,* yaran su uku, Doctor Usman, sai Doctor Zainab ~yanzu haka tayi aure,~ sai kuma Yusra.

*2_ HAJIYA RABI'ATU AL'AMEEN (IKRAM) ~WANDA A YANZU TANA AURE A GARIN KATSINA~* tana zaune da iyalan ta acan.

*3_ DOCTOR ABUBAKAR AL'AMEEN ~WANDA YANZU AKE KIRAN SA DA ABBA~* matar sa ɗaya Doctor Fatima (Hajja Fatu) ~ƴa ga Abokin Doc. Al'ameen wato Haidar da ƙanwar sa Ihsan,~ yaran su Biyu, Doctor Al'ameen (Baffa), sai ƙanwar sa Shakira.

*4_ DOCTOR AL'AMEEN AL'AMEEN (ABBU)* Matan sa biyu, ~Bilkisu (Umma) ƴa ga Baseera,~ yaran ta uku Doctor Zulaiha ~tayi aure,~ sai Fadila da autan su Fadil. Sai matar sa ta biyu *A'ISHA (AUNTY AMARYA)* yarinyan ta ɗaya '''NAFEESAT''' suna kiran ta da Ɗahira.

*5_ HAJIYA LAILA AL'AMEEN* yanzu haka tana aure a Kano, ta auri babban Yaron *WALID.* Suna zaune da iyalan su can.

Waɗannan familyn yanzu haka suna zaune ne a gida ɗaya kowa da part ɗin shi, sai dai akwai Babban parlour'n da ya haɗa su, yanzu haka Doc. Al'ameen Wanda a yanzu suke kiran sa da *KAKA* ya kai shekaru 89years. Tuni ya ajiye aikin sa sakamakon yana fama da ciwon ƙafa wanda a halin yanzu yana zaune ne a wheel chair, matar sa Prof. Nafeesa (Baby) Shekaru uku kenan da Allah ya amshi abin sa.

Za kuyi mamaki idan nace muku duk ka familyn Doc. Al'ameen gaba ɗayan su *DOCTORS* ne, wannan shine burin sa kuma Allah ya cika masa.

Babban asibitin da ya gina ya ƙara haɓɓaka shi wanda a halin yanzu Five Block ne, kuma sosai asibitin me suna *(AL'AMEEN FAMILY HOSPITAL)* tayi fice a ƙasar Nigeria, gaba ɗaya familyn suna aiki ne a Hospital ɗin.

Yanzu haka a halin yanzu an shirya yin babban Walima don taya Doc. Ɗahira(Nafeesa) Al'ameen Al'ameen, Doc. Shakira Abubakar Al'ameen, Doc. Yusra Noor Al'ameen, da Doc. Fadila Al'ameen Al'ameen. Murnan kammala karatun su na likitanci, wanda za su soma aiki ne a ranan da a kayi musu waliman tare da sabbin ma'aikata da za'a ɗiba a ranan.

*KU BIYO NI DON JIN LABARIN WAƊANNAN FAMILYN*

Zaune suke su Huɗu a Babban katafaren parlour'n gidan da ya'amsa sunan sa a haɗuwa da ƙayatarwa, da shigowan ka parlour'n Babban Hoton Prof. Nafeesa (Baby) zaka soma cin karo dashi, wanda tayi sa ne lokacin da ta zama Professor, tana sanye da baƙar abaya me tsananin kyawu da burgewa, wanda duk da kasancewar ta baƙa ba ƙaramin kyau yayi mata ba, sai tayane kanta da Milk Colour ɗin Veil, kyakykyawar fuskarta yalwace take da murmushin da ya ƙara fito da tsantsan kyawun ta tare da Dimpul ɗin ta, a tsaye take ta riƙe ƙugu da hannu biyu tare da ɗan ɗage kanta, da alamun sanda akayi hoton bata san ma za'a yi sa ba. kusa da hoton kuma wani tanƙamemen hoton ne da a cikin sa Al'ameen ne tare da ita Babyn, suna zaune manne da juna sun saka ankon shadda me ruwan powder, gefe da gefen su kuma Noor ne tare da Ikram jingine da jikin su, duk kan su dariya suke yi time ɗin da aka ɗauki hoton, sai gefe kuma sauran hotunan ƴan gidan ne kowa da iyalan sa, sannan sai aka ɗau guda ɗaya wanda su kayi gaba ɗaya familyn, shi wannan ba'a daɗe da yin sa ba, don gab da rasuwan Prof. Baby akayi sa, gaba ɗaya idan ka kalle su sosai suke kamanceceniya da juna, sai dai banbancin launi da ya raba su.

DOCTOR'S FAMILYWhere stories live. Discover now