Episode 28: politics

31 2 0
                                    

*WANI YANKI* 🍂🍂

#family #royalty
#love #politics #familybusiness
#obsession
#mystery #conspiracy

Na Aysha b. Naseer
.
.
.
Wattpad @ AyshabNasir



Straight sultan ya wuce gurin kiran galadima, tadda shi a tsaye cikin farfajiyar falourn shi yana kaiwa da komowa, sultan ya dan rankwafa yace "barka da dare" galadima ya juyo ya mishi wani mugun kallo sultan ya sauke idanunshi kasa hannayenshi na a bayanshi ya rikesu,
Galadima ya koma kan cushion ya zauna ranshi a bace shima sultan ya samu kan carpet ya zauna, suka danyi shiru na sakwanni kadan kapin galadima ya soma magana cikin fada fada
"Yanxu kai sultan har kayi girman da zaka bijirewa maganata na saka kaje ka dinga ganin yarinya amma shi ne kake kokarin watsa mini kasa a ido, kanaso ka nuna cewar cikin masarautar nan ban isa dakai ba, wato ka zabi diyar mai martaba akan tamu, tun yanxu ma ka fara bijirewa maganata kenan yaya idan kuma ka hau kujerar gano, anya kuwa yarima anya"
Sultan yana sauraren fadan galadima bai ce ko uffan ba saida ya gama yaji yayi shiru sannan yace "ayimin afuwa, ban isa na bijerawa maganarka ba  wannan batun auren ni kaina a sama na jishi, dukda anyi shiri dama tun ba yanxu ba, kuma ba laifin mai martaba bane, shi yana ganin an riga an gama magana tun ba yanxu ba shiyasa bai tsaya jin ta ra'ayi na ba"
"Idan baiji ra'ayinka ba sai ka ki sanar mishi da abinda ke ranka?"
To bari kaji koda ka auri Amira sai ka auri khadija, kuma ni da kaina a yau zanje na sanarwa da mai martaba batun aurenka da khadija tunda kai baka iya ce mishi bakason diyarshi... Banason jin wani karin bayani tashi ka fita"
Sultan ya tashi simi simi ya fice galadima ya cigaba da banbami
"Yo in bamu iya tankwaraka ina amfanin duk yakin da muke kan ka hau kujerar, ra'ayinmu dole shi za'abi kuma a mulki na gaba dole ta ko ina mutanenmu su shiga, khadija matarka ce wannan a rubuce take, haka nan ka auri diyar hamida su sake kankane komi, wallahi bata sabuwa"

Sultan yaji kanshi ya mishi wani zapi, wai meyasa ake mishi haka ne innalillahi wa inna ilaihi raji'un yake ta maimaitawa har ya samu ya koma gida,,, a daren ranar galadima yayi kiran mai martaba, ya zayyane mishi komi da ake ciki ya kara da fadin
"Wato saboda ni ba'ajin maganata shi ne aka hana abinda nakeso, bayan kuma yaro yace bayason ita yarinyar wajenka, ita wannan khadija yakeso, to fisabilillahi a bar yaro ya zabi abinda yake so mana"

Mai martaba yaji dacin kalaman galadima sosai, ko kadan yana gudun abinda zai hadashi da galadima, domin babu sauki a tare dashi, mai martava keda mulki amma galadima keda ta cewa, inkuwa ya kawo shawara to dole a bi in ba haka ba hankulan jama'a dayawa sai sun tashi, kowa a fada tsoronshi yake domin yana da goyon bayan manyan yan siyasa masu ci a yanxu, yana da karpi sosai a cikin mulkin, dama shida fulani ke fafatawa da mukarrabanta, ita dinma ba baya bace gurin hada tuggu da son ganin bayan duk wanda ya hanata rawar gaban hantsi sun buga da galadima amma ta kasa domin tun sadda sukai sanadin mutuwar yarima Haidaar AAli mahaifin sultan ya tashi tsaye
Asali ita fulani data shigo gidan sarautar sanda ta auri muhammad Auwal (mai martaba) dama tana da niyyar ta zama fulani wannan shi ne babban burinta na wannan lokacin, a sanda kuma ta soma bincike da shiga harkokin masarauta sai ta fahimci bakin jinin haidar AAlin gun jama'ar masarautar, ta kuma fahimci akwai wani shiri da ake son aiwatarwa, dan iya shine mai kawo mata duk wani rahoto a lokacin, dan haka har da ita akai shirin da aka kawar da haidar AAli sannan aka nada Muhammad Auwalu kan karagar, a sanda burinta na zama fulani ya tabbata sai wasu burikan suka karu sukapi na da yawa, dama haka power take ko yaushe kana gaba kana sake jin dadin ta ne kuma wasu burikan na karuwa kanaso kapi matsayin da kake duk girmanshi, wannan yasa taji tana son kau da sultan domin jininta yayi sarauta...
Shiko galadima bai ankara da shirinsu ba sai da yaji mutuwar surikinshi (mijin 'yarshi), a lokacin bashi da wani goyon baya ko power mai yawa dan haka sai ya rabu dasu ya dinga hada connection a hankali a hankali, har yayi karpin da babu yadda fulani ta isa ta taba nashi... Karpin da yasan ita kanta fulani bazata taba kawowa, domin shi komi nashi a sirri yake, wanda suka bayyana ma kadan ne
Yana da hadin guiwa da masarautar haye, wasu shirin duk tare sukeyi, domin suma haye suna son cin arzikin gano amma mukarraban fulani sun hana, hakan yasa suke so sultan ya hau mulkin domin a ganinsu shi ne na galadima, idan kuwa mulki ya dawo hannun galadima zasu samu Alkhairi yadda suke so, sai dai shi mai martaba bai san da duk wannan matsalolin ba abubuwan dayasani ba wasu masu yawa bane, zuciyarshi a wanke take hakan yasa yake ganin kowa da Alkhairi....
Wannan kenan

