HAJIYA KARAMA (Zainab) POV.
Ta bude motar ta fito tana karewa gidan kallon kamar wani bakonta, ko da yake kusan gidan bakonta ne domin tun zuwanta na farko ba ta sake ba sai yau, Zainab irin matan nan ne da basa bin kawaye sai dai kawaye su bi su dan suna jin sun isa, tana ji da Sarautar da ba ta jininta ba tana jin naira ga kuma daukaka da ta samu sakamakon aikinta na daukar hoto wanda ba kasafai kake mace bahaushiya kuma musulma tana yi ba, bayan daukar hoto Zainab fitattaciyar yar daukar wanka ce Instagram hakan yasa hotunanta suka yawo a duniya kamar wata yar film ko mawakiya ga kuma kyau da Allah ya hore mata da cikar sura irin ta ya mace.
Katon bakin gilashin idonta ta cire tana kara kallon mijin kawarta da kyau, sai ta ga yafi kyau a fili ma fiye da hoton da Humaira ta dora lokacin anniversary su. Daga inda take tsaye sanye da dogon wando na jean da half gown ta atamfa kanta da jar hulla waccw ta bayyana rabin gashin kanta daya sha gyara, ta daga masa hannu alamar HI tana wani yauki da fingers dinta kamar ba farata ba sai wani murmushi take masa na daukar hankali. Da mugun mamaki ya dago mata hannun shi ma wai celebrity ta dago masa hannu da kanta ya santa dan yana daya daga cikin followers dinta na instagram, secondly kuma Humaira na yawan ba shi labarinta ta nuna masa hotonta ya fi a kirga third kyauta ya wuce yadda yake ganinta a hoto domin a fili farinta har wani haske yake kana ganinta ka ga yar fulanin asali kuma wayayyiyar mace."Ba laifi bayan kyau kana da naira"
Ta fada a ranta tana karewa tsaddadiyar motar da yake kokarin hawa kallo, sannan ta doshi cikin gidan tana wani irin taku na daukar hankali, murmushi ya cika kyakkawar fuskarta ko ba komai zuwan da tai yau saboda mijin kawarta ne domin tun a lokacin fa Humaira ta saka shi a status dinta na happy anniversary ta ji ranta ya biya, kuma bukatarta ta biya tun da ta yi arba da shi.
Door bell din ta danna in few minutes house help din Humaira ta bude mata kofar, sai ta nasa kafarta a katon falon tana kare masa kallo, a ranta ta raya ba laifi ita kam ta ga gurin zama. Cike da far'ah da jindadin ziyarar Humaira ta fito ta rumgume ta.
"Oyoyo manyan kasa yau ke da kanki Hajiya Karama"
"To ya za'ayi muna so ne ai dole mu biyo, ykk"
"Lafiya kalau ya gida ya su Hajiya da Ammy"
"Suna nan kalau ina yaranki?"
"Suna makaranta"
Ba laifi Hajiya Karama ta saki jiki suka sha fira da Humaira har abun ya bawa Humaira mamaki domin ba kasafai Hajiya Karama take sakewa tai fira da kawaye haka ba no matter how close they are, ita din tana da wani irin jin da kai da isa idan ana fira sai dai ta rika jefo zance can sama-sama, hakan kuma be hana kawaye binta domin tana kashe musu kudi kamar bata san zafinsu ba, ga kyauta da alheri ga kowa.
"Bude min wayar na ga hotunan anniversary tun da ba a fada mana ba"
Ba musu Humaira ta cire mata password tana dariya tare da fadin.
"Ba mu gayyaci kowa ba fa daga ni sai yara mu kai sai uban gayyar"
Cikin hotuna Hajiya Karama ta shiga tana dubawa, sai da ta bari Humaira ta tashi sannan ta shiga long calls dinta tana bin numbers din da kallo, number da aka sakawa Alone da hoton heart ta bude tayi copying digit din ta shiga message ta saka number ta ta aika ma kanta da number sannan ta goge sakon ta aje wayar tana murmushi.
"Humi zan wuce daman na biyo ne kawai na gaishe ki"
Har gurin motarta Humaira ta rakota tana ta mata godiya domin ba karamin dadin ziyarar taji ba, ba ta bar Hajiya Karama ta wuce ba sai da su kai hoto.
Cikin farinciki ta dawo Masarautar ranta fes domin ta samu abunda take so, part din Ammy tai parking sannan ta fito tana wani irin taku na kasaita kamar wata yar sarki ta shiga cikin gidan. Ko kallon mutane dake gaisheta ba su isheta ba, balle har ta amsa gaisuwar da suke miko mata, yadda take lumshe ido ta bude ma kadai wani abun kallo ne. A natse ta shiga katon falon na Ammy, babu kowa a ciki sai plasma da Ac dake ta aiki bada sanyi, ta kalli farantin dake cike da sweet an dora shi saman kujera, ko ba a fada ba ta san aikin Nana ne ko Yusra. Kusa da farantin ta zauna ta bude wayarta ta soma dannawa, can kuma ta kai hannu ta dauki sweet din ta bude ta fara sha. After like 30 minutes Ammy ta fito daga dakin sanye Holland Nana na rike da gyalen nata tana kuka kamar wata yar 6 years.
YOU ARE READING
FULANI
FanfictionFULANI -The story of unwanted girl, she always had a strong sense of destiny...! The story of a Prince and his kingdom. witchcraft, distorted relationships, hidden secrets, selfishness.