Trailer

126 13 5
                                    

Istanbul Bilgi University,
Istanbul Turkey.

Tunda ta kwanta akan gadon take juyi tana birgima tana chanja direction amma baccin ya gagara a gare ta, ta dauki daya daga cikin throw pillows din da ta jera akan gadon ta danne kirjinta da shi tana lumshe idanu, ta sake dauke shi daga nan zuwa kan fuskarta ta danne kanta da shi amma sam abinda take ji bai ragu ba balle ta samu bacci ya dauketa.
Bayan ta gama juye juyen ta hakura ta tashi zaune ta dora pillows din akan cinyarta ta zuba tagumi tana kallon kyawawan frames din da ta kawata private room din na ta da su, a zahiri ne kawai take kallon su amma gabadaya hankalin ta yana can Nigeria garin Katsina, ainihin mahaifarta inda tayi dukkan rayuwarta, garin da ta rayu cikin matsananciyar kaunar iyaye da kyakykyawar rayuwa, garin da dukkan wani memory dinta yake, mai dadi da kuma bakin memory din da har abada tabon shi ba zai goge daga jikinta da jininta da zuciyarta ba!
Bad memeory din da ya susuta ta ya karya ta ya sabauta ta ya kuma sauya salon rayuwar ta zuwa madaciya daga zuma! wai yau itace a wata kasar take rayuwa ita kadai a matsayin ta na daya daga cikin diyoyin Abba (Alhaji Mu'azzam Bakori) wanda bai yarda diyarsa mace ta matsa ko nan da can daga kusa da shi ba! mai wata irin tsatstsaurar akida akan tarbiyayyar yayanshi. A mafarki idan akace zata baro garin Katsina ta tsallako wata kasar da sunan karatu tashi zata yi tana yi wa mafarkin dariya domin ta san abu ne wanda ba zai taba yiwuwa ba.
But here she is today, after all the ups and downs da Abba ya ga suna shirin rasa rayuwarta gabadaya da amincewar shi da yardar shi harda lallashi ya bar ta ta taho.

Al'amarin da ya faru da ita a littattafai da fina finan soyayya kawai yake faruwa, batai tsammanin a gaske hakan da zai faru ba, balle ga wanda ta sani ko wani makusancinta, ashe a kanta zai faru in reality ba a mafarki ba!
LIFE IS FULL OF SUPRISES

Abubuwan da suka faru da ita sun fi kama da almara ko kuma mafarki, sun fi dacewa marubuta su rubuta su cikin littafin su, zai fi yin dadi ya zama fictional story! sai taji toh koma rubutun zata soma yi kila zai iya rage mata kewa da damuwa? kamar an tsikareta sai ta sauko daga gadon ta nufi study area din ta inda study table da kujera ke jere a gefen table din kyakykyawar study lamp ce da kuma glass verses masu dauke da furannin gaske suna futar da wani sassanyar kamshi.

drawer ta janyo ta ciro katon exercise book da biro ta ajiye akan table din ta bude shafi na biyu ta dora bironta ta soma nazarin sunan da zata baiwa labarin nata.

"Allah ya tsinewa so"
ta fara rubutawa, sai taji title din is too weird! sai tayi canceling ta rubutat
"Shegiya soyayya"
ta kuma yin tunani sai ta ga sunan bai dace ba, sai ta sai tayi canceling ta rubuta
"Soyayya karya ce"
ta sake canceling ta tubuta
"Allah ya tsinewa Q"
ta kuma sokewa ta rubuta
"Duka maza yan iska ne"
ko kuma dai haka zata ce
"Allah wadaran maza"

A kalla tayi minti talatin tana tunanin sunan da zata saka wa labarin ta, ta rubuta ta goge, amma duk wanda tayi tunani sai taga bai zauna mata a kai daidai ba! Ashe marubutan aren't just ordinary people? ashe ko kirkirar sunan labarin ma ba sauki ne da shi ba? toh bari kawai ta bar maganar suna idan ta gama rubutawa ta samo sunan daga baya.

Sai ta dora biron ta fara tunanin toh daga ina zata fara? tun daga ranar da aka haifeta ko kuwa daga lokacin da aka saka mata a makaranta? daga nursery ko primary ko secondary? daga lokacin da hadu da alakakai din da ya rusa mata dukkan farin ciki da jindadin ta ko kuwa daga lokacin da ta shiga matsananciyar soyayyar da ta juye mata masifa da bala'i da tashin hankali?
nan ma sai taji kanta ya kulle ta dinga rubutu tana sokewa, tun tana yi da kwarin guiwa har taji ta sare ta daina sha'awar rubutun gabadaya, saboda ta gano cewa ba kowanne Random mutum ne kawai zai dauko biro ya soma rubutu shiryayye wanda zai making sense ba! Shi rubutun is a gift! baiwa ne daga Allah! kuma alamu sun nuna ita tata baiwar ba'a wannan fannin take ba.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 01, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HABIBUL QALBWhere stories live. Discover now