A take mai martaba ya sa a mishi kiran sultan yazo yanxun nan ba sai anjima ba domin ranshi ya baci, kiran na iske sultan yaji gabanshi ya buga amma dama ya shirya yasan lallai hakan zata faru... Yayi maza yaje amsa kiran mai martaba,
Yana zuwa Mai martaba ya fara mishi fada saboda abin ya mishi ciwo
"Yanxu sultan abinda kaje kana fada kenan, zan maka auren dole, zan cusa maka diyata? Duk tambayar dana maka na zaunar dakai akan ka fadamin in da wacce kakeso? Ka tsarani kace laallai babu wadda kuke tare ashe kana tare da diyar Alkali, ni a matsayina na shugaba ni zaka jawowa zagi sultan, ka jawomin abin magana cikin fada a dinga yi dani da diya ta"
Muryar mai martaba har breaking take kamar yana shirin kuka
Sultan ya maimaita innalillahi domin lallai yasan ran mai martaba ya baci wanda bai dauka hakan zai faru ba, shi ya dauka zasuyi magana da salama ne tunda yasan mai martaba mutun ne bamai son hayaniya ba, amma tunda yaji wannan fadan yasan abin ya mishi ciwo
Sultan jiki a sabule ya soma bayaninshi
"Nasan ranka ya baci mai martava kuma ya baci ne sabosa bakai expecting abu irin wannan daga guri na, ka daukeni mai hankali da nutsuwa da kake saka ran zan kula da jagorancinka koda nan gaba, disappointment ne yasa kaji wannan bacin ran, dan Allah kayimin afuwa ka bani dama nayi maka bayanin komai dalla dalla"
Mai martaba ya dan zauna kan shimfidarshi da aka kawata, ina saurarenka
Sultan ya cigaba
"Tabbas a sanda mai martaba yazomin da maganar Amira gaskiya ta na fadi na cewar bana tareda kowa, saidai yanxu maganar ta chanja kuma yanxu ne kadai damata da zan fadi abinda ke zuciyata a nan gaban mai martaba, ba karya bane ina tare da wata wadda zuciyata ta zaba amma kuma ba khadija bace diyar galadima, shi batun khadija wannan ra'ayi ne kawai na galadima dayakeso, zabinshi ce ba nawa ba ban kuma san dalilin zaba min ita ba"...
Mai martaba ya katseshi wacece ita wadda kakeso din?
Sultan sake dukar dakai yanajin wani nauyin gaske
A hankali kuma ya bude baki yace "maganarta naso maka daxu amma sai na kasa saboda gudun kada kaji kunya kada azo ana kananun maganganu kan fasa auren diyar takawa, abinda zai rabaka da farincikin ka shi nake gudu mai martaba, Allah ya kara nisan kwana"
Shiru ya biyo baya kapin sultan ya samu courage na amsa tambayar, mai martaba ya sake tambayar
"Tambayar a nan itace wacece?"
"Diya ce gurin Alhaji Aminullah sani mai kaba"
Mai martaba yayi shiru yana nazari amma ai diyarshi mace guda daya ce
Sultan yace "hakane takawa"
Takawa ya jinjina kanshi cikin mamaki sai yace "idan na fahimceka matar dana aurawa marigayi khalipa kake nupi" sultan ya sake sunkui dakai "hakane mai martaba Allah ya kara nisan kwana"
Mamaki bai bar mai martaba ya sake cewa komai ba
Har dai sultan ya dan gaji da zaman domin shiru ne ya ratsa sosai wanda sultan shikuma yana sauraron yadda zuciyarshi ke harbawa
"Kaje zan duba nagani" cewar mai martaba a sanda sultan ya fidda rai ma zaiyi magana

Sultan ya tashi jiki a mace ya fita kamar mai tsoron taka kasa, saidai yaji saukin nauyin da zuciyarshi ke mishi koma mene zai biyo baya yasan mai martaba zai yi iya adalcinshi ne, dan haka yana jiran result badan ma dare yayi ba da gurin sahiba zaije ya sanar mata abinda ke faruwa amma kar damun yayi yawa, zai haqura zuwa gobe in Allah ya kaimu...

A yadda sultan ya tsara shine daya tashi yaje gurin sahiba amma sai kuma yace zai bari idan ya taso amma hakan ma bata samu ba, ayyuka ne ta ko ina kuma na mai martaba ne, wasu kuma na shirin bikin ne da mai martaba ke aikanshi, yaga dai lallai ba'a fasa komai na shirin bikin ba sai ma karawa da ake tayi, sai jikinshi yayi sanyi ya rasa kwarin guiwar zuwa gurin sahiba
Sahiba  tun safe take juya wayarta a hannunta, bata taba rike waya haka a hannu ba, infact wayar ma sai ta kwana biyu batasan a duniyar datake ba amma tun jiya da sultan ya tapi ta lalubo wayar ta mata chaji take yawo da ita duk inda zataje, tasan yanada number ta tunda shi da kanshi ya saka mata simcard na kasar waje a lokacin kuma  taga har nan kasar akwai network ma'ana layin yanayi, saidai har dare babu sultan babu labarinshi, babu kira, sai ta kirkirar mishi uzirin ko ya kira bata shiga bane kuma bai samu zuwa ba, amma Allah yasa gobe yazo, idan yazo sai ya karbi numberta ta nan....

#not edited

WANI YANKITempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang