Page 4

11 1 0
                                    

💕💕 RUSHDAH 💕💕

     Page 4

©️oum zahrah....💞

Zaune suke a dining suna breakfast,
Cin abinci suke a nitse,

Dady ne ya kalli mami dake kusada shi ya ce har yanxu hanan basu sakkoba
Natura akira su suna xuwa .
Hanan da rushdah ne suka fita daga dakin , sakkowa sukayi suka nufi dining
A hankali take tafiya cikin sanyinta da yake nature dinta ne .
Gaidasu hanan tayi haka ma rushdah,
Ko kallo basu ishi mumy da Azeez ba sai cin abincin su suke wanda hakan ba karamin kona wa dady rai yake ba ,
Xama hanan tayi kusa da ya Ayaan
Rushdah ko tsayawa tayi ta rasa in da xata xauna ,
Kujera daya ne babu kowa akai wanda ke daya side in da ayaan ke xaune .
Rushdah xauna mana ganan guri kusa da yayanku ,
Bai so xaman yar kauyennan kusa da shiba amma ba yanda ya iya saboda dady.
Dagowa yayi suka hada ido ya hade fuska shi dai gaskiya bai son wannan yar kauyen amma da alama dady da mami sun bata wani matsayi ,
Zama tayi a dosane saboda sarai ta lura wanan guyen bai so xaman ta gurin ba .
Hanan yi serving din ta pls

Ok mami , bude coolern tayi ta debo mata chips da egg din sai ta xubo mata pepper soup din ta tura mata gabanta da tea ,
Mika hannunta tayi don daukan spoon a kusa da ayaan mistakenly ta ture pepper soup din ya xube wa ayaan a jiki,
Daskarewa yayi tsabar bacin rai .
Dan Allah kayi hakuri ,
Idonshi ne ya rene ya koma ja .
Azeez ko gimtse dariyar da ke cinsa yayi kar ya futo saboda ya san hanlin ayaan tsap zai make shi .
Subhanallahi ayaan tashi ka je ka cire kayan .
Hanan ne ta mike ta taimaka masa ya tashi tsabar takai ci ko amsawa mami da ke tambayanshi ko da zafi pepper soup din ya wuce fuuu ya haura sama.
Xauna mana hana ai ba da gangan kikayi ba kin bi kin daga hankalinki,
Xama tayi amma ko yunwa bata ji gani take kaman ya dauka da gangan tayi.
Azeez ne ya tashi don mika mata spoon din da daman shi xata dauko ya jawo mata wannan abin.
Harar da mumy ta masa shi yasa ya xauna ba shiri , daukan spoon din tayi suka cigaba da break fast kowa ya koma daki.

Shigewa bayi yayi yana mai jin haushin wannan wawiyar yarinyar,ji yanda ta xuba mishi abu kaman bata gani?
Mtswwww ..
Wanka ya sake yi yafito duk ransa abace. Completely ta bata masa mood dinsa .

Hanan dan Allah wanchan mutumin baxai ga kaman da gangan na xubar masa ba ?
Wlhy ba da sanina na xubar masa ba ki yarda da ni,
Rushdah ba wanda ya ce kinyi laifi ki dai na kuka pls na ga alama daman kukan kike sonyi ko?
Ba haka bane .
Mami ce tashigo ta samesu hakan .
Hanan ku shirya ku tafi kasuwan mana ko sai rana tayi ne?
Muna fitowa yanxu ,
Yanxu dai ki wuce bayi ki wanko fuskarki ki saka powder mu tafi kasuwa.
Tashi tayi a sanyaye ta shiga wanko fuskarta tayi ta futo ta dauki hijab dinta suka fito suka je parking lot jiran driver,
Mai gadi ne ya matso suka gaisa da hanan ya shaida mata driver ya fita da mumy yanxu,
Toh mallam habu nagode .
Saukowa yake daga staircase din cikin shirinsa na English wears sun masa kyau ya fito kamar balarabe,
Hangosa hanan tayi da sauri ta nufesa,
Ina xakije haka ?
Kasuwa xamuje ya Ayaan amma umar bayanan ko xaka saukemu a wuse market idan muka gama xan kira shi ya dauko mu ?
Bai yi magana ba amma da alama ya yarda kiran rushdah tayi wanda ta tsaya a gefe tana kallonsu , tsoronsa take saboda gani take xai hukuntata akan abinda tayi mai daxun,
Ke idan ba kuda abinyi ku gayamin in wuce .
Sorry yaya ta kusa karasowa tsaki yayi shifa gaskiya bai cika son yanda abu ke hadashi da wannan yar kauyen komai sai ta nuna kauyancinta .
Tun da tashiga tayi shiru suko sai hirarsu suke kamar batanan cikin motar.
A kasuwan ya saukesu ya wuce xuwa ina xa xaashi.

Maryam yaushe kika ga ya dace mu gayama yaronnan halin da ake ciki game da abinda ya faru a ribado?
Mu dan bashi lokaci ya dan kimtsa kasan jiya ya dawo bayan wasu shekaru dayayi baya tareda mu .
Shikenn Allah ya shige mana gaba .
Ameen ya rabbi .

Xaune suke a garden shida abokinsa yazid ,
Kai kuma tun daxun nake jira shiru duk na rasa sukuni na,
Sorry kasan abin yanxu yaxama hot cake dakyar na samo wanan agurin kb ,

Guy wata chik aka kawo fah wlhy ta hadu da alama baxata yi wuyan samuba ,
Tapawa sukayi
Amma kasan mey ?
Wannan dan nachin ya dawo jiya so xamu dinga waya kafin kaxo kasan bai son alakarmu amma ba yanda ya iya dole ya bar mu yanda ya ganmu,
Gaskiya bro dinka dan yawa ne ya xakayi batun wannan beb din ?
Hmmm bari dai xamuyi magana yanxu bari in je in watsa wannan kayan kafin in yi tunanin hanyan da xanbi , sallama sukayi yazid ya fice yana layi kamar xai fadi ya shiga motarsa mai gadi ya bude mai yana fatan shiriya ga yaran .

Agajiye suka dawo daga kasuwa rike da ledoji manya manya guda biyu bude kofar palorn sukayi .
Mumy ce xaune a palorn ita kadai tana kallon news gaidata suka yi ta amsa a ciki ciki,
Wuceta sukayi suka haura sama .

💕💕RUSHDAH 💕💕Where stories live. Discover now