Part Two Page Nine

213 11 2
                                    



DAMA TA BIYU
(The Second chance)

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU yayin da 'YAR JAGORA ta dauki KARA DA KIYASHI a rashin sani.......

Littattafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu

*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis*

Part Two
Page Nine.

•••••Abinci aka gabatar musu dangin shinkafa da miyar kaji da su taliya sannan lemuka daga na gwangwani zuwa na gargajiya zobo da kunun aya da Mummy bata yarda ta rabu dasu don ita na gwangwanin ba damun ta suka yi ba takan ce ita wannan gas din damunta yake yi don haka bata cika sha ba sai dole.

Suna ci ana hira,Immileey dai kamar ta koma cikin Goggo Lari haka ta dinga yi har saida ta gaji tace "Ke ni don Allah kin dameni kije can wajen Mummyn naki mana kin maqale min anan."

Zumburo qaramin bakin ta tayi tace "Kaii Innah."

Jannah tace tana dariya "Su Lily anga Innah shagwaba ta tashi."

Dariya kowa yayi banda Immileey dake ta cuno baki ita a dole an bata mata rai,Mummy tana dariya tace "Rabu dasu kinji Khadijatu ni taho wajen nawa da ake miki gori zo mu zauna muci qauna."

Dariya aka sake yi Goggo Lari tace "Allag bar qauna."

Mummy tace "Amin inda gaske kike."

Hira sosai akeyi ana dariya har magriba,Su Mooha suka fice don yin tasu sallar a masallaci yayin da matan suka yi tasu a gida.

An riga an sanar da Abeey zuwan su don haka ana magriba ya dawo tare gabadaya aka sake zama bayan aka dan taba hira.

Hirar bata yi nisa ba Abeey ya gyara zaman sa yace yana gyaran muryar janyo hankalin su gabadaya yana kuma kallon Mooha yace "Muhammad yi mana addua don zaman namu yayi albarka."

Mooha ya gyara zaman sa yana murmushi ya ja addu'ar yanda ya kamata,yana gamawa duk suka shafa a fuskokinsu tare da fad'in "Amin." Gabadaya.

Abeey da murmushi yalwatacce kan fuskar sa ya fara magana da "Ba wani abun ne yasa na tura a dauko ku ba kamar yanda kuka sani danaje nayi muku magana daman toh zancen passport ne ya taso mun gama magana da wanda zai yi muku gobe idan Allah ya kaimu zamuje gabadaya a kaiku ayi muku tare da Khadija,kamar yanda kuka sani a zulqhada/Zulqhida muke wanda yana mutuwa watan hajji zai kama kuma inshaAllahu wannan hajjin damu za ayi ta gabadaya banda Muhammad na riga da na gama shirye shiryen komai yanzun passports dinku suka rage wanda nasan nan da en kwanaki zai fito."

Hawaye Goggo Lari ta fara yi yayin da Baffan Immileey ya fara godiya yana shiwa Abeey albarka kamar ya ari baki Immileey kuwa da bata fahimci cewa harda su za a tafi ba sai ta soma dariya tana fad'in "Alhamdulillahi Innah ta zata je hajji babban burinta na duniya zai cika don Allah Innah ta kiyi mana addua sosai kinji,Mun gode Abeey Allah ya qara maka arziqi da wadata da yalwa mai albarka."

Amnah ce ta zungure ta tana dariya tace "Ke baza ki yiwa kanki addua ba me zakije yi kenan?"

Zaro ido tayi tana kallon ta tace "Me kike nufi?"

Jannah tace "Harda mu fa za a tafi bakiji me Abeey yace ba."

Ai yau gabadaya babu kunyar ta rarrafa wajen qafar sa tare da kama su tace "Wai da gaske ne Abeey abinda sukace?wai tare zamu tafi hajjin nan?"

DAMA TA BIYUWhere stories live. Discover now