_*🍒KWAƊAYI DA BURI🍒*_
_*MALLAKAR HAUWA S ZARIA*_
*(MMN USWAN)*_*SADAUKARWA GA MOMCY*_
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI._
_*BABI NA UKU*_
Nannauyar ajiyar zuciya Naseer ya sauke gami da rumtsa idonsa.
A ɓangaren Maimunatu kuwa sai bayan sallar asuba sannan ta falka, baki ɗauke da salati, gani gari ya fara wayewa yasata furta subhanallilahi!! badai har anyi Sallah ba?"
Cikin azama ta miƙe gami da daukar buta ban ɗaki ta nufa,sai da tayi tsarki kana ta fito baƙin rijiya ta zauna tayi alwala.
Bata ɗauki godon lokacin wajan sallah ba saboda rana yariga daga fara fitowa, bayan tayi sallama ta jima tana rokon Allah ya shiga lamarinta kana ta shafa, sannan ta ɗauki calbi ta fara azkar, sai da ta kwashe minti sama da ashirin tashafa kana ta miƙe zuwa ɗakin mama.
Da sallama ta shiga ɗakin, kasancewar mama tariga data idar da nata sallar hakan yasa ta masara a kwance, har ƙasa ta duƙa kamar yanda ta saba kullum gami da furta Inna kwana mama"Mama dake kwance fuskanta na kallo bango hakan yasa ta bawa Maimunatu baya.
Juyowa tayi gami da furta Maimunatu har kin tashi?"e" mama, ina kwana?"
Lafiya ƙlau, su ɗan jima suna hirarsu ta ɗa da mahaifi, cikin hiran tasu take tambayar yaushe Nana zata dawo?"
Au! na mance ban gaya maki ba, jiya mukai waya da innarki uwale shine take sanar dani da dawowar Nana.Cike dajin daɗi tace"yaushe tace dawo?"
Ina sha Allahu yau ƙinsan yau ne kasuwar jibiya....cike dajin daɗi Maimunatu tace"Allah ya kawosu lafiya, kana ta miƙe, ɗakin baba ta nufa, kasancewar bai dawo daga Masallaci ba hakan yasata fitowa, kici ta nufa taje ta haɗa duk wasu kwanukan da tasan anyi amfani dasu jiya takai gidin rijiya kana ta dawo ta share kici da tsakar gida gami da kintsa komai ta aje komai a mahallinsa.Har a lokacin mama na ɗaki kwance, tana cikin wanke-wanken kenan baba ya shigo, gani shigowarsa da sauri ta miƙe gami da cire hannu daga wanke-wanken da takeyi har ɗaki ta bishi, duƙawa tayi ta gaishesa.
Cike dajin daɗi ya amsa gami da tambayarta zancen jarabawar da suke shirin zanawa"Sati biyu ya rage mana mu zana.
Amma kina karatu ko?"
"E" tace"kana yayi mata addu'ar samu nasara sannan ta miƙe taje ta ƙarisa aikinta.Tana gamawa kicin ta dawo wuta ta hura, ragowar tuwon jiyan daya rage ta wanke kana ta yayyanka ta zuba su cikin tukunyar sannan ta ɗora akan wutan"sai a lokacin mama ta fito daga ɗaki, ba tare dataje ta gaida mijinta ba kici ta nufa gani Maimunatu ta gama duk wasu aiyukan daya kamata tayi yasata jawo kujeran mata ta zauna kusa da murhun.
Gani shigowar mama yasa Maimunatu mikewa daga kan kanfan da take zaune har ta juya zata fita daga kicin ɗin kenan mama ta kiranta, wajan zauna ta nuna mata.
Bude tukunyar tuwo dake wuta tayi, gani har ya fara zafi yasata meda murfin ta rufe,kwanto zaninta tayi kana ta kwance kullum dake hannu zainta Naira hamsin ta ciro, mikewa Maimunatu tayi gami da furta jeki gurin ya'u mai tireta ki siyomi gayen shayi ta ashirin suga ta talatin.
"To" Maimunatu tace gami da sanya hannu ta amshi kuɗin, ɗaki ta koma ta sanyo hijib kana taje ta siyo mata aiken nata.Tana dawowa miƙe mata tayi"yawwa yar albarka mama tace"kana ta umarce ta data ɗauko mata ƙarami tukunya wanda dama duk safe a ciki take dafa gayen shayin nata.
Gani tuwon na tausa yasa mama saukewa tukunyar miya ta daura shima yana tausa ta sauke kana ta ɗora ruwan gayen shayin nata.
Yana zafi ta juya cikin kofin da tuni ta tanada kana ta juye dukka sugar talatin ɗin ta fara juyawa, yanayi tana kurɓa,jin sigar ya maka raɗau yasata cewa"yawwa haka nake so, da wuya ya kasheni gwama daɗi ya kasheni.
Maimunatu dake tsaye ido kawai ta zubawa mamar tata gami da zancen zuci"kai wannan mata akwai shegon kwaɗayi" mama dake zaune umartan Maimunatu tayi data ɗauko mata kwano.
Manya-manyan yanka ta cire gami da zuba miya akai kana ta fara ci, ko wani ɓalli takai baki sai ta bishi da ruwan shayi, tanayi tana sosa kai ga uban zuba dake tsantsafowa sake jikinta, gani bazata iya jure kallo abin takaici ba tasa Maimunatu barin waje.
YOU ARE READING
🍒 KWAƊAYI DA BURI🍒
Fantasía🍒 KWAƊAYI DA BURI🍒labarin wata matace mai shegen kwaɗayi da buri, wanda hakan zai sa ta ɗau yarta ɗaya tilo taba da'ita aure ga wani attaji ba bare da da tayi binciken waye shi ba.ku biyoni domin jin cikakken labarin.