Episode 14: kyautatawa ta farko

39 6 0
                                    


Sahiba na falour tana kallon wani indian movie ta jiyo sallama ta amsa tana miqewa tsaye hadimar ta dan gaida sahiba tace "gimbiya Amira ce ta aiko ayi miki gyaran jiki na biki"  sahiba da mamaki tace bismillah ku shigo,,, suka shiga mai gyaran jikin ta zauna itakuma  hadimar ta ma sahiba sallama ta koma
Sahiba ta zauna suka shiga gaisawa da mai gyaran jikin, ba wata babba bace bazata pi shekaru 25 a duniya ba dayake tana da surutu sai ta dan dinga jan sahiba da fira tana kara mata haske kan yanayin yadda zasuyi gyaran jikin
Tunda yanxu na wata biyu ne aka biya har zuwa lokacin biki, zamu fara ne da yi sau biyu a sati a wannan watan idan bikin yaa kusa sai a sake kara yawan kwanaki a hankali hakan zaisa gyaran jikin yapi zama da kyau a jikinki
Sahiba tace to masha Allah, matar tace a nuna mata bandakin da zasui aiki da dakin
Daya daga cikin bedrooms din kasa suka dauka matar mai suna Rafi'a kamar yadda tace ta buqaci sahiba ta ware zani guda daya wanda duk sanda zasui aikin dashi ne zasuyi, sahiba ta nemo zani wanda yapi dadewa cikin kayanta yayi laushi, Rafi'a tayi mamaki dan ta dauka gimbiyar zata dakko sabuwar atampa ne amma taja bakinta tayi shiru.....


Sultan na office yana ta faman aiki bil haqqi da gaskiya, yaji knocking yace yes bismillah, khalipa ya shigo ya fada kan cushion din dake gefe ya zauna yana huro iska daga baki... Sultan ya dan kalleshi ya maida idonshi kan aikinshi yace "Ina ka shiga tun safe ban ganka ba, i thought ma bakazo ba inaso na karasa wannan aikin ne ma na kiraka"
Khalipa ya sake bajewa yana jin sanyin AC na ratsa shi yace "u always come early, nikuma danazo sai na wuce gurin engineers din dama munada meeting dasu".... "So how far me kuke shiryawa i hope kunsan ko mene zakuyi producing saida izini na ko?" Khalipa yayi dariya yace "ofcourse manager"
Shiru ya dan ratsa khalipa ya katse shirun da cewa "banyi breakfast ba na fito wlh yunwa nakeji lets go down muga me zamu samu"
Sultan ya girgiza kai "kana da aurenka amma kake fitowa bakayi breakfast ba, bari nayi aure kaga har lunch za'a ke kawomin office" wata muguwar dariya khalipa ya kyalkyale da
"Ko ba lunch ba, badai Amira bace amaryar... kuma ni ai dani da gauro bamu da wani banbanci, banbancin kawai shine na ajiye mutun mutumi a gida ko ba komai in ina neman horo na kalleta zan tsorata"

Sultan ya ajiye aikin yana kallon khalipa dake fadan maganganun carefree yana dariya
"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging" khalipa ya dubi sultan yadda yake magana with serious tone ya tabe baki "to naji lawyern matata... muje muci wani abu pls kai baka gajiya da aiki ne"
Sultan ya maida kanshi kan system kamr beji abinda khalipa ya fada ba, "ai kaji matsalar ka ba dama a danyi raha dakai sai ka dau fishi" still sultan bai tanka shi ba "to Allah ya huci zuciyar d'an kanina to be" sultan ya kalleshi "kai nine kanin naka" khalipa ya bushe da dariya "i know zakai magana ya miqe "muje to babban yaya"
Sultan yace kaje kayi order gani nan
Come soon
Sultan yabi bayan khalipa da kallo, cikakken namiji ne, da bai rashin komi ta kowanne fanni ba, amma zama da khalipa sai wanda ya shirya, sai kuma wanda khalipan ke so, mutun ne da ke haquri da wanda yakeso amma in ya dora ma karan tsana u ll hate yourself in bakka da self confidence domin duk wani abu naka sai yayi criticizing,, something is definitely missing in khalipa something......


Sultan ya tadda khalipa har ya soma cin abincinshi, a da ne khalipa bai iya ci sai ya jirashi... sultan yayi murmushi yanxu an fara girma, sanda suka kusa gama cin aabincin ne khalipa yace "wai kuwa ka lura a purchase na simintin nan yankin Haye sunpi kowanne yanki saye" sultan yace "kwarai amma i don't think its a problem tunda sara ne sukayi" khalipa yace "hakane
Sultan ya ida cin abincin sannan yace da khalipa "meyasa daka ji labarin hadin aurenmu da Amira naga kamar you 'are not that excited wanda nayi zaton zakapi kowa murna"
Khalipa ya girgiza kai "no ai ni naso da kanka ka zabi matarka wlh i hate irin wannan hadin hadin, duk familys din duk iri daya, kuma irin auren hadin nan is just cuta wlh, baka da yadda zakai, kaidai Allah ya baku zaman lafiya" sultan be wani gamsu da tunanin khalipa ba "u always think childish khalipa, mene cuta abu na family" khalipa yace "eh naji din"
"After work zaka rakani zan fara sayayyar lefe", khalipa yace "nikuma?, nida ke a matsayin yayanka haba wuce nan, kaje tare da amaryarka kawai ta lodi kaya son ranta"
"Amarya Tace bata zuwa wai tana busy ta rubuto mini wani dogon list na wasu daga cikin kayan da takeso da kuma wanda bataso sam a saka"
"Chab kace kudi zasuci ubansu" cewar khalipa.... sultan ya shafa sumar kanshi "kuma gasu da wahalar nema" khalipa yasa dariya, sultan kuma yayi murmushi.....

WANI YANKIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora