♡ ♡ ♡ *LAD'EEFARH* ♡ ♡ ♡
*STORY AND WRITTEN BY AUTAR MAMA*
*Marubuciyar*
*CAPTAIN SALEEM*
*KAINE GWANI NA*
*RAYUWAR GIDAN MU*
*TARIHIN MASARAUTAR MU*
*ZAINAB (ZEIY)*follow me on Wattpad @inteesar Roshni
Instagram @Intee_baby
Snapchat hafsat1549*K'irk'irarren labari kuma gajere*
*Alhamdulillah ina mai rok'on Allah ya bani ikon isar da sakon da nake son isarwa sannan ya yafe min kuskuren da zanyi a cikin wannan littafin*
*Wannan labarin k'irk'irarre ne.. Ban yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba!*
بسم الله الرحمن الرحيم
_________________
______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
PAGE 1
Sanya ya ke cikin suit wanda sukai matuk'ar karb'an farar fatarshi, kakkyawane sosai kai da ganin kamaninsa kasan ba bahaushe ba ne... Don yafi kama da larabawa ko shuwa, hannunshi rik'e da jakar zuwa aikin shi,k'afafunshi sanye da sau ciki, siririn glass ne fari a idanunshi wanda ya k'ara masa wani had'add'en kyau... Matashi ne wanda bazai wuce shekaru 34 ba aduniya amma da ganinshi kasan kud'i ya zauna sannan yana cikin kwanciyar hankali. Tsadadden agogon dake sanya a tsintsiyar hannunshi wanda ya k'awatu da wani lallausan bak'in gashi yayi 7:15 ya nuna, cikin hanzari ya d'auki wayoyin sa dake kan mudubi ya fita daga d'akin. Taku ya ke yi kamar an sashi dole har ya sakko daga stairs jakarshi ya ajiye akan tsadaddiyar kujerar dake makeken parlon ya nufi dining area wanda ke d'auke da kujeru guda goma sha biyu... Kuloline kala² kai da ganin kalar kulolin kasan masu tsada ne... Wata matashiya ce ta fito daga wani k'ofa da alama dai kitchen ne hannunta rik'e da flask d'in ruwan zafi me d'an banzan kyau, kakkyawa ce itama amma ba can ba, sai dai farinta har ya d'ara nashi, a shekaru bazata wuce 25 ba,komai dai². Riga da zani ne ajikinta wanda ta kashe wani uban d'auri daya dace da kwaliyar ta... Fuskar ta d'auke da murmushi ta k'arso dining d'in, ajiye flask d'in ta akan dining sannan ta matso kusa da shi a tana masa side hug tare da light kiss a chick d'inshi a hanakali ta furta, "Good morning". Murmushi ya yi wanda ya kusa zautar da ni lol.. Ya shafo lallausan fuskar ta ya ce "Mrng soul". Zama ta yi ta fara serving d'in shi. "Ya isa". Ya fad'a cikin muryar shi me dad'i yana ma ta murmushin shi me zautar da ita ya kuma dilmiyar da ita cikin kogin sonshi. Tea ta had'a mishi sannan ta zauna agefen shi ta shiga bashi abincin cike da kulawa da kuma nuna tsantsar so har ya gama... Tashi ta yi ta nufi tsakiyar palon ta d'auko jakarshi da sannan ta dawo dining d'in cikin muryarta me sanyi ta ce "FAHAD time is going". Murmushi yayi sannan ya mik'e, cikin kulawa suka rik'o hannun junan su, babban compound d'in gidan suka nufa tafiyar kusan minti 5 sukai sannan suka isa parking space. Motarshi kirar Roll Rayce fara k'al ya shiga... Kamar karsu rabu haka ta ji addua ta mishi, sai da taga fitar shi sannan ta sauke ajiyar zuciya ta koma cikin gidan. Sai tara sannan ma'aikatan gidan suka fara zuwa cikin k'ank'anin lokaci suka gyara gidan... D'akinta da kuma na mijinta ne kawai basu gyara ba, dan ita ta ke gyara abinta.
2:34pm
Ta sauya kayanta zuwa simple gown fuskarta ba kwaliyya ta na kallo gabanya d'auke da bowl wanda ta had'a fruit salad tana ci a hankali, sanyi AC na ratsa ta har wani lumshe ido ta ke yi... Wayarta da ke gefenta ta janyo, Contact d'inshi ta shiga ta fara rubuta mishi text "Missing U a lot Honey". Yana zaune a cikin office d'inshi naura me kwakwalwa agabanshi yana latsawa yaga wayarshi ta yi haske... Murmushi ya saki bayan ya gama karanta sak'on na ta. Reply yayi ma ta da "On My way home sweet". Ajiyar zuciya ta yi sannan ta mishi reply da "So Soon?". Kiranta yayi sai da ta saki wani lallausan murmushi sannan ta d'aga "Are not missing me?". Ya tambayeta cikin kulawa. "Sure am missing yuh". Ta fad'a ad'an shagwab'e. Door bell aka dannawa ba k'akk'autawa... Gabanta ne ya fad'i tana addu'a aranta Allah yasa ba k'anwar mijinta ba ce. Jin ta yi shuru yasa shi cewa "Are yuh their?". Murmushi ta k'ak'alo a d'an hanzarce ta ce "i will call u later". Ta katse wayar. A d'an sauri ta isa bakin k'ofar ta sa key ta bud'e. Tsaye ta ke sai faman hura hanci ta ke tana d'add'age fuska, dan kyau kham me kyau ce sosai, sanya ta ke da doguwar riga b'aka wadda ta haska farar fatarta a shekaru bazata wuce 18- 19 ba. Bangaje ta tayi tana ya mutsa fuska hannunta janye da trolling babba. Jiki a sanyaye ta rufe k'ofar ta, bak'uwar har ta yi wa kanta mazauni akan kujera cike da gadara ta ce " Ladifa ko ruwan ma sai kin yi wa mutum rowa? Mtsww Allah ya sawwake wallahi.. Illar rashin gadar arzik'i kenan, rowa dai a jinin ahalinku ya ke". Daga haka ta mik'e fuu ta nufi kitchen, it dai Ladifa bata ce komai ba ta zauna akan kujera....