💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO*📖
'''®Ɗaya tamkar da Dubu'''💪✓*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_.
*EPISODE Forty Four*
Yana sake koma wa wajen ta ya ga alamun ta sake sume wa, juya wa kawai yayi ya sake ɗibo ruwa ya watsa mata
Hakan yasa ta farfaɗo numfashin ta ya dawo, sai dai idanun ta suna rufe ta kasa buɗe wa, illa kuka da take yi ƙasa-ƙasa tana riƙe da kanta, sai faman rawan sanyi take yi haƙoran ta na karkarwa
Ko kaɗan ba ya jin zai iya taimaka mata saboda zallan tsanar ta da yake ji a ransa, juya wa ya sake yi ya koma ɗakin sa, magani ya ɗauko mata ya zo ya jefa mata, cikin kausashshiyar murya da zaka gane yana a cikin ɓacin rai, wanda daƙyar ma maganar take fita yace da ita, "ki gaggauta tashi ki gyara min gida. Kar in dawo na ga baki gyara nan wajen ba, kar na dawo baki cire min ƙazantar nan naki ba na maimaita miki.. "sai yayi shiru yana juya wa ya yi waje ya fice
Ɗahira bata motsa ba tana nan yanda ya bar ta, illa kuka da take tayi, sosai take kukan har da su shashsheƙa, ta rasa meyasa Usman ya tsane ta, mene ne tayi masa a rayuwa da yake nuna mata wannan zazzafan tsanar? Tana a cikin halin mutuwa ko rayuwa amma shi ko kaɗan ba ya tausayin ta, shin yaushe ne zai tausaya mata? Har yaushe ne zata fita a cikin wannan uƙuban nashi? Me yake nufi da ita ne? Idan so yake yi ya kashe ta meyasa bazai kashe ta a lokaci ɗaya ba sai ya gana mata azaba haka? Ba ta jin zata iya yafe wa Bawan Allan nan, har ABADA! Baza ta taɓa yafe mishi ba domin ya cutar da ita.
Ta shafe fiye da awanni uku bata iya motsa wa daga inda take ba, sabida ko kaɗan bata da ƙwarin jiki, ga tsananin ciwon da take fama dashi, amma don kar ya dawo ta fuskanci wulaƙancin sa, tana kuka ta yunƙura ta tashi daƙyar, jikin ta gaba ɗaya ya tsume sai karo da haƙori take yi tana ƙanƙame jiki, hawayen nata ma sun kafe illa kukan zuci kawai da take yi, daƙyar da jan jiki ta isa Fridge ta sanya hannu ta buɗe ta ɗauki ruwa, maganin da ya ajiye mata ta ɗauka tasha ko don wai zata samu sauƙin ciwon da take fama dashi, sai ta sake rarrafa wa ta isa inda gaba ɗaya ruwa ne sharkaf da aman ta a wajen, kallon wajen take yi tana tunanin ta ina zata fara, baza ta taɓa iya wa ba saboda zazzaɓin da take fama dashi, daga ƙarshe zube wa tayi nan ta dinga sheƙa wani aman, ga tsananin yunwa dake addabar ta, jikin ta sai faman rawa yake yi, majinu na tsiyaya ta hancin ta
Sake rarrafa wa tayi ta kwaɓe kayan jikin ta gaba ɗaya, ta sauya wani rigan daƙyar, rufe kanta tayi ta ƙudundune tana ci gaba da rawan sanyi, gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi ta rasa inda zata saka kanta, addu'a kawai take yi a ranta Allah ya kawo mata mafita, tunda take bata taɓa shan wahala makamanciyar irin ta yau ba. Runtse idanun ta tayi tare da tamke bakin ta zuciyar ta na ƙuna, duk second ɗaya tsanar Usman na sake ruruwa a ranta, tana jin har abada baza ta taɓa yafe masa ba, sai Allah ya saka mata.
Wasa-wasa har dare Ɗahira tana cikin wannan mawuyacin halin, ta kasa taɓuka komi, a haka ta wuni zurr komi bata saka a cikin ta ba, ta kasa ma tashi bare ta samu abinda zata saka a cikin ta, tana jin sai dai ya kashe ta domin baza ta iya yin komi ba.
YOU ARE READING
DOCTOR'S FAMILY
FantastikFamily ne me cike da abun mamaki, gaba ɗayan su sun kasance DOCTORS ne, Rayuwar Ɗahira da Usman waɗanda suka kasance cikin Familyn, sun kasance maƙiyan juna, inda ƙaddara ta zo ta haɗa su aure, suna zama ne tamkar za su kashe juna don ƙiyayya, ya ts...