*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_
Email-Karamciwritersass@gmail.comVisit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb
_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_
'''Shafi na 14'''
Ɗagowa yayi ya kalleta, itama kallon sa take idanunta cike da wasu hawayen. "Ƴar ka ta rasu yau, amma kallo kake abinka" juyawa tayi tana hawaye da sauri ya tashi ya biyota, tarar gabanta yayi sannan ta tsaya. "Karki saka wani tunanin a ranki Falmata, na kasa bacci shiyasa na kunna kallo dan in rage damuwa. Ta gefensa kawai ta wuce, ta nufi part ɗinta ta kira su Aunty Yana.
A yanda ta bar Jannat haka suka sameta. "Ko kaita asibiti zamuyi?" Mommy ta faɗa a ruɗe "A'a samo min ruwa kawai ki gani, a samo min mai sanyi." cewar Aunty Yana. Da sauri Mommy ta nufi fridge ɗin ɗakin ta ɗauko gorar ruwa mai sanyi ta kawo. Buɗewa Aunty Yana tayi ta zuba ruwan a hannunta sannan ta shafa a fuskar Jannat. Ajiyar zuciya mai nauyi Jannat ta sauke.
Khalil yana kwance a gado sai dai idanunsa biyu ya kasa ko da gyangyaɗi bare ya runtsa. Tashi zaune yayi ya saka pillow a bayanshi ya lula duniyar tunani. _To waye ya yiwa Jannat fyaɗe da har za ta kamu da cutar yoyon fitsari?_ shine abinda ya furta a ransa. _Fyaɗe ko Haihuwa sune suke haddasa yoyon fitsari, kenan Jannat fyaɗe akayi mata? To waye yayi mata?_ kan shi ya sake dafe wa da hannu. _Ahmad yayiwa Jannat fyaɗe kuma ta sani ko Safina ta sani, gudun kar asirin sa ya tonu shiyasa ya gudu ya bar garin ko ƙasar._ a firgice ya dira daga gadon lokacin da zuciyarta ta furta masa hakan. "Ya Allah ka sassautawa Jannat, baiwarka ce mai haƙuri, tausayi gami da kawaici" fridge ya nufa ya buɗe ya ɗauki ruwa mai sanyi, a gurin ya shanye ya yarda robar. "Ba zan taɓa bari a cutar da Jannat ba nayi alƙawarin sai na ƙwato mata haƙƙinta gurin duk wanda ya zalunceta"
Cikin kuka ta rike hannun Aunty Yana gam. Mommy ta zauna kusa da ita. "Jannat..." ta ambaci sunanta sannan ta saka kuka. Aunty Yana ta hau nasiha "Idan kina kuka ai zaki ƙara karya mata zuciya itama" "Da asuba zamu tafi asibiti kawai, bana son rasata, kina gani har yanzu bata dawo dai-dai ba ko magana fa batayi" Mommy ta ƙarasa maganar tana hawaye. "Ki kira likita yazo ya duba ta anan kafin a shafe makoki mu kaita asibiti." kai kawai Mommy ta gyaɗa.
Ana fitowa daga masallaci ta kira Doctor gida. Ya zo kuma ya shiga ya duba Jannat ɗin, idanunta a buɗe ta kafesu guri guda amma ba um ba um-um. Bayan ya gama auna ta ya kallesu ya ce "Tana fama da matsala ta damuwa da yawan tunani, kuma hakan zai iya sakawa ta zauce ta rasa tunaninta, domin jininta ya hau sosai Dan haka ku kiyaye ku riƙa yin duk wani abu da zai sanyaya mata zuciya" "To ai ka ga ƴar uwarta ce ta rasu dole dama ta shiga damuwa haka" Likita yayi ajiyar ya ce "Tun farko ma da ba'a faɗa mata ba, saboda wannan matsalar ta ta, ga hawan jini tana dashi at her age da bai kamata ace tana da damuwar da har zai iya haddasa mata ciwo kamar hawan jini" sai lokacin Mommy ta ce "Ba mu da yadda muka iya ne, wani sa'in damuwa ita take tunkararka ba kaine kake tunkararta ba, amma dai in sha Allah zamu kiyaye abubuwan da ka faɗa" "To Hajiya Allah ya bata lafiya, idan da hali a daina gaisuwa a gabanta dan zai iya ɗaga mata hankali" "In sha Allahu, mun gode."
*****
A hankali yake driving cikin nutsuwa, kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar da yana cikin damuwa. Tun daya shiga layin gidan ya hango canopy har huɗu kuma ko wanne cike da mutane zaune akan carpets da aka shinfaɗa. "Allahu Akbar, dagaske dai Safina bata rayuwa, Allah yayi miki rahama yasa ke ƴar aljanna ce."

YOU ARE READING
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Historical FictionGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...