*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_
Email-Karamciwritersass@gmail.comVisit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb
_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_
*Ina mai bawa Makaranta wannan littafin haƙuri, na ji na shiru da sukayi, ina rubutun script ne, kuma kun san taura biyu bata taunuwa, amma in sha Allah, in sha Allah daga yanzu zaku ji ni ko yaushe, domin littafin yazo gaɓar ƙarewa, kamar yadda nayi bayani a shafin farko cewa littafin gajeran labari ne, zanyi ƙoƙarin ƙarasa maku a ƴan kwanakin nan, ina godiya matuƙa da kulawarku, wanda suka min magana pc duk naji daɗi kuma nagode, messages ɗin pc ba ko yaushe nake iya amsawa ba saboda yawa ina mai baku haƙuri, nagode matuƙa.*
'''Shafi na 17'''
Da mamaki Zulaihat ke bin inda Hanne ta bari. Ranta a ɓace ta miƙe tsaye "Tashi mu tafi kawai" ta faɗa tana kallon Murja. "Haba dan Allah akan wannan banzar za ki wani fusata" "Murja idan ƙanwar sa bata daraja ni ba, kina tunanin zanji daɗin zama dashi? Gaskiya bazan yarda ta wulaƙanta ni ba, tun yanzu zan nemawa kaina ƴan ci" "Hakane kuma." Tashi Murja tayi suka fita.
A tsakar gida suka tarar da Umma da Sa'ad. "A'a ba dai kun fito baku ci komai ba" Murmushin yaƙe Zulaiha tayi sannan ta ce "Ai munci Umma, yanzu Mama ta kira ta ce tana son ganina shiyasa zamu tafi" "To ki gaida ta da kyau" kallon Sa'ad tayi ta ce "Kaje sai ka raka su ko?" "To Umma."
A ƙofar gidan ta kalleshi cikin ɓacin rai ta zayyana masa komai, haƙuri yayi ta bata kuma ya mata alƙawarin in sha Allah zai wa tubƙar hanci.
****
Suna fitowa daga pharmacy Rayyan ya kalli Khalil ya ce "Amma mene ya samu Jannat?" "Ba wani abu bane, kawai tana fama da zazzaɓi ne" ya san ba gaskiya bane, kawai murmushi yayi.
Suna kai maganin Rayyan yayi masu sallama ya tafi.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya. Daddy kwananshi uku a asibiti aka sallameshi, Bikin Sa'ad da Zulaiha kuma an saka rana. Shirye-shirye yake abinsa bai san halin da Jannat take ciki ba, kuma bai nemi ya sani ba, domin bai ma san Safina ta rasu ba. Ta ɓangaren Rayyan kuwa yana ta bincike yana so ya gano mene ya faru da Jannat kuma ya gano sai dai bai samu asibitin da take ba.
*Bayan Wata Bakwai*
*Airport*
Passengers ɗin da suka taho daga Florida zuwa Kano, sune suke ta tururuwar sauka daga jirgi. Yana sauke ƙafarsa yaji gabansa yayi mummunan faɗuwa. Sai da yayi addu'a sannan ya ƙarasa sauka. Mota daya saka a zo ɗaukarsa daga gidansu tuni driver yazo.
Da sauri driver ya karɓi trolley ya saka a booth sannan ya buɗe masa mota ya shiga. Ya zagaya ya shiga motar.
"Yallaɓai barka da sauka"
"Yauwa Sammani da fatan na sameku lafiya?"
"Duk kowa lafiya"
"Ma sha Allah, gidana za ka kaini"
"Maigida ya ce a kaika can, domin gidan na ka babu kowa"
"A'a Safina fa? Bata gidan?"
"Eh haka dai ya ce babu kowa a gidan naka" a zuciyarsa kuwa cewa yayi _Amma meyasa aka ɓoye masa mutuwar matarsa?_Ba wanda ya ƙara cewa komai har suka ƙarasa gida. Yana yin parking Ahmad ya fito ya shiga ciki, yayinda maigadi ya tsaya yana ɗauko kaya.
******
Kuka sosai take hankalinta a matuƙar tashe, Mommy ta dafa kafaɗarta ta ce "Kiyi haƙuri Safina, baki da inda ya fi gidan mahaifinki, ni ma a baya nayi tunanin barin gidan saboda abinda yayi mana, amma kuma da yayi min bayani na fahimce shi, sannan kuma har rashin lafiya yayi duk akan wannan al'amari, ki yafewa mahaifinki"

KAMU SEDANG MEMBACA
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Fiksi SejarahGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...