*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_
Email-Karamciwritersass@gmail.comVisit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb
_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_
*Not Edited*
Ƴan Wattpad dan Allah idan kun karanta littafi ko da ba zakuyi comment ba ku riƙa Vote please
'''Shafi na 15'''
*Bayan Sati Biyu*
Jannat na kwance akan gado tana latsa wayarta Mommy ta shigo. "Jannat baki gajiya da danna waya?" "Mommy ina so in samu abinda zai rage min kewa, ina tunani ne har yanzu, shiyasa kawai nake shiga nayi game" "Hakan yayi in dai zai faranta miki to Alhamdulillah" tashi tayi zaune, Mommy ta kai dubanda zuwa ledar fitsarin da zaren ya sauka tana ƙasa har ta kusa cika. "Mommy ya akai Safina ta rasu?" ta faɗa tana ƙara goge waye da ya fara zuba daga idanunta. "Jannat dan Allah ki bari ki warware sai mu yi wannan maganar" "Ya Ahmad ban gan shi ba, haka Sa'ad da ƴan gidansu ba a faɗa min ko sun zo ba, yau kwana sha huɗu da rasuwar Safina" "Kan su sukayi wa, amma ni bana so ki damu dan basu zo haba" "Haba Mommy damuwa ya zama dole, musamman Sa'ad ina son ganin shi Mommy" "Yanzu dai ba wannan ba, ki tashi muje Daddynku yana son ganinki, Farhan da Mijinta ma sun zo" "Mommy tazo shine bata nemeni ba?" "To ai kiran Daddy ne na san tana zuwa falon shi suka nufa" a hankali ta tashi ta shiga toilet ta gyara jikinta ta cire zanin daya ɓaci da fitsari, kafin ta fito kuma Mommy ta naɗe bedsheet ɗin ta shimfiɗa wani. Tana fitowa Mommy ta saka mata hijab sannan ta riƙe hannunta suka tafi.
Suna shiga ɗakin da Khalil ta fara haɗa ido, gabanta taji ya faɗi kawai hakanan taji duk ta takura. Zama tayi ƙasan carpet kusa da Farhan taga Farhan ta ɗan masa, sai duk taji babu daɗi, kawai tashi tayi ta koma ƙasa kujerar da Mommy ke zaune ta zauna.
Daddy ya kalleta ya ce "Baki ga mutane ba, meyasa baki gaida Khalil ba" bata ɗaga ido ba kawai ta gaida shi ya amsa cikin sakin fuska.
"Jannat...!" da kakkausar murya Daddy ya kira sunanta ta ɗago ta kalleshi. "Waye yayi miki fyaɗe?" gabanta taji yayi mummunar faɗuwa, ta kasa ɗaga kanta ta kalli Daddy. "Magana nake miki" ya furta cikin faɗa. Ta ɗan zabura tare da riƙe ƙafafun Mommy ta fara kuka. "Ai ba kuka za kiyi ba, faɗa mana za kiyi dan muji abinyi." jikinta gaba ɗaya karkarwa yake. "Zan...za..zan faɗawa...Mom...Mommy" "Ba Mommy zaki faɗawa ba ni mahaifinki za ki faɗawa" Sai a lokacin Mommy ta ce "Ka bar ta ta faɗa min sai na faɗa maka, likita ya ce a daina mata hayaniya" "Babu ruwana da wani likita duk abinda ya sameta ita ta jawa kanta ta jawa ƴar uwarta mutuwa" Cikin faɗa Mommy ta ce "Ta ya ya ta zama silar mutuwar ƴar uwarta?" "Saboda taje an mata fyaɗe ita kuma tana jinyar ta mota ta kaɗeta" "To kuma shine ya zama laifin Jannat? Kai baka ga laifin korar da kayi mata shine silar faruwar haka ba" "ki daina min shouting akan gaskiyar da nake faɗa" miƙewa tayi tsaye tana faɗin "Wannan ba gaskiya bane ka faɗi son ranka ne kawai, duk abinda ya sameta kai ne ka jawo saboda bakin ka baya faɗar alkhairi a kanta, na ƙara tabbatar da cewa baka ƙaunarta" "Oh yanzu faɗa da nake wa ƴaƴana shine ya zama rashin ƙauna" "Ƙwarai kuwa wannan ba komai bane face tsantsar ƙiyayya" Hajiya Bilki sai a lokaci ta taso ta riƙe Mommy tana bata haƙuri kan ta zauna. Jannat kuwa kuka take sosai yayinda Farhan da Khalil kansu ke ƙasa.
