🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *RASHIN SIRRU*
(Sharrin Abokai)Alk'alamin
JANNA JAY
Wattpad @jannahjay8Marubuciyar
A dalilin su
Faccala tace
Kuduri ko Manufa
Namijin KishiShafi na Goma sha Biyu
Maman Hanan har dare tana nan, ganin ank'i watsewa ga uban kira da Sale yake mata yasa ta tafiya bayan ta jidi abubuwa ta tafi da zummar kwana kusa zata dawo mata.
Shirin tarb'ar Sulaiman Zee tayi komai yayi tsaf banda favorite dishes nashi da tayi, zaman jira suke sai lallab'ar Fa'iza take akan kar ta tafi Dariya Fa'iza tayi tace " Gaskiya Anty banson na zauna na takura maku balle kinsan Ya Sulaiman kar ya sagemin gwuiwa ya koreni" kama baki tayi " Haba bazai yiba insha Allah, kinga tunda kikazo ban fiya jin laulayi ba" Dariya sukai gaba d'aya " Kinsan zama da mutum sau tari yana sa mutum jin karfin jikinshi" Dirin mota da suka jine yasa Fa'iza rugawa daki tana dariya, fuskar Zee tuni ta washe ta tafi taryar mijin nata. Koda ya shigo ta rungemshi wata siririyar ajiyar zuciya ce ta kwace mata dariya yayi ya rad'a mata " This shows you really miss me" bata ce komai ba sai huci kad'an da tayi idonta a lumshe, kara kamkameta yayi a jikinsa ya rad'a mata " How is My Baby?" yana shafa cikinta a narke tace " He missed his Fa" ba k'aramin farin ciki Zee ta shiga don yawan tsoron da akai ta bata a gidan ya dameta, bakinta kasa rufuwa yayi aikuwa tunda Fa'iza ta fito ta gaidashi, suka shige d'aki Fa'iza bataga fitowar daya a cikinsu ba sai da goma ta wuce Zee ta zo mata sai da safe. Tun bayan dawowar Sulaiman bata k'ara tsorata a gidan ba.
Bikin Salman ya kankama tuni Zee sun gama yin ankonsu na matan Abokai wani Paper Lace ne mai kyau d'an 25k zasu saka ranar Kamu, ganin yanda ta dan k'ara cika yasa tasa aka mata Maxi dress mai shigen Boubou ta kuwa fita tsaf, don tayi kyau ba k'arya ga wani Dauri da ta kafa wanda ya fitar da tsantsar kwarjininta da aji, takalmi da jakarta wanda suka dace dashi, haka wuya da hannunta. Tun da suka shigo wajan event din tare da su Hajar Hamida khadija, Sulaiman fara'arshi ta k'aru don sai yaga kaf wajan ba wanda ya kamo ta had'uwa ga Sulaiman da son yaga nashi ya fita, tunda suka hallara a hall d'in idon mayen ke kanta ga 'yan mata k'awayen amarya kowacce taci make up da dinkinta amma ba abunda yake d'aukar idonshi sai Zee ba abunda ke kai kawo a ranshi sai in ya tuna yanda Sulaiman ke kuranta taste d'inta kawai sai yaji tsigar jikinsa na zubawa, idonshi tuni sun shige lungu ya gaza d'aukesu daga side da suke. Ana tsakiyar Sulaiman ya zo inda Zee take ya jata dan gefen Hall din ya mata introducing wani old friend d'inshi sai ga Hamza da Ja'afar sunzo Hamza yace " Hajiya Zee wannan gayu kaman kece amarya" murmushi tayi tace " Ina kuwa wane ni da kamo kafar amarya, mu manya masu nauyi" kaman had'in baki shida Ja'afar suka ce " Haba ai anan yan mata nawa suka fiki girma da tsufa" Oga Sulaiman kai ya fashe don daga jin maganar su Hamza yasan ba shikadai yaga haduwar Zee d'in tasa ba, haka suka dinga kururuta ta tana dojewa daman shi Hamza haka yake kaman wani bature bai gani yayi shiru. Bayan ta koma ta zauna ganin idon mutum biyu suna mata kallon da ta kasa gane inda ya nufa yasa gaba d'aya gabanta ya dinga faduwa ga wani irin takura da takeji. Amarya da Ango Salman sunyi kyau kuma komai ya tafi a tsare, haka program din ya k'are idonsa na bibiyar Zee, a na gamawa kowa ya watse masu masauki suka tafi sukan su Sulaiman da Zee sai hotel, haka Idris da sauran kasancewar komi a Kano ya wakana, don Salman d'an kano ne. Tana shiga bayan tayi wanka tayi sallah kwantawa tayi flat kan gado tana jin wani tsoro na shigar ta " Wai meyasa haka take faruwa? Meyasa shi bai iya ajiye idonshi gefe, haba kallon k'urillan yayi yawa" tana tsakiyar tunanin k'iran Hajara ya shigo mata tace mata " Hope kin shirya fita" rashin nutsuwar da take jine yasa tace " Gaskiya banjin zan iya don banjin dadi" Hajara tace " ko mu shirya tafiya Maternity? " dakyar take yake tace " Hmmnn zakiyi bayani in yazo kanki, kiji ya muke jin yawan laulayin nan" haka tayi sallama ta cigaba da kwanciya shikam Sulaiman a bayan sallah a masallaci nan ma sun had'e da wasu friends d'insu na A. B. U sai aka shiga wasu abubuwan.
YOU ARE READING
RASHIN SIRRU (sharrin abokai)
Ficción GeneralYana shigowa yaji wayar matar tasa tana ringing sai dai kafin ya iso kan gado inda take tuni wayar ta tsinke, basarwa yayi ya isa kan gadon yazauna tare da furta "wash" ya zare hular dake kansa, karar shigowar message wayar tayi da same number da ta...