Episode 25: Rejection

26 7 0
                                    

Khalipa cikin rauni yace "ya akai milana? Im i not accepted? Baki so na ne?" Ya furta kalaman kaman yana dabawa kanshi wuka a ciki,
Milana ta dena girgiza mishi kai ta buda bakinta tace "babu wata maganar soyayya tsakani na dakai khalipa, mu'amula mukai dakai ta kyautawa saboda musulunci matsayinka biyu ne a gurina, kai dalibi na ne danake karantarwa kuma majinyaci na ne wanda nake kula da lafiyarshi ka dena tunanin bayan wannan alaqar kuma akwai wata inaso ka tsaya iya matsayinka"

Khalipa ya zuba mata ido  "he just can't let her go he's so much in love with her" yace "a gurin ki milana wadancaan sune matsayin da kika daukeni amma a gurina kinada babban matsayi, wallahi inaji kamar zan iya mutuwa idan kika qi ni idan har ban sameki ba milana"
Milana ta kalleshi tayi ajiyar zuciya sannan ta wuce zata koma bukkarsu, yayi saurin rike hannunta ya kamota yana kokarin rungumeta a sanda idanunshi ke zubda hawaye
Milana ta fizge hannunta cikin jin haushi ta kwace kanta duk a lokaci guda ta sauke mishi wani zazzafan mari a fuska
Ya shafa gurin data mareshi yana kallon idanunta da babu ko digon tausayinshi, "karka sake gigin tabani khalipa karka sake, wannan shi ne na karshe, idan kuwa ka sake na rantse da mahalicci na sarki Allah sai kayi nadama mai yawa, karkaga ko a baya ina dan rike hannunka saboda duba bugun zuciyarka, wannan inayi ne da niyyar kula da lafiyarka a matsayin majiyanci na, soyayya ni da kai ba abu ne mai yuwuwa ba"
Ta wuce shi yana tsaye a daskare kamar gunki

A hankali ya tsugunna a filin gurin da babu rufi kuma babu bishiya yayyafi ya soma sauka yana jika er sharar dake jikinshi,,, bai tabaji zuciyarshi tana mishi irin wanann zapin ba, mene aibunshi da zata ce bata sonshi, shi ya yarda ta dokeshi ma tace tana sonshi dan bayajin zai iya rabuwa da begenta cikin ranshi, tun ranar farko daya fara buda idanunshi a wannan duniyar da bai san kowa ba da ita ya fara tozali kuma idanunshi suka tabbatar mishi da she's the one,,, the one and only, kash zuciyarshi bata mishi adalci ba, zapin dayakeji yakeso ya fitar dan haka ya tsaya tsugunne cikin ruwan mai karpi yana zuba yana jikashi tun daga gashin kanshi har tafin kafafuwanshi, sam sam khalipa bai da niyyar komawa daki domin ya kasa jin sassaucin dayake nema,
Sidi yaji shiru shiru dan har ya soma bacci ma ya farka yaga babu khalipa ya dan leqo, a mamakance ya soma tunanin ko khalipa ya fara haukacewa ne, tunda inba hauka ba meya kai me hankalin cikin wannan ruwan dake zuba kamar da bakin kwarya,

Sidi Ya nemi abinda zai dan kare kanshi ya fita da dan gudu ya karasa ya riko khalipa yaja shi zuwa daki, khalipan rawar dari kurun yake, ya zauna a kasan dakin jikinshi na rawa, sidi yace "meke damunka? Akwai inda ke maka ciwo?" Khalipa ya gyada kai "ina ne? Fadamin" cewar sidi
Khalipa ya nuna zuciyarshi yace nan "zuciyata namin suya, tana fitar da zapin da gangar jikina bata iya dauka inaji kamar zan mutu"
Sidi bai fahimci inda zancen khalipa ya dosa ba saboda a tunaninshi ko jikinshi ne ya sake motsawa, ya dakkowa khalipa wasu kayan busassu yace chanja ka saka wannan tukunna, khalipa ya karba ya chanja tunaninshi gabadaya yana gun milana, bayan ya chanja sidi ya debe wadancan ya saka cikin wani bokiti sannan ya nemawa khalipa warm guri inda ruwan dake diga a bukkar baze dameshi ba, ya samu khalipan ya kwanta ya nemi malullubi ya rufe shi ya sake kawo wani zanin ya rufeshi saboda sanyi

Jikin khalipa feels warm thanks to sidi amma zuciyarshi yaki akeyi, bai taba tsammanin milana zatai rejecting dinshi ba? Ya dauka itama tana da same feeling a kanshi tunda yaga kyautatawar datake nuna mishi kuma dai yaga shidin ba baya bane ta fannin kyau amma ya zatai mishi haka, wannan tunanika khalipa yayi tayi kanshi ya dinga ciwoo a sanda bacci ya daukeshi ma bai samu nutsuwa ba domin kwakwalwarshi bata huta ba, sai ya soma tuna event din daya faru ranar, a ranar dayaji zuciyarshi na mishi daci kan sukarshi da aka dinga yi a hankali cikin baccin ya soma tuna rayuwarshi ta baya dukda bai tuna dukaba amma ya fahimci shi dan wani sarki ne a wata masarauta, ya fahimci yanada brother like a twin brother shi ne sultan din, ya fahimci yadda akeji dashi kuma shima yadda yakeji da kanshi, lafiyarshi da fatarshi, daa yadda 'yan mata ke burin ya zama nasu, ya kuma fahimci cewar an aura mishi wata sahiba amma bai tuna irin abubuwan daya mata ba, he then recalled hashim amma bai gama gano suffar hashim din ba ya dai tuna irin takun saqa da sukeyi and lastly ya tuna irin makirci da aka hada mishi a kamfanin siminti,
A kai akai yake fidda huci da numfashi sai ya samu kanshi da bude idanunshi a lokaci guda dukkansu biyun, zapi yake ji a jikinshi sosai, ta ko ina ya dago ido ya kalli sidi dake gefe yana tilawa
Sidi ya ankara da khalipa yayi saurin karasawa gareshi yace sannu sannu, ya taimaka mishi ya tashi zaune har a lokacin zuciyarshi tana mishi azabar zapi babu abinda yakeso ya gani yanxu sai milana

WANI YANKITempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang