Episode 29: Becoming mrs

28 3 0
                                    


Yau Alhamis, idan har za'a daura auren yarima sultan da gimbiya amira to gobe ne ranar kamar yadda momy ta fada, inaso na ganshi kapin goben,,
  kapin ranar da za'a daura aurenshi da wata, to kodai duk batun soyayyar a mafarki na ne.. Sahiba ta sake juya wayar hannunta tanaji zuciyarta na dada bugawa, ko kuma dai yayi fushi ne dan nace mishi xanyi tunani? Amma ai kalamanshi basu nuna yayi fushi ba sam
Tayi shiruuuu "maybe nice nayi gajen haquri"

Gajiyar jiya tasa sultan bai tashi da wuri ba, hakan yasa yana tashi a girguje ya shirya ya tapi office, saidai tun bai yi nisa a ayyukan shi ba kiran mai martaba ya iskeshi kan yana nemanshi idan ya tashi a aiki, yau kam yanaso yaje gidansu sahiba gaskiya domin maganar ba ta waya bace baze kirata ba, zaipi so yaje ya sameta da kanshi ya sanar mata abinda ake ciki, taji bajintar da yayi a kanta na kaiwa mai martaba zancenta,
Yana tashi ya koma gida ya danyi wanka ya sauya kaya, danma ayyukan masu muhimmanci ne akeyi badan haka ba bazeje aikin ba ai, saida yayi sallar la'asar sannan yaje kiran mai martaba, nan pa mai martaba ya saka shi a gaba da dogon jawabi mai ratsa jiki, domin mai martaba yayi amfani da kalmomi masu dadin saurare ga kunnuwan sultan...

Sai magrib suka tashi sukai sallah sannan suka dawo aka sake wani meeting din dashi da Amira, sakamakon abinda ya faru a meeting dinne ya hana sultan zuwa ga sahiba, zai jira har sanda mai martaba ya kayyade mishi
Sultan ya sake juyawa kan shimfidarshi yana jin kamar kuma baze iya jurewa ba, zuciyarshi na ingizashi yaje ga masoyiyarshi......

Da tunanin sultan sahiba tai bacci kan dadduma tana rokon ubangiji yasa hakan yapi mata Alkhairi, yasa auren da mai martaba zaiyiwa sultan yasa shi yapi musu Alkhairi gabadaya, zuciyarta tayi nauyi, ta bude idanunta cikin dare yapi sau 5 duk a zatonta asuba tayi amma idan ta kalli agogo sai taga sabanin haka, sai taji dare ne, itakam wannan dare yayi mata tsaho, gabadaya baccin bai mata dadi, bataso gari ya waye dan kada a daura auren sultan amma kuma tanaso daren ya kare saboda wani bakinciki datakeji ba, daga karshe ta sake yo Alwala tayi nafilfilu, har akayi kiran asubahi tayi sallah sai kuma bacci mai nauyin gaske ya dauketa da dogon hijabinta a jiki,
Sahiba taji hayaniya a kanta kuma kamar ana kokarin cire mata hijab, ta farka ta buda idanunta, sai taga cousin sisters dinta a dakin ta tashi zaune da sauri....
Babbar cikin su Hajara ce tace "sahiba kinsha bacci" sahiba ta tashi tsaye tace "anty hajara yaushe kuka zo, ko momy bata nan?" Dan abu mawuyaci ne wani yazo dakin sahiba, balle wadannan cousins din nata 'yan uwan Abbah daba qaunarta suke ba tasani sarai
Qanwar hajara wacce zatayi sa'ar sahiba tace "kedai maza kiyi wanka kije Abbah na can yana nemanki tun daxu, ya hanama a tadake wai gara ki samu ishasshen bacci, da momy taga baccin naki yaqi karewa ne tace na tada ki"  sahiba a ranta tace "Abbah ya dawo kenan"  ta kalli agogo karpe 11 har da Arba'in, lallai tasha bacci, domin bata taba barci haka ba, ta shige bandakin, ta bar 'yan matan su hudu cikin dakin
Watakila kawo yanxu an daura auren yarima sultan, tasan ma an riga an daura, sai taji  hawaye sun zubo mata, wannan shi ne ta leqo ta koma.. Ta danyi kuka kuma sai ta goge idonta tana mai bawa kanta haquri, komi na rayuwa happens for a reason, trust the Almighty sahiba...

Ta ida shiryawa su hajara sukaa fito sunai mata rakiya, a falourn kasa ne taga momy da wasu 'yan uwa, ga akwatina a baje a falourn kaya ta ko ina, sahiba ta gaggai dasu suka amsa suna Allah ya sanya Alkairi amarya"
Sahiba ta dubi su hajara, wace ake bikinta cikinku?, sai suka sa mata dariya "ashe dai momy da gaske take, to kije zakiji" cewar daya daga cikin su a daidai sanda suka zo kofar dakin Abbah,
Suka barta a nan suka juya, babu mutane sosai cikin falourn Abbah wasu duk a waje suke, shi da kanshi yace taje daki gashi nan zuwa
Sahiba ta shiga dakin Abbah tana ta mamaki wannan lamari, ba dadewa Abban ya shigo ta gaidashi tana mishi sannu da hanya yace "yawwa sahiba"
"Lallai nasan baki san da wannan zancen ba, kuma nasan watakila kiyi mamakin abinda zakiji, wato shi yarima sultan yaje ya samu mai martaba.... Sanda Abbah ya ambaci sunan yarima sultan saida  sahiba taji gabanta ya fadi
"Kuma ya sanar mishi shipa kece zabinshi, dukda ya sanar a kurarren lokaci amma mai martaba bai gaza fahimtarshi ba, ya fahimceshi kuma yanason faranta mishi hakan yasa ya fasa daura mishi aure da ita diyar wajenshi amira ya maida kanki"
"Kaina Abbah?" Sahiba taji bakinta yayi saurin tambaya saboda rikicewa
Abbah yace "nasan kinada biyayya sahiba, kuma shi wannan yaron sultab bashi da wata makusa in kinji irin kyakkyawar shaidar daya samu sai kinyi mamaki, idan kikaji yadda iyaye ke mishi tallar 'ya'yansu sai kinyi mamaki, amma duk cikin 'yan matan ciki da wajen Gano ya tsallake kowacce mace ya tsallake kowacce budurwa, ciki harda gimbiya Amira ya zabeki ke da kike bazawara ma sahiba, wanda kece zaki zama uwargidanshi kuma uwar 'ya'yanshi watakil ma ana saka ran kece fulani a nan gaba"
Sahiba tayi dimmm tana hango responsibility da kalubale da suke tunkararta, amma hakan bai hanata jin wani dadi cikin ranta ba, ashe yarima sultan yarimin gaske ne har haka, Allah yasa ba mafarki take ba

WANI YANKITempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang