*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_
Email-Karamciwritersass@gmail.comVisit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb
_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_
'''Shafi na 16'''
Riƙe kumatu tayi ta ƙurawa Mommy ido tana cije leɓe. Matar da ke jinyar ɗayan gadon ta fara bawa Mommy haƙuri, cikin ɓacin rai Mommy ta ce "Ai tana da hankali sai ance ga abinda za tayi ko ga abinda za ta ƙi yi" "Sai haƙuri yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halinsa ba" "Hakane amma ai ta san daidai" "Kiyi haƙuri dan Allah, tunda yanzu bata da lafiya ma" "Shikenan" Mommy ta faɗa sannan ta kalli Jannat dake tsaye tana hawaye. Har za ta mata magana sai ta fasa kawai ta juya baya. "Kiyi haƙuri Mommy" ta faɗa tana share hawaye. "Zauna muyi magana" zama tayi a hankali sannan ta sauke ƙwayar idon ta ƙasa.
Sai da Mommy ta karanci fuskarta na ɗan lokaci sannan ta ce "Jannat duk abinda mahaifinki yayi miki sunansa ba zai taɓa canzawa daga mahaifi ba, ki yi haƙuri kuma ki manta komai" riƙe Mommy tayi gam tana kuka tana shashsheƙa ta ce "Mommy ki gafarceni, amma bana son Daddy bana ƙaunarsa, komai ya faru dani shine sanadi, dan Allah ki daina yi min maganarsa ki daina please" sosai take kuka Mommy tana shafa bayanta ta kasa cewa komai. Sai da tayi kuka mai isarta sannan ta ɗago rinannun idanunta ta kalli Mommy "Ko mutuwa nayi kada akai gawata gidan mahaifina, alƙawari na ɗaukarwa kaina ba zan koma gare shi ba, gara na mutu ina garari." Mommy kasa ɓoye hawayenta tayi, yana fitowa ta saka hannu ta goge. Matar dake gefe tana jin su ta taso ta zauna daga ɗayan ɓangaren. Dafa Jannat tayi ta ce "Abinda mahaifiyarki ta faɗa gaskiya ne, kada ki ce zaki guji mahaifinki akan duk wani laifi da yayi miki, shine silar zuwanki duniya, kuma saɓa masa babban haɗari ne, idan ya miki laifin da ba za ki iya jurewa ba, ki kai shi ƙara wajen wanda kika ga sun isa da shi, amma ki ce za ki guje shi ko kuma kice zaki bar gidan mahaifinki, to za ki ƙara jefa rayuwarki a haɗari"
kallon ta Jannat tayi cikin kuka ta ce "Idanuna sun rufe bazan taɓa iya ɗaukar shawararki ba, nayi hakan da farko amma bata amfaneni ba, duk da haka nagode maki, nagode sosai."
******
"Ba daidai bane abinda ka aikata ga ƴaƴanka, ka auna maganar a mizani, tun tuni nake faɗa maka ka daina furta mummunan kalami akan ƴaƴanka" Ummu ce ke faɗar maganar a falon Daddy, shi kuma yana zaune ya kasa cewa komai.
