Alhaji Garba nera tare da matansa zaune saman luntsuma-luntsuman kujerun da suke jere a tanfatsestsen falon gidansa. Kallo ɗaya za a yi masu a fahimci suna cikin yanayi maras daɗi saboda shimfiɗaɗɗar damuwar da take saman fuskokinsu, sannan babu mai cewa da ɗan'uwansa kala saboda tashin hankali da suke cikin a dalilin iftila'in da ya faɗa wa Alhaji Garba a daren shekaranjiya na ƙonewar supermarket ɗinsa, don babban attajiri ne wanda sunansa ya zagaye sako da lungu na garinsu. Kafin wannan iftila'in ma ba a fi wata guda ba 'yan fashi suka shigo gidan haɗe da ɗauke masu duk wata kaddara da suka mallaka, sai ga shi kuma sun wayi gari da labarin gobarar supermarket ɗin Alhaji Garba wanda ta ƙone kurmus kasancewar gobarar tsakar dare ne, kuma tana da alaka da wutar lantarki dalilin da ya sa aka ɗau lokaci mai tsayi kafin wutar ta mutu. Wannan iftila'in ya yi matuƙar girgiza su, ba su kaɗai ba hatta mutanen gari sun girgiza matuƙa har ma wasu suka fara zargin ko da sa hannun wasu mutane cikin lamarin duba da abin da ya faru kwanakin baya.
"Assalamu alaikum! Assalamu alaikum! Assalamu alaikum!"
Muryar Jidda mai aikinsu ta ratsa massarafar sautinsu haɗe da katse masu zaman shirun da suke yi.
Maimakon amsa sallamar, sai wata razananniyar tsawa mai matuƙar firtigitawa Hajiya Binta ta daka wa Jidda tana faɗin,"Wacce irin jaka kidimahuwa ce ke? Me ya sa ba kya fahimtar yanayin mutane? Kin yi sallama fiye da ɗaya an maki banza, me ya sa ba za ki shafa wa mutane lafiya ba? Ki ɓace mana da gani ko na ci ubanki a gidan nan banza shashasha kawai!"
"Ki bi ta sannu mana, zagi ba namu ba ne mu da muke cikin wannan yanayin."
Cewar Hajiya Salima kasancewarta mace mai sanyi sosai saɓanin Hajiya Binta mace masifaffiya kuma abun ya dame ta saboda auren Alhaji ma ta yi yana da alaka da kuɗinsa dalilin da ya sa ta fi nuna damuwarta a fili l'.
"Ke na jima da sanin ba ki damu da annobar da ta faɗa mana ba, tunda..."
"Ya isa haka!"
Alhaji Garba ya yi saurin katse su a ɗan tsawace, zuciyarsa tana tafarfasa don haka bai fatan sun ƙara masa wani abu a kan wanda yake ciki."Alhaji Ahmad yana jira na ɗakin baki tun ɗazu sai na dawo."
Ya faɗa yana mikewa tsaye********
"Na rasa gane me yake faruwa da ni abokina, duba ka gani asarar da na tafka cikin watannin nan."
Alhaji Garba ya faɗa cikin rawar murya tamkar zai fashe da kuka.Cikin kwantar da murya Alhaji Ahmad ya ce,
"Ka yi haƙuri abokina! Kowanne bawa da tasa kaddarar. Lokuta da dama Allah Yakan jarabce mu da kaddara don a gwada imaninmu, saboda haka ina so ka ɗauki wannan jarabawar a matsayin kaddara."
"Ni fa gani nake kamar da sa hannu a wannan lamarin!"
Alhaji Garba ya faɗa hawaye suna cika masa idanuwana kiris yake jira ya fashe da kuka.
"Haba abokina! Ya kamata ka fid da zargi a ranka, ka yi imani da Allah, sannan ka yarda da kaddara mai kyau ko akasin haka."
Alhaji Ahmad ya faɗa yana ƙafe sa da ido, sai da ya yi masa wa'azi sosai sannan ya bar gidan, wacce sam Alhaji Garba bai ɗauki ko kalma guda a ciki ba kodayake ba ma fahimtar abin da ya faɗa yake yi ba don hankalinsa yana wani waje daban.*******
Tashin hankali wanda ba a sa masa rana! Alhaji Garba ya tafi banki ciro kuɗi don fara wata sana'ar, sai dai abin da ya gani ya girmi tunaninsa. Babu komai cikin akawun ɗinsa, take ya suma sai da aka zuba masa ruwa ya farfaɗo yana ta sambatu rantse-rantsuwa mahaukaci sabon kamu.
Tun daga lokacin rayuwa ta fara yi wa iyalan Alhaji Garba tsanani, babban tashin hankali da suke fuskanta wani lokacin Alhaji Garba ba shi maraba da mahauci saboda magana yake shi kaɗai, sannan har kwanan gobe ya ƙi yarda da kaddara sai fama zargin mutane yake yi.
VOUS LISEZ
TUN A DUNIYA
ActionTUN ADUNIYA! gajeran labari ne mai kunshe da tausayi, zalunci, soyayyar gaskiya, kaddara, dss