Shiru ne ya biyo baya bayan Mommy ta haƙura ta zauna. "Jannat waye ya miki fyaɗe ina tambayarki a karo na biyu kafin ki hasalani" Cikin kuka ta ce "Daddy na tuba na bi Allah na bi ku, Daddy ban san abinda na aikata ya kai ƙololuwa da zan fuskanci irin wannan hukuncin ba, wallahi Daddy ni na san bakin ka ne ya kamani, kayi haƙuri dan Allah" tana gama faɗa ta miƙe sa sauri ta bar ɗakin tana shashsheƙar kuka.
Mommy ta kalli Daddy ta ce "Ka zauna kayi tunani kuma ka tuntuɓi Malamai kaji shin ba bakinka bane yake kama ƴaƴanka, a wannan karon ba zan taɓa bari ƴa ta da ta rage ta salwanta ba" ta share hawaye cikin takaici ta ce "Ka hana ƴan uwana su tafi da ita su nema mata magani, kuma ka zo nan kana ta ƙara aibatata, zan ɗauke ta mu tafi ba zan sake dawowa ba, dan haka ina buƙatar takardar saki daga gareka." juyowa tayi ta tafi har ta fita babu wanda ya iya magana.
"Alhaji dan Allah ka bi ta ka bata haƙuri" "Haƙuri fa kika ce? Ni da aka wa laifi kuma nine zan bayar da haƙuri" "Ai baka faɗi ba ita matarka ita kuma ƴarka dan Allah kaje, na san Hajiya Falmata haƙurinta ne ya ƙare kuma ta kasa jurewa ne" "Kamar yadda take ganin tana da iko da Jannat haka nima, sannan yadda take jin tana son Jannat bata fi ni son ta ba" "Safina ko arba'in batayi ba, dole akwai zafin hakan a tattare da ita" "Ni babu abinda zan iya akan hakan, nayi iya bakin ƙoƙarina ta nuna ban isa da Jannat ba" Sai lokacin Khalil ya ce "Daddy dan Allah kayi haƙuri kan abinda ya faru, ni ka bani dama zan lallaɓa Jannat a hankali har ta faɗa min wanda yayi mata, amma idan aka ce za a bita da zafi to za taji tsoron faɗa" "Shikenan kaje ka same su kayi musu maganar. Tashi yayi ya fita Farhan da saurin ta tashi tana ƙoƙarin bin sa Daddy ya dakatar da ita.
Kuka sosai take kamar ranta zai fita, ita kuma Mommy tana ta haɗa kayansu a trolley, knocking Khalil yake tayi amma sam taƙi ta buɗe ƙofar haka ya gaji ya juya.
A nan falon Daddy inda ya bar su anan ya samesu. Zama yayi gefe ya ce "Daddy a yanzu suna cikin damuwa amma a hankali za a bi abin dan Allah ka sanyaya zuciyarka" "Ba damuwa Khalil, kaima Allah yayi maka albarka" "Amin Daddy" Jin horn na mota ne ya saka Daddy tashi ya leƙa sai gani yayi motar Mommy ta fita daga gidan. Da sauri ya fuzgi key ɗin mota ya fita, duk suka miƙe suna ta alhini.
Kafin ta fita daga layin yayi saurin tarar gabanta, aikuwa da sauri taja burki ta tsaya.
