8

1.3K 99 8
                                    

Da wani irin zazzabi Falmata ta farka, fuskarta ta kumbura gaba daya jikinta sai ciwo yake idonta ma ya kumbura sosai sakamakon kukan da ta kwana tana yi.
Babu abunda ta fasa daga cikin aikin gidan da ta saba, ta sani sarai idan ta saka kuiya ko tace ba zata iya ba wani karin wahalar ne. Tana aikin tana kukan zuci har ta yi ta gama, ta dawo dakinsu ta zauna ta gefe daya dan bata iya zama daidai.

Tumba ce ta shigo dakin tana kare mata kallo.

“Ba za ki tashi ki je gurin aikin ba?”

Kallon Tumba tai kamar zata fasa kuka, bata jin abunda ta ce sai dai tana ganin bakinta na motsi.

“Ban ji komai ba Umma”

Ta fada muryarta na rawa kamar yadda jikinta ma yake rawa dan ganin take kamar dukanta Tumba za tai ko ta sake mata wani mugun sherin. Wani kallo Tumba tai mata.

“Ni za ki fara yi wani sabon siyasa?”

Ganin Tumba ta nuna kanta da yatsa yasa ta nemi duk inda wani kuzari yake ta tattaro shi ta saka a jikinta ta mike tsaye ta karasa kusa da Tumba dan jin abunda take fada.

“Wallahi ban ji me kika ce ba Umma bana ji sosai”

Ta fada kamar zata fasa kuka, Tumba ta san Falmata ba zata mata karya ba, ba zata mata haka da gangan ba, yanayinta kadai ya isa ya sanar da gaskiyarta.

Tumba ta dan tabe baki, sai a lokacin ne take girmama marin domin ba marin wasa Baba yai ma Falmata ta ba, gashi fuskarta har ya kumbura.

“Cewar nai ki tashi ki tafi aikin”

Tumba ta fada cikin daga murya ta maimaita mata ta yadda za ta ji. A take Falmata ta fara murza yatsun hannunta so take ta sake tuna mata cewar sun koreta amman sanin waye Tumba yasa dole tai shiru ta sauke kanta kasa.

“Ba za ki je, ki ba su hakuri ba?”

Wannan karon ta ji domin Tumba da karfi tai maganar.

“To”

Amsa tana motsa jikinta daker domin ba karamin tsami yai mata ba. Tumba ta juya ta fice daga dakin. Falmata ta nufi gurin da Hijabinta yake ta dauka ta saka ta fito. Da gangan Tumba ta kira ta karbi dumamenta ganin Baba na tsaye yana shirin tafiya.
Falmata ta nufi inda Tumba take da zimmar karba ba dan ta ji abunda tace ba sai dan ganin tana miko mata kwanonta. Ba dan tana jin yunwa ba domin komai ya fitar mata a rai, kan ta karasa Baba ya daka mata tsawa.

“Kar ki karbi abincin nan, ba za ki sake cin abincin gidana ba, tun da kika zabi iskanci....”

Cak Falmata ta tsaya ta kasa karasawa gurin da Tumba take zaune taka miko mata dumamen, ta ji abunda Baba yace saboda yanayin muryarsa irin mazajen nan da idan suna magana daga murya suke, balle kuma ita da baya iya yi mata magana a hankali.

“Haba Malam ba a horo da yunwa, na san Falmata ta yi laifi amman ka dubi girman Allah ka yi hakuri, ba a biye ta yaro”

“Ni dai na fada miki ban yafe a bata abincin gidana ba, ba zan ciyar da karuwa ba”

Ya fada kai tsaye sannan ya nufi kofar fita ko inda Falmata take be kalla ba. Baki sake Falmata ta bishi da kallo hawaye na sauko mata zuciyarta na mugun kuna, kamin ta kalli Tumba wacce ke kukan karya.

“Wallahi da na san haka abun zai zama da ban fada maka ba, wannan abu be min dadi ba ni Ramatu”

Bata iya ji yo komai amman tana gani ganin yadda bakinta ke motsi ta san da kuma kukan murnafurcin da take, ta san ta shirya komai ne. Daker Falmata ta hade abun da ya tsaya mata a wuya sannan ta nufi kofar fita tana jin kamar ta mutu a yau ta huta, taya zata rayu a idan ubanta kuma ace ba zata ci abincin gidan ba? Miyasa Tumba zata mata haka? Me tai mata? Saboda ta fadi gaskiya? Mi ya kaita fada mata gaskiyar? Miyasa ma yasa ta aikata tun farko? Tana tafiya tana tambayar kanta tambayar da bata da amsa hawaye sai aikinsu suke a fuskarta.
Gidansu kawarta Khadija ta nufa, sa same a tsakar gidan tana wanki kasancewar yau assabar babu school, Khadija na ganin Falmata hankalinta yai mugun tashin.

FULANIWhere stories live. Discover now