Daga cikin hadiman da fulani ta aikowa gimbiya sahiba harda Abida wacce itace kan yan gulmar sahiba wancan lokacin, tun sanda salima tazo tace mata wai sahiba ta chanja ta yi kyau kamar wadda ba yar kasar ba Abida taketa son ta ganta saidai kapin ta samu zuwa har sultan ya wuce da ita gidan kaka galadima, sai kuwa gashi fulani ta zabo harda ita ta aikowa gimbiya sahiba.... Abida tai zugum ta zubawa sahiba ido, ita gani take badai waccan sahibar bace wannan wata ce, wannan yar gayu ce kalar masu kudi waccan kuwa kamar Almajira jiki duk kashi.... Suna nan tsaye sahiba tana nuna musu guraren da sukeda hurumin shiga da inda bazasu shigar mata ba saiga sultan
Abida a ranta tana iyyee lallai gimbiya sahiba ta waye yanxu Allah mai iko, hadiman suka sake gaidashi sannan yasa hannu ya zagaye kugun sahiba ya jawota kusadashi a gabansu, yace "kuje yau babu bukatar wani aiki duk na sallameku gobe ku dawo"
Suka rissina mishi sannan suka juya suka fice, Abida kuwa har da tintibe tana tafe tana waigen sahiba, sahiba ta daga kai ta kalli fuskarshi tace "meyasa ka sallamesu yaa yarima baka gudun abinda fulani ko galadima zasuce"
Ya koma ya samu guri ya zauna yana jimamin abinda ke gudana cikin masarautar, sahiba ta hau sama ya bita da kallo yana tunanin ina ta tapi, ko taji haushi ne dan bai mata reply ba, ya miqe da dan hanzari ya haye steps din bai tadda ta a falour ba, dan haka straight ya wuce bedroom ya taddata tana tsaye tana ninke gyalen data cire yayi tsaye a bakin kofar yana kallonta... Ta cire dankwalin kanta, doguwar sumar kanta ta bayyana, bata ankara ba sai taji hannunshi a kan ribbon din ta ya tayata cirewa... Ta dan dubeshi tana murmushi "yaa yarima ba cirewa zanyi ba ai"
Yace "ai naga kinata cire abubuwa nace to bari na tayaki" ya soma kokarin zuge zip din rigarta, ta juyo da sauri tana facing dinshi a dan tsorace tace "a'a wlh ba cirewa zanyi ba" ya dan bata fuska, keda za'a miki abin arziki shi ne kike gwaliya" sahiba ta danyi tsuru tsuru gabanta na faduwa ta rasa dalili.... Sai ya janye hannunshi daga kan zip din itakuma taja baya da dan sauri tana sauke numfashi, ya karasa gun wata drawer ya jawo ya dakko wasu takardu da waya ya zauna kan sofa yace "zo kiga" ta karasa ta dan zauna tana kallan abubuwan daya ajiye
Yace "kyautarki ce tunda kinki bani tawa kyautar da kikamin Alqawari"
Tasa hannu ta rufe bakinta "auuuu" alamun ta mance
Yace "kin manta ko" tai saurin girgiza kai.... Kaine kayi gajen haquri
Yayi wata gajerar dariya yana gyada kai kapin yace "wannan sabuwar waya ce da sabon layi, dasu zaki cigaba da amfani" ta karba tana mai jin dadi tace nagode ya yarima
Ya kwabe fuska "lah banason godiya kinsan me nakeso?" Ta girgiza kai yace "a peck ya nuna kan kuncinshi, ta dan kau da kai tana murmushi mai kama da blushing a kunyace... Shima sai yace "shikkenan tunda kyautar farko bata samu godiya dakyau ba, zan rike kyauta ta gaba" still bata tanka shi ba ya cigaba ganin bata da niyyar magana "dama admission din ne na...." Da sauri ta juyo tana kallon takardar dayake jujjuyawa a hannunshi tayi kamar zaka karba yaqi bata ta kuma kai hannu zata karba ya goce, a shagwabe tace "plss mana yaya" ya maimaita yadda ta fada yana kwaikwayon muryarta ta sake cewa "dan Allah nagani yaya" sai ya noqe kanshi alamun yaqi, batareda yayi tsammani ba yaji lallausan lips dinta a kan nashi for just some seconds taja baya ta miqo mishi hannayenta duka biyun, ya kalleta da sexy eyes dinshi kapin kuma ya miqa mata takardun ta karba hannunta har karkarwa yake tana dubawa zallar farinciki zane akan fuskarta... Abbah ya hanata cigaba da karatu saboda ita mace ce kuma bazawara a wancan lokacin, amma cikin kankanin lokaci komi ya chanja, nata mijin da kanshi ya nema mata batareda tunanin karatun mace baida amfani ba kamar yadda mentalityn wasu mazan yake..... Bata san sadda ta soma weeping ba.. Sultan ya jawo ta ya rungume yana lallashi....Is short right yeah saboda Banajin comment,, Abeg naji ruwan comment naaa, ginger me you guyss i wanna feel the love.. Yadda zan suburbudo read moreeessss
YOU ARE READING
WANI YANKI
Romance"Itama mutun ce kamar kowa khalipa, sahiba ba ita ce tayi kanta ba, akwai mutane da sukapi sahiba muni kuma ko sahiba fa to be frank ba mummuna bace, she's beautiful her own way, kaine dai ka kasa acknowledging"...... Meze faru da ita idan mijin da...