A yau lahadi,ita ce ta kama ranan da Nabil zai wuce Camp,wanda yayi mata waya tun jiya ya ke shaida mata zuwan sa don su yi sallama.
Tun bayan da ta tashi tayi sallar Asuba ta kasa komawa bacci,saboda damuwar tafiyar sa,ko kadan bata so suyi nesa da juna,don ba karamin sabo da shakuwar da suka yi,ya riga ya zama wani bangare na jikin ta, wanda rabuwa da shi abu ne mutukar wahala,sati ukun da zai yi gani take kamar shekara zai yi a can.
Duk da ya fada mata irin cuku cukun ta yayi don ganin an bar shi a Kaduna,domin shima baya so yayi nesa da ita,amma abun bai yiwu ba,sai dai wanda ya sa yayi masa abun,yayi masa alkawarin service dinsa a Kadunan zai yi,shi ya sa hankulan ya dan kwanta,tunda wancan kusan shekara ne baza su so sake yin ni sa da juna ba.
Kasancewar weekend ne,su Dady basa tashi da wuri,ya sa ita ma ba ta yi saurin hada breakfast ba,bayan tayi wanka,sai ta saka yar doguwar riga mara nauyi,ta koma ta kwanta a kan gado jiki a mace.
Karar ringing tone din daya shigo wayar ta ce ta sata sakin dan murmushin jin dadi,tunda ta san wanda yake kiran,kallo agogo tayi taga har tara yayi kamar yadda ya fada mata zai ison,mamakin yadda har lokaci ya tafi ta shiga yi,kafin ta dauki kiran cikin sanyin jiki,yake shaida mata ya iso yana falo,ta amsa shi da gata nan sakkowa.
Hijab din da tai sallah da shi dake kusa da ita ta janyo,ta saka,kana ta dauki turare mai sanyin kamshi ta fesa a jikin ta,sannan ta fice,cike da murna ganin sa,tare da bakin cikin rabuwan da zasu yi na satuka.
A hankali take taka matakallar har ta karaso falon,inda ta hango shi zaune kan 1 sitter din kujerun dake falon,sanye yake da sweat pant a jiki kalar ash,sai blue din mai karamin hannu,duk da simple dressing yayi,ya mata kyau sosai.
A haka ta karaso tare dayi masa sallama da siriryar muryan ta,amsawa yayi yana sakar mata murmushi da ke narkar mata da zuciya,ita ma ta maida masa martani,kana suka sake gaisawa,ta samu kujeran da ke gefen sa ta zauna,idanu ya zuba mata ido yana kallan ta kafin ya
"My life kin ko san yadda hijabi yake miki kyau kuwa?
Dan murmushi tayi tana sunne kai,kana ta ce
"A a"
Ya ce "please ki rika samun often shi saboda ba karamin fito min da kyanki yake yi ba"
A kunyace tace "Na gode,insha Allah zan rinka saka maka"
Murmushin gamsuwa yayi da amsar ta,sannan ya ce "Ai ni ke da godiya,tunda ni za a saka ma wa"
Shiru ce ta biyo baya kafin ta cije t sake fadin
"Yanzu My Hearty in ka tafi sai na yi satuka ban ganka ba kena"sai ga hawaye,wanda take ta makale su tun dazu
Ganin hawayen ta ne ya tada mishi hankali yana jin saukar sa tana taba masa zuciya
Dan matsowa yayi in da take zaune ya marairaice murya,kamar zai yi kukan shima kafin ya ce
"Don girman Allah ki daina wannan kuka,meyasa My life zaki rinka min asarar hawayen ki masu tsada?wallahi kema kin san ba a son raina zan yi tafiyar nan ba,sai dai abu ne daya zama dole,da babu inda zan je balle nayi nisa da ke,plss ki barr ni na tafi ina tunawa da beautiful smiley face dinki ba Crying face in ki ba"ya fada yana mai da fuskar sa irin ta masu kuka
Ai bata san sanda ta saki dan dariya ba har dimples din ta na lotsawa,haka yake,ko yaya ne ya gan ta cikin damuwa sai ya san yadda yayi ya kawar mata da shi wajen sa ta farin ciki .
Shi ko shagala yayi wajen kallan ta,ganin kyan da ta kara yi masa,ya san duk ranan daya data zama matar sa,yana daya daga cikin mazaje masu sa a a rayuwa.
Kafin ya ce"Yauwa!Toh ko kefa,yadda na tafi na barki kina dariya haka nake so na dawo na tarar da ke cikin farin ciki,domin ta haka ne kadai hankali na zai iya kwanciya kin ji"ya fada yana langwabe kai irin na mai lallashi
YOU ARE READING
K'ADDARA TA
RomanceBanko kofar dakin ta yi a fusace,dole yau ayi wacce za a yi a kare tsaknin ta da shi,hakimce a zaune ta same shi ya bama kofa baya daga shi sai boxers,ba riga sai karfaffn jikin sa d ke a murde,macbook pro na a gaba shi abnda ta hango a ciki screen...