4

1.9K 106 9
                                    

*Fadime dabam ta kauyen Katsina ita ce take jin busar sarewa. Falmata dabam ita ce ta Yola mai aikin raino a gidan Sarki, sai dai dukansu ana musu inkiya da Fulani. Fatar kun gane za ku daina rudewa 😀*

SIRLEEM POV.

"Hajiya ina jin kamar ba zan iya jira har Nana ta kare Karatu na aureta ba....!"

Ba Hajiya kadai ba gaba daya kanensa kallonshi su kai. Da Mamaki Hajiya tace.

"Ban gane ba?"

Ya cika ma bakinsa iska ya busar sannan ya shiga murza hannunsa kamar mai shafa mai.

"Kawai dai bana iya jira, tana kula wasu bayan kuma kowa a Masarautar nan ya san ni zata aura, sannan ina ganin kamar yan gidansu basa son hadin nan nawa da ita idan abun ya kai wani lokacin za su iya lalata shi"

Ajiyar Hajiya ta sauke.

"Gaskiya ne, za su iya lalatawa amman zancen tana kula wasu kar ya dame ka kai auren a haka ai zata daina kuma idan ka gani ka rika magana"

"Na ganta da Deen din nan da yake zuwa duba yaran Shattima, na je har Part din su na yi magana babu wance komai karshe ma Hajiya Karama ta taso tana fada ni wai ina takurawa Nana kamar wani ubanta"

Hajiya ta yi murmushi mai kama da dariya.

"Kar hakan ya dame ka Sirleem kai dai ka aureta kawai komai zai wuce"

Ya kalleta cike da gajiyar jin abunda take yawan nanata masa idan yai mata complain akan Nana.

"But Hajiya miyasa dole sai Nana? Tsakanin da Allah neman auren nan na saka kaina ne kawai saboda kin tirsasa ni amman ni kaina yarinyar nan bata kwanta min ba, ni kuma na fara gajiya gaskiya ba zan jure daukar wulakanci a gurin kowa ba na fi karfi haka, dan kawai tana yar sarauta ubanta yana sarki mahaifiyarta tana matar sarki yayanta yana dan sarki ba zan dauki wannan wulakanci ba na fi karfin wulakanci a gurin kowa ni"

Ya fada yana daga kafadunsa, Rima ta tabe baki tana ture kofin tea dake gabanta tare da kallon yayan nata.

"Ni kaina ba son auren nan nake ba, dan dai kawai Hajiya ta matsa ne akan ayi, amman miye amfanin hada alaka da makiyi alakar ma ta aure haba dai..."

Murmushi Hajiya tai ta taso daga kujerar da take zaune ta dawo bayan Sirleem ta tsaya.

"M2 ba haka duniya ta sanka ba? Kai a yadda kake Celebrity sai kaje ka auri wacce bata kai ba? Ga yar sarauta yar masu naira kuma kyakkyawa yarinya mai kurciya a gidanku? Ba ka lura ba? Maran manyan mutane suna auren yar manyan mutane? A yadda kake sannen a duniya ai kamata yai ace ka auri yarinyar da ta isa gaba da baya, taya za a tashi maganar da kasan zata iya saka Mai Martaba a cikin wani hali bayan gashi kwance ba lafiya? Baka tunani ya takama mu sakawa Mai Martaba da irin hallacin da yai mana? Idan mahaifiyarta matar sarki ce kai ma taka uwar matar sarki ni da Zainabun Jirgi daya ya dauko mu domin dukanmu Mai Martaba muke aure. Ke kuma Rima da kike fadar hakan ai kyautatawa ce wanda yai maka sheri sai ka saka masa da alheri, ba ni da burin da ya wuce na ga Sirleem ya auri Nana a yanzu ku karfafawa dan'uwanku guiwa ba wai ku sare ba"

Ta karasa tana kallon Rima. Sirleem ya juyo yana kallon mahaifiyarsa tasa.

"Amman Hajiya ai ba Nana ce kadai yar sarauta ko yar masu arziki ba, akwai da yawa mi yasa ba zaki bar ni naje da kaina na zabi wacce tai min ba?"

"idan zaka auro yar sarkin Makka, dan arzikinsu da Sarauta ba ka cika min burina ba matukar baka auri Nana ba, idan kuma zaka auri yar sarkin talauci na duk duniya bayan ka auri Nana to ba zai tana damuna ba, ni dai burina Nana ta zama uwargidanka"

A hankali ya aje numfashi yana kallon kanensa wanda shi ma kallonsa yake suna mamakin furucin mahaifiyar tasu. Talba ya ce.

"Amman Hajiya miyasa?"

FULANIWhere stories live. Discover now