"Magana nake maka amma kayi shiru" "Astagfirulla!" ya furta sannan ya sauke ajiyar zuciya. "Kina nufin duk abinda ya faru nine sila?" gyaɗa kai tayi ta ce "Ko shakka babu, lokacin da ka kori Jannat ai na faɗa maka bai kamata ka koreta ba, bama korar ce illa ba, ka hana kowa a danginka ya karɓeta, sannan ka san family ɗin mahaifiyarta ba ƴan nan bane, ina Jannat za taje? Sannan ƴar uwarta ta ɗauke ta ta kaita gidanta amma ka buɗe baki kace tunda ta ɗauketa itama za ta gani. Idan ka haɗa maganar ka kuma auna ka mata kyakykyawan kallo zaka tabbatar da cewa bakinka ne ya kama ƴaƴanka" "Taya kenan?" "Ta yadda na faɗa mana, kace Jannat za ta gani kuma ka ƙara maimaita kalmar ga Safina, mijin Safina yayiwa Jannat fyaɗe ta kamu da yoyon fitsari, yayinda takaici ya saka Safina tayi loosing control ta fita bata cikin hayyacinta mota ta bugeta, ka duba maganata sosai ka gani wannan illar furucin ka ne ya jawo hakan"
Miƙewa Daddy yayi tare da faɗin "Kina nufin Ahmad shine yayiwa ƴata fyaɗe?" ganin Daddy ya ruɗe ya saka Ummu tashi ta ɗauko ruwa mai sanyi a fridge ta tsiyaya a cup ta miƙa masa. Karɓa yayi a take ya shanye ya dire kofin. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Babu ko shakka akan abinda na faɗa, Ahmad har yau baya gari kuma ba'a san inda yake ba, kuma daga Safina har Jannat ba yaƙi wanda ya faɗi abinda ya faru" Dafe kai Daddy yayi tare da faɗin "Na tafka babban kuskure, nayi haka ne dan in hukunta Jannat amma ba dan na tsaneta ba kamar yadda Falmata take tunani, ban taɓa tunanin abin zai kai ga haka ba" "Tabbas kayi kuskure, wannan shi ake kira da illar furuci, abu ɗaya zakayi a yanzu shine kaja Jannat a jiki, ka aura mata wanda take so, sannan ka nemo Ahmad ka hukuntashi" shiru Daddy yayi na wasu lokutan dan kan shi yaji na sara masa.
Ɗago idanu yayi ya kalli Ummu ya ce "Idan har Ahmad ne ya lalatawa Jannat rayuwa, sai....sai....." tari ne ya sarƙe masa, da sauri Ummu ta riƙesa lokacin tuni ya zube a ƙasa ya suma.
*Hospital*
Rayyan na tsaye jikin gadon, Ummu na daga gefe, yayinda Likita yake tsaye yana rubutu a cikin file kafin ya bawa Rayyan takarda. Karɓa yayi yana dubawa Likitan ya ƙara da faɗin "Kaje pharmacy ka karɓo, magunguna ne da drip da za a sanya idan wannan ya ƙare" "Okay" "Jininsa ya hau yana buƙatar hutu sosai, ko da ya farka kar ayi hayaniya da yawa a gaban shi" "In sha Allahu" Ummu ta faɗa idanunta akan Daddy. Likita na fita ta mayar da kallonta ga Rayyan "Nagode sosai, ba dan na ganka ba, da ban san waye zai kawo shi asibiti" zai yi magana aka turo ƙofar aka shigo. Farhan da Khalil ne, da sauri Farhan ta ƙarasa gaban Ummu ta rungumeta ta fara kuka. "Kiyi haƙuri kin san baki da lafiya dai" Khalil ya miƙawa Rayyan hannu sukayi musabaha, dan Rayyan ya gane shi sosai saboda abinda ya faru wajen ɗaurin aure. "Ummu mene ya samu Daddy?" Farhan ta faɗa tana hawaye. "Da sauƙi ma a yanzu. Jininsa ne ya hau, amma Alhamdulillah ya fara sauka ma, sai dai Likita ya ce kar ayi hayaniya a kansa"
Khalil ya ƙarasa suka gaisa da Ummu, ya kalli gadon da Daddgy ke kwance "Amma meya jawo hakan?" "Akan case ɗin Jannat dai" a fusace Farhan ta ce "Wai Jannat so take ta kashe Daddy" "Kin ga bata da wani laifi, sai dai in ni za ki yiwa faɗan ina so na kashe shi, Jannat da take gadon asibiti, bata ma san me yake faruwa ba"
Gaban Rayyan ya faɗi sosai _Mene ya samu Jannat ɗin bayan barinta da gidansu?_ ya furta a ransa. "Amma Ummu tunda kin san abin na ɗaga masa hankali ki daina maganar zai fi" Farhan ta faɗa idanunta akan Ummu. "Idan kika ce haka kuwa kin zama butulu, duk irin ƙaunar da Jannat ke maki amma kice kar a taso da magana, shikenan abinda aka mata anci bulus kenan?" "Amma Ummu ni kaina a yanzu na yarda duk abinda Daddy yayiwa Jannat laifinta ne" cikin ɓacin rai Umma ta ce "To shima mahaifin naku nadamar abinda yayi mata ne ya saka jininsa ya hau, me Jannat tayi miki Farhan?" juyar da kai Farhan tayi tana zuɓurar baki.
