ZAGON KASA 1
Musalin 12 na dare nahau online domin duba comment din da members dina suyimin dangane da labaran da nake bayarwa a group dina mai suna KOTUN MASOYA.
Bayan na gama yan dube-dubena zan sauka kenan sai naga message ya shigo.
Koda na duba sai naga ai macece tamin magana domin Zainab Zee nagani a user name dinta amma batasa hoto ba.
Abun da tace shine "Slm har yanzu bakayi bacci ba?
Fuskata a sake nace "Wslm ai indai kiga na kwanta bacci sai zuwa karfe 1.
Murmushi tayi tace "hmm kodai nazo na tayaka kwanane?
Cikin yanayin mamaki nace "ban fahimci abunda kike nufi ba?
Du-du-du bamui magana ta cikakkun 5 minutes ba sai ji nayi tace "kana sex chat??
Murmushi kawai nayi hade da cewa "ashe kema kina daya daga cikin mutanan da suke tattare da dabi'un dabbobi?
Cikin yanayin bayyana bacin rai tace "Da kasan wadda kake magana da ita na tabbata ba dalilin da zaisa kayi kokarin dangantani da dabbobi.
Raina a bace naja wani dogwan tsaki nace "Mutswwwww!! Kefa a cikin dabbobinma kinkai makura a cikin karnuka irin wadanda suke haushi cikin dare ba gaira ba dalili.
Ban sani ba ashe wannan furucin yai matukar fusatata wanda hakan yasa ta kuduri niyar afkani a cikin katafariyar chakwakiya.
Budar bakinta sai tace "Ni kuma nayima alkawarin saika kwanta dani a zahirin ba'a sex chat ba badan komai ba sai dan bukatar lalata rayuwarka sannan ta sauka daga online.
Nan take nikuma nayi Remove and Block dinta.
A kalla an samu kimanin wata 6 da faruwar wannan al'amarin wanda hakan yasa gaba daya na manta da abun daya faru a tsakanina da ZAINAB ZEE.
Sanadin labaran da nake bayarwa a social network ne ya hadani da mutane da dama domin bazan iya iyakance mutanan da suke bibiyar labarai na ba.
(Musa Ibrahim) yana daya daga cikin masu bibiyar labaraina amma kwata-kwata da haduwata dashi bamu dauki cikakken wata biyuba.
Ba ranar da zanhau online ba tare da nayi chatting da Musa Ibrahim ba.
Kwatsam wata ranar asabar da musalin karfe 8 na safiya sai naji kira ya shigo wayata koda na daga kiran bayan mun gaisa sai yace
"kana magana da abokinka Musa Ibrahim daga facebook na dauki numbarkane a cikin labaran da kake bayarwa domin na kiraka mu gaisa.
Bayan mun gaisa sai yace "ga kanwata itama tana bukatar gaisawa da kai.
Cikin yanayin girmamawa tace "salamu'alaikum dan uwa anwuni lafiya?
Fuskata babu alamar damuwa nace "lafiya kalau yar uwa yasu abba da mummy?
YOU ARE READING
ZAGON KASA
Romancelabarine mai ban takaici gaminda nishadantarwa gami da fatakarwa wa'azantarwa.