Fitowa yayi ya ƙarasa jikin motar tasu, ta sauke glass. "Falmata ban san meyasa kike ƙoƙarin yanke hukunci ba" "Saboda ina son ƴata ta tsira da rai" "Amma shikenan bani da damar hukunta ƴaƴana?" "Kana dashi, kuma a baya ma na baka wannan damar, amma a yanzu Jannat na cikin mawuyacin hali tana kuma buƙatar medication dan haka zamu tafi asibitin masu yoyon fitsari idan ta warke ko wace magana sai ayi" "Wane asibiti zaku je?" "Za muje wanda yake a triumph na san dai gado zamu bamu" "To shikenan zamuje daga baya Allah ya bata lafiya" kallon Daddy ta ƙarayi dan tayi mamakin addu'ar da yayiwa Jannat, sai taji tausayinsa ya kamata sosai. A hankali ta furta amin. Jannat kuwa har lokacin kan ta yana ƙasa tana sharar hawaye sam bata ɗago ba. Komawa yayi ya janye motar sa suka wuce.
*2 Days Later*
Farhan na zaune kan kujera hannunta riƙe da glass cup cike da lemo tana kurɓa idanunta akan plazma. Daga bedroom ya fito ya zauna kan kujerar kusa da ita. Da sauri ta miƙe tana haɗe rai za ta bar wajen. "Amma ina ganin hakan kamar ba shine maslaha ba" "Kai ka ga haka" "Kema kin gani domin hakan da kike sam babu dacewa" dawowa tayi ta tsaya a gabanshi tare da kama ƙugu "Kai abinda kake ya dace? Ai ni kake aure ba Jannat ba" "Amma Jannat ai ƴar uwarki ce kuma idan nayi mata kamar nayi miki ne" "A'a a'a sam ba haka bane a ranka, duk abinda kake kanayi ne a matsayinta na tsohuwar budurwarka" kallonta yayi cike da mamaki "Yanzu Farhan kike faɗin maganar nan da bakinki, kada ki manta Jannat jininki ce" "Ta ɓangaren Daddy ba" ta murguɗa baki kawai ta wuce "Turƙashi" ya faɗa tare da sauke ajiyar zuciya.
Tana kwance a gadon asibitin daga gefenta wata mata ce tana riƙe da hannayenta gam saboda matsanancin ciwon mara da take. Likita da niurse guda biyu suna tsaye a kanta tana ta ni shi sama-sama. Jannat dake zaune idonta na kansu. Bayan likita da nurses sun tafi Jannat ɗin ta sauka daga gadon a hankali ta zira silifas ta ɗauki ledar fitsarinta ta ƙarasa jikin gadon nasu.
"Sannu, Allah ya bamu lafiya" Matar ta ɗago kai ta kalli Jannat ta ce "Amin ya rabbi, ke ai naki da sauƙi" "Eh to da sauƙi zan ce dana ga ta fini shan wahala, amma ciwon a zuci da ban ne, tunda ni nawa fyaɗe ne nata kuma haihuwa ne" "Kenan fyaɗe akayi miki kika kamu da wannan ciwo" "Itama kusan haka ne banbancinku shine ita har sai da ɗauki juna biyu" turo ƙofar da aka yi ne ya saka ta yi shiru. Ganin Mommy ce ya saka ta koma kan gadonta.
"Kin san likita ya ce ki daina yawo ko?" "Eh Mommy ai ba fita nayi ba" "To yanzu dai ga abinci zauna ki ci" "Allah yasa ba daga gida ya fito ba" "Daga nan ne, lafiya?" "Mommy na tsani Daddy dan haka bazan ci duk abinci da yazo daga gare shi ba." Mommy bata san lokacin data ɗaga hannu ta tsinkawa Jannat mari.....
Next page.....✍️
#Follow
#Vote
#Comment
#Share

VOUS LISEZ
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Fiction HistoriqueGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...