Ummu ta kalli Khalil ta ce "Ka ga ɗauki matarka ku tafi, da na san haka za ta zo tana faɗa ai da ban ma gayyato ta ba, da nace karka faɗa mata" murmushin yaƙe yayi ya ce "A'a Ummu ba haka bane, yanzu dai ina magunguna da aka sayo" sai a lokacin ta ce "Yau na manta muna ta surutu, wannan ɗan maƙocinmu ne" Farhan da Khalil suka kalli Rayyan dake tsaye. Ummu ta cigaba da faɗin "Lokacin da Alhaji ya faɗi. Na fito da hanzari na duba driver baya kusa, ni kuma ban iya driving ba, na kira driver wayar shi a kashe, ina fita dan na samu wani sai Allah ya sa na ganshi yana ƙoƙarin shigar da mota gida na roƙe shi ya kawo mu, da alamu ma daga wajen aiki yake"
Kallon shi sukayi suka ce "Mun gode Allah ya saka da alkhairi" ɗan lumshe manyan idanunsa yayi sannan ya buɗe, da alama hakam ya zame masa jiki "Karku damu ai duk yi wa kaine" "Takardar magani tana hannunsa, Khalil ka raka shi ku karɓo" "A'a ba damuwa bari na karɓo" Khalil zai yi saurin cewa "Karka damu muje tare."
*****Suna zaune a falo, an ajje masu abinci da kayan ciye-ciye, ita da ƙawarta ne suka zo, duk ta kasa sakewa. Umma da Sa'ad suna tsakar gida zaune sun ɗan ba su guri dan su samu su taɓa abubuwan da aka kawo domin su.
Hanne ta buɗe labule ta fito daga uwar ɗaki, dama duk abinda ake tana ji taƙi fita sai da taji Umma da Sa'ad sun fita daga ɗakin.
Akan sallayu ta gansu zaune, ƙawar na siyaya masu lemo a wasu sabbin kofunan roba da aka sayo takanas saboda zuwansu.
Ƙarasawa tayi ta zauna gaban su tare da faɗin "Sannunku" "Yauwa" suka amsa yayinda gwanar Yayan nata ta kasa magana.
Taɓe baki Hanne tayi ta ce "Hala kece Zulaihat ɗin?" ɗagowa tayi ta kalleta ta ce "Eh ni ce, ke kuma Hanne ko? Ai Yayanki yana bani labarin ki" "Uhm gaskiya ne, amma shi bai taɓa faɗa miki cewar yana da budurwa ba?" kallon mamaki Zulaihat da ƙawarta Murja suka yiwa Hanne kafin Murja ta ce "Amma ke kina ƙanwarsa kina neman ruguza masa soyayya?" "Saboda bana ƙaunar wata wadda zata raɓe shi idan har ba Jannat ba, kuma ki sani muddin kika ce za ki auri mayaudari kamar Yayana..." za ta miƙe tsaye ta kaɗa hannu "Wallahi kin kaɗe" tana gama faɗa ta koma ɗaki abinta, ta barsu anan da sakakken leɓe.

YOU ARE READING
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Historical FictionGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...