Shafi na 20

141 15 1
                                    

*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
           _[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
  _[Karamci tushen mu'amala tagari]_
     Email-Karamciwritersass@gmail.com

Visit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb

_*Wannan shafin Sadaukarwa ne ga duk wani masoyin wannan littafin, na nesa dana kusa, ina godiya matuƙa musamman Mdm Alhadji Marie, Amal Beby da sauransu.*_

_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_

                    '''Shafi na 20'''

"Akan Jannat yanzu kumatuna ya zama madakar ka ko yaushe?" ta faɗa hannunta na kan kuncinta, hawaye na zuba daga idanunta. "Akan Jannat za ki iya fuskantar ko wane irin ɓacin rai"

Tashi tayi tsaye ta kalleshi ranta a ɓace yake sosai, ta saka hannu ta goge hawayen idanunta "Ai yanzu ma bata ɓaci ba tunda kana tausayin Jannat ka sakeni sai ka aureta" wucewa tayi har ta buɗe ƙofa ta juyo ta kalleshi. "Kuma ka sani wannan cikin sai na ɓarar dashi wallahi, dan bashi da wani amfani" tana fita yayi saurin bin ta ya tari gabanta. "Me kike nufi da hakan?" "Ai kafi kowa sani" ta faɗa tana aika masa harara. "Farhan dama ashe ke kallon kitse nakewa rogo?" bata bashi amsa ba kawai ta wuce.

                 ****

"Ka sani muddin kace za ka auri yarinyar nan wallahi sai na saɓa maka, kuma sai na hanaku jindaɗi" Mommy ta faɗa rai a ɓace. Rayyan dai shiru yayi ya kasa cewa komai.

"Ni wallahi abin har mamaki yake bani, sai kace wanda aka asirce" Khairat ta faɗa tana ajje waya kan cinya. Ranshi a ɓace ya ce "Idan muna magana da Mommy kina saka baki ranki zai mugun ɓaci"

"Ai ni ya kamata kazo ka rufe da duka sai in san kaji haushi Rayyan, ka huce akan Khairat, ai nina fara magana ita ƙarasawa tayi" bai ƙara cewa komai ba ya tashi ya bar ɗakin.

"Shashasha" Mommy ta faɗa tana bin shi da kallo. "Wallahi Mommy ina ganin Yaya sai kin haɗa da addu'a, dan ba banza suka bar shi ba" "Da alama kam, dole sai na tashi tsaye, dan muddin ina raye ba zan taɓa bari ya auri wannan watsatstsiyar ba."

                 ****

"Sannu Jannat, Allah yasa wannan abu ya zame miki kaffara" kallon Ummu tayi bata ce komai ba, sai Mommy da Daddy ne suka amsa. Khalil yana daga gefe kusa da Daddy.

"Yanzu baki buƙatar komai?" Daddy ya tambaya cike da kulawa. "Bana so na mutu yanzu" ta faɗa idanunta cike da hawaye. "Ba za ki mutu ba Jannat, insha Allah sai kin ga ƴaƴanki har ma da jikoki, ita cuta ai ba mutuwa bace" Ummu ta faɗa tana dafa kafaɗarta, Yayinda Mommy ta tashi da sauri ta fita, dan ji tayi
zuciyarta ta karye.

"Khalil mene ya hana Farhan zuwa?" Ummu ta tayi tambayar. "Itama bata jindaɗi ne, amma tace zuwa gobe in sha Allah za ta zo" ya shimfiɗa ƙarya ba shiri. "Allah ya bata lafiya" Ummu ta faɗa sannan ta maida kallonta ga Jannat.

Da Khalil da Daddy da Mommy ƙarfe 11 na dare suka bar asibiti, dan Ummu cewa tayi a wannan karon ita za tayi jinya.
 
                  ****

Ta juya masa baya, magana yake amma sam taƙi ta tanka masa, har sai daya gama sannan ta juyo ta kalleshi. "Ka faɗa min gaskiya, mene tsakaninka da wannan da ake kira da Jannat" "Wace gaskiya bayan wacce na faɗa yanzu" "Sa'ad ni fa sam ban gamsu da abinda ka faɗa ba, domin yadda take magana kamar ka zalunceta ne"

SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅Where stories live. Discover now