part titee five

109 11 2
                                    

🌹🌿🌹🌿🌹
     🌿🌹🌿🌹
          🌹🌿🌹
               🌿🌹
                    🌹

🌿 *TAWAKKALI*
🌿
( _Labarin Nooriya da mijin yayarta_)

🌹
🌿🌹
🌹🌿🌹
🌿🌹🌿🌹
🌹🌿🌹🌿🌹

Page 8️⃣0️⃣8️⃣1️⃣to8️⃣2️⃣8️⃣3️⃣

WRITTEN BY
🌹 *AMINA UMAR FARUQ* 🌹
  _Kwantagora_

Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN*
and now
*TAWAKKALI*

_SADAUKARWA GA_
*Aminiyata NAFEESA HUSSAINI Ina rokon ALLAH yajikanta yaimata rahama amin🤲ya rabbi*

Wattpad AminaUmarF

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

   *_PEN: WRITER'S  ASSOCIATION ©_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

       
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________

https://mobile.facebook.com/Pen-Writers-Association-100990022185172

✍🏽Typing

_Bismillahirrahamnirraheem_

*"Noor!* *Noor!!* *Noor!!!* subhanallahi! bata motsaba balle tafarka, cike da tashin hankali haɗe da tsantsan tsoro yasake kiranta still no response, da alama *Noor* kam tayi nisa...

cikin tsantsan tashin hankali yashare wani gumi da yatsatsufo mashi agoshi, tareda furta ya ilahil'alamina! ya mujibussalihina!!.

"Ya ALLAH!!! banyi wannan abin dan na cutawa wannan "baiwar takaba nayine dan samun kusanci da'ita", domin raya sunnar ma'aikinka ya mujibudda'awati ina rokonka kar kasa wani abin yasameta ya ALLAH ameen....

"Sai kuma yaɗaga kai da sauri yakalli magen nan, wacce taƙura mashi jajayen idonta masu mugun ban tsoro, musamman ga wanda yake tsoronta sosai take kallon shi kamar zatace mashi kai! miƙo mun ita na yagalgalata, wani mugun harara yawatsa mata tareda kallon gefenshi,

aikam yai arba da wasu baƙaƙen kwabashun takalman shi daya cire, da sauri yaɗauka cikin mahaukaciya zafin nama yakai mata wani irin mugun jifan,

da saida tabugi marfin ƙofar ɗakin tareda sakin wani ƙara azaba sannan ta zube ƙasa ba motsi da alama itama tasumane, cike da ɓacin rai yace banza shegiya nace akawo mun kenan dan kiyimun gyara ba ɓarna ba.

"Sannan yamaida kallonshi ga *Noor* datake wance magashiya, da sauri yaɗagata tareda ɗaukarta yakwantar da'ita" akan bed sannan yaɓude wani ɗan ƙaramin firjin dake gefe gadon , yaɗauko ruwa agora me tsananin sanyi yabuɗe jikinshi yana rawa ya yayyafa mata,

take taja dogon ajiyar zuciya
can saita buɗe ido ahankali tafara kallon ɗakin, sannu ahankali ta tunada abinda yafaru dai-dai lokacin da idonta yasauka akan magen da kusan tare suka farfaɗo, sai kuka take meyau! meyau!! meyau!!!..

"Aikam tayi zumbur tamiƙe da sauri yariƙeta tareda rungumeta aƙirjin shi, cike da tsananin tsoro jikinta yana azababben kerrrrma ta ƙwaƙume shi sosai, wanda akaro nafarƙo datayi hakan tana me faɗin...

wayyo ALLAH na yah *Naseer* mage CE gatanan ta biyuni zata kamani wayyo dan ALLAH karka bari takama ni, inajin tsoron ta sosai kaji?...taƙarashe faɗin dasakin kuka me cike da tsantsan tsoro jikinta kuwa sai mugun rawa yakeyi, gawani gumi dayake tsatsufo mata tako'ina ajikita.

TAWAKKALI labarin nooriya da mijin yayarta labarine me taɓa zuciyaWhere stories live. Discover now